Editor

9513 Posts
SSS ta mamaye CBN, ta karbe ikon ofishin Emefiele

SSS ta mamaye CBN, ta karbe ikon ofishin Emefiele

Daga WAKILINMU A ranar Litinin jami'an hukumar tsaro ta SSS suka mamaye ginin hedkwatar Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ke Abuja inda suka karɓe ikon ofishin Gwamnan Bankin, Godwin Emefiele. Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewar ba yau SSS ta fara farautar Emefiele ba kan zargin almundahana. A baya, hukumar SSS ta buƙaci kotu ta ba ta izinin tsare Emefiele amma ya zamana ba ya ƙasa sakamakon hutu da ya tafi wanda zai ƙare ranar Talata, 17 ga Janairu. Sai dai a Disamban da ya gabata Babbar Kotun Abuja ta haramta wa SSS cafke Emefiele, ko tsare shi, ko kuma…
Read More
Shugaban ACF ya caccaki Afe Babalola kan kalaman ƙarfafa siyasar kuɗi

Shugaban ACF ya caccaki Afe Babalola kan kalaman ƙarfafa siyasar kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani jigo a Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), Muhammad Alhaji Yakubu ya yi kakkausar suka ga wanda ya kafa kuma shugaban jami’ar Afe Babalola, Ado Ekiti, Cif Afe Babalola (SAN) kan cewa wanda ya fi kowa kuɗi, amma ba wanda ya fi kowa ba, zai yi nasara a zaven shugaban ƙasa mai zuwa. An kuma ambato Babalola na cewa ɗan takarar shugaban asa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi ne ya fi cancanta da ya gaji shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, jigon ACF ɗin…
Read More
NESG ta nemi ƙaruwar mata a harkokin siyasa da noma

NESG ta nemi ƙaruwar mata a harkokin siyasa da noma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasa ta Nijeriya (NESG), ta nemi a ƙara shigar da mata cikin harkokin siyasa da noma don ƙara ƙaimi ga cimma muradun cigaba mai ɗorewa a ƙasar. Dokta Osasiyi Dirisu, Mataimakiyar Darakta a Cibiyar Innovation Policy, NESG, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a wani taron manema labarai kan bugu na farko na Cibiyar Innovation Center (PIC) Gender and Inclusion Summit (GS-22) a Abuja. Dirisu ta ce, shigar da mata a fagen siyasa da kuma harkar noma zai taimaka wajen cimma manufofin SDG da inganta haɗa jinsi. Ta ce, babban taron da…
Read More
Gamayar ƙungiyoyin 1,000 NCPC ta yi babban taro a Kano

Gamayar ƙungiyoyin 1,000 NCPC ta yi babban taro a Kano

DAGA MUHAMMADU MUJJITABA a KANO Shugaban gamayar ƙungiyoyin bunƙasa rayuwar al`umma ta fanin ilimi kiwan lafiya da sauransu, Malam Askiya Sheikh Nasiru Kabara, ya jagoranci gangamin taron ƙungiyar da ya gudana a birnin Kano, a ranar Lahadin makon jiya. A jawabinsa ga mahalata gangamin ya ce, wannan ƙungiya an kafa ta ne domin talafawa ƙoƙarin hukumomi na bunƙasa harkar lafiya, ilimi, bunƙasa tattalin arziƙ, da sana oin dugaro da kai wanda aikin wannan ƙungiya zai bada gagarumar nasara wajen samar da zaman lafiya tsoro da kwanciyar hankali dama najeriya baki ɗaya kamar dai yadda shugaban wannad ƙungiya Malan Askiya ya…
Read More
FOSOGED ta horar da mata 20 ilimin na’urar kwamfuta a Kano

FOSOGED ta horar da mata 20 ilimin na’urar kwamfuta a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gidauniyar wayar da kai da cigaban Al'umma wato Faundation For Social Orientation and Gender Development (FOSOGED ta baiwa Yan mata 20 horo a kan naura mai ƙwaƙwalwa da ya gudana a Husna Plaza da ke unguwar Sharaɗa cikin Birnin Kano, A Jawabinta shugabar Ƙungiyar Hajiya Mariya Durumin iya ta bayyana cewa sun shirya Bada hoton ne don qara ƙarfafar 'yaya mata ta yadda duk wani vangare na cigaba a rayuwa su ma ya kasance su ma an dama da su musamman harkar fasahar sadarwa wanda a yanzu da shi ne duniya ta ke cigaba. 'Muna…
Read More
Dandalin shawara: Ba na sha’awar namiji sai mace ‘yar uwata

