Editor

9513 Posts
JAMB ta ayyana ranar da za ta fara fitar da sakamakon UTME

JAMB ta ayyana ranar da za ta fara fitar da sakamakon UTME

Hukumar shirya jarrabawar neman gurbin karatu a makarantun gaba da sakandare (JAMB) ta ayyana ranar da za ta fara fitar da sakamakon jarrabawar UTME da aka rubuta kwanan nan. Cikin sanarwar da ta fitar ranar Litinin, JAMB ta ce za ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME ranar Talata, 2 ga watan Mayu, 2023. Sama da mutum miliyan 1.6 ne suka rubuta jarrabawar UTME a makon jiya don neman gurbin karatu a makarantun gaba da sakandare daban-daban da ke faɗin ƙasar nan. Hukumar ta ce, ta amince ta fara fitar da sakamakon jarrabawar ne bayan taron gaggawar da ta gudanar a…
Read More
Ɗan sanda ya tuttula kashi a wando bayan ya ɗirki barasa a Kwara

Ɗan sanda ya tuttula kashi a wando bayan ya ɗirki barasa a Kwara

Wani ɗan sanda a Jihar Kwara ya tuttula kashi a wando bayan ya yi tatil da barasa. Wani faifan bidiyo da aka yaɗa ya nuna yadda jami'in ya tsula fitsari da tuttula kashi a wando alhali yana sanye da kayan aiki, yayin da abokan aikinsa biyu ke ƙoƙarin tallabo shi. Tuni Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kwara, Paul Odama, ya ba da umarnin a tsare Yohanna don gudanar da bincike. Da yake tsokaci kan batun, CP Paul Odama, ya nuna ɓacin ran rundunar kan abin da jami'in ya aikata, tare da bayyana lamarin a matsayin abin ƙyama. A cewar Kakakin ‘yan…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum 40 a Kebbi da Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe mutum 40 a Kebbi da Zamfara

Rahotanni daga jihohin Zamfara da Kebbi sun ce 'yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 40 a ƙauyukan jihohin yayin harin da suka kai da asubahin ranar Lahadi. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar, wasu 'yan sanda guda shida na daga cikin mutum 36 da 'yan bindigar suka kashe a Ɗan Umaru da ke yankin Zuru a Jihar Kebbi. Mazauna yankin sun ce an yi jana'izar mutum 27, sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon harin. Kazalika, sun ce 'yan bindigar sun sace mutane da dama haɗi da shanun jama'a yayin harin da suka kai ƙauyuka maƙwafta. Bayanai sun ce maharan…
Read More
NLC ta hana shuwagabannin jihohi bada kyaututtuka ga ’yan siyasa

NLC ta hana shuwagabannin jihohi bada kyaututtuka ga ’yan siyasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), a ranar Alhamis, ta hana ɗaukacin shugabanninta da sauran jami’an majalisar na jihohi 36 na Tarayyar Nijeriya bayar da kyautuka ga ’yan siyasa. NLC ta kuma ce ta ɗauki matakin ladabtarwa cikin gaggawa kan duk jami’an da ke haɗa baki da wasu gwamnonin jihohi wajen bijire wa umarnin majalisar gudanarwa ta ƙasa NAC. Shugaban Majalisar, Kwamared Joe Ajaero ne ya bayyana haka, a ƙarshen taron kwana biyu da NAC ta gudanar a gidan ƙwadago da ke Abuja. Shugaban NLC, wanda ke tare da Babban Sakatare, Kwamared Emma Ugboaja da sauran shugabannin…
Read More
SOAR ta horar da masu fafutukar kare haƙƙin jinsi

SOAR ta horar da masu fafutukar kare haƙƙin jinsi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata ƙungiya mai zaman kanta 'Sexual Offense Awareness and Response Initiative', ta ce, ta horar da mutane aƙalla 257 a matsayin maza masu fafutukar kare haƙƙin jinsi a sansanonin 'yan gudun hijira daban-daban (IDP) a Benuwai. Jami’in shirin na ƙungiyar, Mista Chibuzor Njoku ne ya sanar da hakan a taron kwamitin aiwatar da haƙƙin ƙananan yara na Benuwai a ranar Alhamis. Chibuzor ya bayyana cewa, an yi wannan horon ne akan dandamalin shirin samar da shawarwarin samari na yaƙi da cin zarafin mata da ayyukan Y-map. Ya ci gaba da cewa, wani shirin - Girls Empowerment…
Read More
Ƙungiyoyi sun bayyana shiyyar da ya dace ta fitar da Shugaban Majalisar Dattawa

