Editor

9513 Posts
Gobara ta babbake hedikwatar ‘yan sanda a Kano

Gobara ta babbake hedikwatar ‘yan sanda a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano A yammacin Asabar gobara ta tashi a hedkwatar 'yan sanda ta Kano da ke unguwar Bompai. Rahotanni sun nuna gobarar ta tashi ne daga ofishin Provost ta kuma bazu zuwa sashen kuɗi da ɗakin taro da ofishin Kakakin hedikwatar da ofishin mataimakin kwamishinan 'yan sanda (Admin) da sauransu. Mai magana da yawun 'yan sanda na Jihar Kano, Abdullahi Haruna, ya shaida wa Freedom Radio cewa ba a samu asarar rai ba, kuma wutar ba ta taɓa wasu muhimman takardu ba. Binciken Manhaja ya gano wutar ta shafi dukkan ofisoshin da ke saman bene na ɗaya na…
Read More
Makomar tallafin fetur a Nijeriya bayan Yunin 2023

Makomar tallafin fetur a Nijeriya bayan Yunin 2023

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa zuwa Yunin 2023, za ta daina biyan kuɗin tallafin fetur da ta saba biya. Ministar kuɗi da kasafi ta ƙasar Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a lokacin da ta ke gabatar da kasafin na 2023 ga jama'ar ƙasar. Ta bayyana cewa a 2023, gwamnatin ta ware naira tiriliyan 3.36 ne kawai domin biyan tallafin fetur na wata shidan farko na shekarar. Ta kuma ce wannan matakin na tafiya ne da ƙarin wa'adi na watanni 18 na cire tallafin da aka sanar a 2022. A lokacin da take bayani kan gundarin kasafin, ministar ta bayyana…
Read More
Dalilin da ya sa muka bada umarnin tsare Doyin Okupe – EFCC

Dalilin da ya sa muka bada umarnin tsare Doyin Okupe – EFCC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta ce, ta bayar da umarnin tsare tsohon mai ba Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan shawara kan Harkokin Jama’a, Doyin Okupe, bisa buqatar sa-ido da ta gabatar a ranar 18 ga watan Yulin shekarar 2016, sama da shekaru shida kafin a yanke masa hukunci a kan tuhume-tuhumen kuɗi da babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi. Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama tsohon Shugaban Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP, Doyin Okupe. A cewar lauyansa Tolu Babaleye, an kama…
Read More
An shiga watan taƙaitawa da daina aiki da tsoffin kuɗi

An shiga watan taƙaitawa da daina aiki da tsoffin kuɗi

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA An shiga watan taƙaitawa da kuma daina aiki da tsoffin kuɗi. Wannan ya ƙara bayyana ne bayan isa 9 ga watan nan na Janairu inda ya ke ƙa’idar taƙaita fitar da kuɗi a na’urorin kuɗi na ATM a Nijeriya. Babban bankin Nijeriya CBN ya fara aiwatar da sabuwar ƙa’idar da kuma nuna hakan ba zai kawo wata matsala ba a Nijeriya. Tuni hakan na nuna an fara aiki da tsarin nan na rage amfani da takardun kuɗi don haka ya zama ko dai kowa ya yi ƙoƙarin komawa aiki da na’urori ko kuma ya riƙa shan…
Read More
Kawo ƙarshen cutar Kwalara

Kawo ƙarshen cutar Kwalara

A cikin rahotonta na baya-bayan nan, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya ta sanar da jimillar mutane 19,228 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara, ciki har da mutuwar mutane 466 a shekarar 2022. A ra'ayin wannan jarida, wannan lamari ne mai firgitarwa da ya kamata gwamnati ta ɗauki nauyinsa daqile shi a kowane mataki. Kwalara cuta ce da ake saurin kamuwa da ita da ta ke haifar da gudawa da amai. Ana kamuwa da ita daga najasa ta hanyar gurvataccen abinci, abin sha, da rashin tsafta, kuma yana haifar da rashin ruwa a jikin ɗan adam. Yawan masu…
Read More
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kaduna ya sauya sheƙa daga APC zuwa LP

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kaduna ya sauya sheƙa daga APC zuwa LP