Dandalin shawara: Ba na sha’awar namiji sai mace ‘yar uwata

Data AISHA ASAS TAMBAYA: Good morning, my darling aunty Asas. How was your night? Sorry na yi kiran ki tun da safe, daga baya ƙawata ta ce, ai saƙo zan tura. Mun tava haɗuwa da jimawa, but I think you will not remember, saboda an jima, kan case na wata ƙawata da har ki ka je gidansu about her been raped. Yanzu ma wurinta na samu your number. Matsalata gaskiya I will be honest with you tun da mafita nake nema, wallahi ba na sha'awar namiji gabaɗaya, irin na fi feeling ina buƙatar mace idan na yi sha'awar abin, amma…
Read More
Tinubu ya naɗa Jega da Abdulaziz hadimansa

Tinubu ya naɗa Jega da Abdulaziz hadimansa

Daga WAKILINMU Ɗan takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa gogaggun 'yan jarida biyu hadimansa domin ƙarfafa ofishinsa na yaɗa labarai. Waɗanda aka naɗa ɗin su ne; Mahmud Jega a matsayin Mai ba da Shawara na Musamman Kan Sha'anin Hulɗa da Jama'a, sai Abdulaziz Abdulaziz, Hadimi na Musammam Kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a. Kafin naɗin nasa, Jega mai fashin baƙi ne a tashar Arise TV, kuma marubuci a jaridar Thisday, ya kuma riƙe muƙamin Babban Edita na jaridar intanet ta 21st Century Chronicle. Shi kuwa Abdulaziz, zaƙaƙurin ɗan jarida ne wanda har…
Read More
Ban san inda na caka wa Ummita wuƙa ba, cewar ɗan Chana

Ban san inda na caka wa Ummita wuƙa ba, cewar ɗan Chana

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano A cigaba da zaman sauraron shari'ar ɗan asalin ƙasar Sin ɗin nan, Mista Frank Geng, da ake zargin ya kashe budurwarsa mai suna Umulkhulsum Sani Buhari dake zaune a Unguwar Janbulo cikin birnin Kano tun kimanin watannin baya, Mista Geng ya faɗa wa kotu cewa, bai san inda ya caka wa Ummita wuƙa ba. A zaman na jiya Alhamis, 12 da Laraba 11 ga Janairu, 2023, da ya gudana a babbar kotun jihar Kano ƙarƙashin Mai Shari'a Sanusi Ado Ma'aji, Frank ya ce, ya kashe wa Ummita sama da Naira miliyan sittin daga haɗuwarsu…
Read More
2023: Da alama INEC ba za ta ci kasuwa da malaman jami’a ba

2023: Da alama INEC ba za ta ci kasuwa da malaman jami’a ba

Daga BASHIR ISAH Da alama Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta shirya yin amfani da jami'anta a matsayin turawan zaɓe a zaɓen 2023 maimakon amfani da malaman jami'o'i kamar yadda ta saba a baya. Majiya mai tushe daga hukumar ta shaida wa jaridar News Point Nigeria cewa, kawo yanzu ba a yi batun amfani da malaman jami'o'i a shirye-shiryen da INEC ke yi dangane da zaɓen na bana ba. A cewar majiyar, "Kimanin kwana 40 kafin zaɓe ke nan amma ba a ce komai ba game da sako malaman jami'o'i a shirye-shiryen da hukumar ke yi. "Da kamar yadda aka…
Read More
Fitaccen ɗan wasan barkwanci, ‘Papa Ajasco’ ya kwanta dama

Fitaccen ɗan wasan barkwanci, ‘Papa Ajasco’ ya kwanta dama

Daga WAKILINMU Tsohon ɗan fim a masana'antar Nollywood, Femi Ogunrombi da aka fi sani da Papa Ajasco, ya kwanta dama. Ɗaya daga cikin masu shirya fina-finai, Husseini Shaibu ne ya sanar da rasuwar tasa a shafinsa na Tiwita ranar Lahadi. “Na samu sanarwar rasuwar 'Papa Ajasco', Mr Femi Ogunrombi daga majiya mai tushe….," in ji sanarwar. A halin rayuwarsa, Papa Ajasco ya yi fice a fim ɗin barkwanci mai dogon zango shiryarwar kamfanin Wale Adenuga Production. Ogunrombi ya maye gurbin jarumi Abiodun Ayoyinka ne a matsayin Papa Ajasco a cikin shirin bayan da Ayoyinka ɗin suka samu matsala da furodusansa.
Read More