30
Apr
Daga BASHIR ISAH Da alama wasu daga jihohin Nijeriya sun ɗauki nauyin kwashe 'ya'yansu da suka maƙale a Sudan zuwa gida bayan da Gwamnatin Tarayya ta yi jigilarsu zuwa ƙasar Masar. Jaridar News Point Nigeria ta kalato cewar, jihohin da lamarin ya shafa sun haɗa da Borno da Jigawa da kuma Kaduna. Shugaban Ƙungiyar 'Yan Nijeriya Mazauna Sudan (Ɓangaren Dattawa), Dokta Hashim Na’Allah, ya tabbatar faruwar hakan. Ya ce, “Tabbas, gwamnatin jihohin Kaduna da Jigawa sun kwashe 'yan asalin jihohin yau.” Haka shi ma ɗalibi Abdullah Anyuabuga, ya ce “gwamnatin Kaduna ta kwashe 'yan asalin jihar a yau ta tafi…
