28
Apr
Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ƙarshe dai, Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar tsawaita wa’adin cire tallafin man fetur har bayan wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari a karagar mulki. Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-Tsaren Ƙasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a wannan Alhamis yayin da ta ke zantawa da manema labarai a Abuja. A cewarta, Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa NEC ce ta yanke shawarar cewa ba yanzu ne lokacin da ya dace a cire tallafin man fetur ba a ƙasar. Ministar wadda ta bayyana hakan bayan kammala zaman majalisar wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta, ta ce…
