Mahaifiyar marubuci Ayuba M. Ɗanzaki ta kwanta dama

Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano

Ayuba Muhammad Ɗanzaki dai fitaccen marubucin hikaya ne da yake yin rubutunsa cikin harshen Hausa na zube da kuma rubutacciyar waƙa musamman ta yabo ga Fiyayyan Halitta (S.A.W.). Ya wallafa littafai da dama, waɗanda suka haɗa da ‘Shingen Ƙauna, Adawar So, Rayuwar Bilkisu, Fadar So, Kurman Hisabi’ da dai sauransu.

Mahaifiyar ta marubuci Ayuba Muhammad Ɗanzaki dai wato Hajiya Salamatu Garba Zakirai, wadda aka fi sani da Hajiya Talatuwa Ɗanzaki ta rasu ne ranar da ta gabata daidai da 4/5/2023, da ƙarfe Sha Biyu na dare (12:00AM). Cikin tattaunawar da wakilinmu ya yi da fasahin marubucin Ayuba Muhammad Ɗanzaki anzaki ya faɗa cewa: “Kawai ajali ne ya kira ta ba tare da wani ciwo ba, duk da a baya akwai cutar da ta ringa damun ta ita ce olsa, amma ba ita ce ta kai ta kushewa ba. Don ta ma ji sauƙi sosai.

“Hasalima ranar da ta rasu, a ranar ne ta dawo daga ziyarar kwanaki Biyar da ta kai garin kakanninta. Kuma ƙalau ta dawo ba tare da wani ciwo ba. Allah Sarki! Ashe bankwana ta je yi musu. Ta dawo ne da yamma, da dare kuma ta koma ga Ubangijinta. Allah Ya ji ƙan ta Ya haska makwancinta amin.”

Hajiya Talatu Ɗanzaki, ta rasu tana da shekaru 80 a duniya, ta bar ‘ya’ya shidda, biyar maza da mace ɗaya da kuma jikoki 30. Daga cikin ‘ya’yan nata akwai: Alaramma Malam Garzali, da Injiniya Mukhtar, Aunty Lami, da kuma ɗan autanta wato marubuci Ayuba Muhammad Ɗanzaki, wanda shi ne shugaban ƙungiyar marubuta ta AREWA AUTHORS FORUM kuma tsohon shugaban tsohuwar kungiyar marubuta ta ‘Tsintsiya Writers Association’.

Marubuci Ayuba Muhammad Ɗanzaki, shi ne dai ya kafa ƙungiyar marubuta ta ‘Kainuwa Authors Kano’ kuma yake jagorantarta. Bayan haka shi ɗin member ne a ƙungiyar marubuta ta ƙasa reshen jahar Kano (ANA Kano) da kuma ‘Hausa Authors Forum’ (HAF).

Allahu Akbar! Mutuwa ke nan rigar kowa. Allah Ya ji kan ta da gafara, Ya haska makwancinta, Ya sa Jannatul Firdausi ce makoma gare ta Amin.

Yadda marubuta suka taya juna Alhini

Kasantuwar duniyar rubutu, duniya ce da take maƙil da mutane ma’abota hankali da tunani da kuma tarin ilimi a mabambantan fannoni, kuma suke da matuƙar zumunci, da haɗin kai da ƙaunar juna. Tarin alherinsu da taimakon juna ya rivanya saɓaninsu sama da kashi 75%. Wannan ne ya sa komai ya faru ga ɗayansu, to ‘yan uwansa marubuta ke yin dandazon taya shi murna idan na farin ciki ne. Haka idan na baqin ciki ne su taya shu alhini. Wannan sananniyar al’ada ce da dukkan waɗanda ke da alaqa da duniyar rubutu ya san da ita.

To kamar haka ne ya faru sakanni kaɗan da sanarwar rasuwar mahaifiyar marubuci Ayuba Muhammad Ɗanzaki. Saboda kasancewr a lokacin dare ya raba amma sai ga ɗaiɗaikun matubuta a shafukansu na social media na ta yin addu’o’in neman rahama ga mamaciyar da kuma miƙa saƙon ta’aziya ga ɗan uwa Ayuba Zakin Marubuta. Wasu kuma na kira da masu lalubar lambobin makusantansa don samun tabbaci.

Hakan ce ta kasance har kusan asuba. Yayin da wasu kuma gari na wayewa suka niƙi gari suka yi sammako don a sallace ta tare da su. Wannan karamci ne da tsakanin marubuta ya zame ɗabi’a. To balle ga zakin marubuta wanda yake mutum ne na mutane, da duk sabgar marubuta ba ya yarda a baro shi a baya. Lallai ko ashe shi ma za a yi masa.

Har a jiya Alhamis da 11/5/2023 da ake yi addu’ar (7) garin na Ɗanzaki bai fasa karɓar baƙoncin marubuta masu zuwar masa gaisuwa ba. Ba ma a maganar amsa kiran waya, ko sakon kar ta kwana, ko sako ta manhajar whatsaf da facebook. Wallafa saƙon ta’aziya a shafukan facebook kuwa wannan ba na a maganarsa.

Don ba marubutanmu na dauri ba hatta marubutan yanar gizo ba a bar su a baya ba. Lallai wannan ce ta sa Zakin Marubutan ya wallafa a shafinsa yana cewa: “Allah na gode maka da ka ba ni jama’a masu so na. Na rasa bakin gode muku. Alhamdulillah.”

Yayin da shi kuma marubuci Zubairu Musa Balannaji wanda na na hannun daman Ayuban ne, cikin wanj saqo da ya wallafa a shafinsa na facebook da ya masa take da ‘Saƙon Godiya Gami Da Ban Gajiya’ yake cewa: “Muna masu mi’ka sa’kon godiya da kuma ban gajiya ga ‘daukacin Al-ummar da su ka halarci jana’iza da kuma ta’aziyyar babban rashi da mu ka yi na Uwa a gare mu, Mahaifiya ga Dan’uwa abokin aikinmu Marubuci Ayuba Muhammad Danzaki, musamman ma yan’uwa Marubuta maza da mata da Manazarta, har ma da Makaranta littafan Hausa masu ‘kaunarmu, wa’danda su ka yi takakkiya su ka zo, wasu tun daga gari-ya-gari su ka tako su ka zo.

“Da masu kiran waya su yi ta’aziyya, har ma da masu Addu’o’in samun rahama gare ta a social media. Ha’ki’ka wadannan jerin mutanen da na ambata sun nuna mana ‘kauna gami da karamci. Muna Addu’ar Allah Ya saka musu da mafificin alkhairi, Ya kuma ‘kara mana dan’kon zumunci a tsakaninmu. Ita kuma Mama Allah Ya gafarta mata dukkanin kura-kuranta, Ya sanyaya makwancinta.”