Ƙungiyoyi sun bayyana shiyyar da ya dace ta fitar da Shugaban Majalisar Dattawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gamayyar ƙungiyoyin da ke sha'awar tsoma baqi a harkokin siyasa a arewa maso yamma, 'Rescue North West APC Group' ta ce, ta raba gardama kan kujerar Shugaban Majalisar Dattawa. An ruwaito gamayyar ƙungiyoyin na cewa shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya ce ta cancanta ta samu kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10 da za a kafa. A cewarsu, ya kamata a baiwa shiyyar wannan kujera saboda ta ba da gudummuwar tulin ƙuri'u, waɗanda suka taimaki Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya kai ga nasara a zaɓen 2023. Bayan taron da ƙungiyoyin suka gudanar a jihohin Katsina, Kaduna,…
Read More
Matsalolin haƙora da yadda za a magance su (3)

Matsalolin haƙora da yadda za a magance su (3)

Daga AISHA ASA Mai karatu sannunka da jimirin bibiyar jaridar al'umma, Manhaja. Kamar yadda muka faro wannan darasi na matsalolin haƙora sati biyu baya, yau ma za mu kawo wasu daga matsalolin da yadda za a iya magance su. Idan kun shirya, zan ce Allah Ya sa a amfana da abinda za a karanta. A wasu lokuta rashin hasken haƙora kan zama matsala ga mai tare da shi, saboda sau da yawa idan aka kalli haƙoran sai a yi wa mai su kallon ƙazami, duk da cewa, yana wanke su yadda ya kamata. Sau da yawa akan bazama neman man…
Read More
NANS ta ba wa MultiChoice wa’adin kwanaki 7 don cire ƙarin farashin satalayi

NANS ta ba wa MultiChoice wa’adin kwanaki 7 don cire ƙarin farashin satalayi

Daga AMINA YUSUF ALI Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) yankin Kudu maso yammacin ƙasar nan, ta ba wa kamfanin satalayi na MultiChoice Nigeria, wa'adin kwanaki 7 kacal a kan ya soke ƙarin farashin da ya yi nufin yi a kan biyan tashoshin DSTV da GOTV. Hakazalika ƙungiyar ta yi barazanar rufe dukkan wuraren da ake sayar da tauraron ɗan'adam ɗin na Multichoice. Ƙungiyar ɗaliban ta bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata a wani jawabi da shugaban tsare-tsarenta, Adejuwon Olatunji, da mataimakinsa, Alao John, da jami'inta na hulxa da jama'a, Opeoluwa Awoyinfa suka sanya wa hannu. A kwanankin…
Read More
Shawara ga gwamnati kan kwashe ’yan Nijeriya daga Sudan zuwa Masar

Shawara ga gwamnati kan kwashe ’yan Nijeriya daga Sudan zuwa Masar

Game da yadda na ke bibiyar batun ’yan Nijeriya da ke Sudan inda yaqi ya goce, a ganina akwai sarqaqiya musamman ganin wannan Talatar za a fara kwashe su zuwa Masar daga Khartoum yayin da wasu xalibai sama da mutane dubu sun shiga motacin bas suna ka iyaka da Ethiopia yadda suke Neman haurawa zuwa Addis Ababa, sun fara Shan wahala. Gaskiya wancan hanya ta qasa cikin Ethiopia ba kyau akwai qarancin abinci da ’yan ta'adda a hanya, idan ba Allah ya kiyaye ba komai na iya faruwa don haka a bi a yi hattara. Ya kamata kafin a fara…
Read More
Maza, sai mun gyara kanmu za mu samu mace tagari

Maza, sai mun gyara kanmu za mu samu mace tagari

Assalam alaikum. Fatan kowa yana lafiya, fatan kuma mun sallah lafiya. Allah Ya sa muna da rabon ganin da yawa a gaba. Da yawan daga cikin maza na ganin mata a matsayin wata halitta mai murɗaɗɗen hali wacce da wuya ka gane ina ta dosa. Hakan na cima matan tuwo a ƙwarya kwarai. Mujallar Hivisasa ta ƙasar Kenya ta gudanar da bincike a kan musabbabin hakan. Kaɗan daga ciki binciken da suka gudanar sun gano cewa hormones ɗin mata na taimakawa wajen halayyarsu, hakan ya sa ake ganin mata masu wuyar sha'ani. Cikin mata kashi ɗari, kaso saba'in da biyar…
Read More