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Isaac Auta Zankai da wani ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazavar Zariya, Suleiman Dabo, sun fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar LP. Sakataren Jam’iyyar LP na Ƙasa kuma Shugaban Majalisar Gwamnan Jihar, Umar Farouk Ibrahim ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar mai wakilai 450 da kuma aaddamar da taronta a Kaduna ranar Alhamis. Ibrahim ya ce, rabin ’yan majalisar dokokin jihar magoya bayan takarar Obi-Datti nd, inda ya ce goyon bayan da aka samu daga masu kishin jihar, alama ce da…
Read More
Gwamnan Anambra ya roƙi Buhari ya saki Kanu, ya ce zai tsaya masa

Gwamnan Anambra ya roƙi Buhari ya saki Kanu, ya ce zai tsaya masa

Daga BASHIR ISAH Geamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya roƙi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan ya hanzarta sakin jagoran IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ba tare da gindaya wani sharɗi ba. Soludo ya yi wannan roƙo ne yayin da yake jawabi a wajen taron siyasa ranar Asabar a Awka, babban birnin jihar. Ya ce, “Ina roƙo Gwamnatin Tarayya kan ta saki Mazi Nnamdi ba tare da wani sharaɗi ba. Ina son a sakar mini shi, zan tsaya masa. “Muna da buƙatar Nnamdi Kanu domin tattauna matsalar a yankin Kudu maso Gabas. Dole mu murƙushe matsalar tsaro a yankin Kudu maso Gabas,…
Read More
A karon farko za a fara haska wasannin gasar Saudiyya a tashar DSTV

A karon farko za a fara haska wasannin gasar Saudiyya a tashar DSTV

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Bayan naɗa Cristiano Ronaldo a matsayin sabon ɗan wasan ƙungiyar Al Nassr ta ƙasar Saudiyya, hukumar gasar sun ƙulla yarjejeniya da DSTV don yaɗa wasannin gasar Larabawa a tashar DSTV. Za a nuna gasar Larabawa ta talabijin a Channel 240. Kowa zai iya kallon wasannin Al Nassr a tashar 240. Wannan shi ne karo na farko a tarihi da za a nuna gasar wasannin Asiya ta talabijin a tashar DSTV. A ɗaya ɓangaren kuma, Hukumomin Saudiyya na shirin kau da kai daga dokokin auratayya ta ƙasar domin yarjewa sabon tauraron ɗan wasan da ƙungiyar Al Nassr…
Read More
APC Arewa Community tana taka rawar gani a Legas – Sa’adu Yusuf

APC Arewa Community tana taka rawar gani a Legas – Sa’adu Yusuf

Daga DAUDA USMAN a Legas An bayyana cewar Ƙungiyar APC Arewa Community a Legas a ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙungiyar na jihar Legas Alhaji Sa'adu Yusuf Dandare Gulma, tana taka rawar gani a Legas da kewayenta. Shugaban ƙungiyar na Ƙaramar Hukumar Mailan dake cikin garin Legas Alhaji Adamu Abdullahi Abubakar ya tabbatar da hakan jim kaɗan bayan tashi daga taron da ƙungiyar ta APC Arewa kwaminiti ta shirya wa ɗan takarar shugabancin ƙasar nan a ƙarƙashin inuwar Jam'iyyar APC tsohon Sanata Bola Ahmed Tinubu 'yan siyasar Nijeriya gaba ɗaya domin goya masa baya a lokacin gudanar zaɓuɓɓuka masu zuwa. Taron wanda…
Read More
Za a fara aikin haƙo fetur a Nasarawa a Maris – NNPC

Za a fara aikin haƙo fetur a Nasarawa a Maris – NNPC

Daga BASHIR ISAH Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPCL), ya ba da sanarwar shirinsa na fara haƙo fetur a Jihar Nasarawa a watan Maris mai zuwa. Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya snaar da hakan ga Gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule, yayin da Gwamnan ya ya jagoranci wata tawagar jihar zuwa ziyarar NNPC a Abuja. Kyari ya ce wannan ɓangare ne na ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na gano fetur a sassan ƙasar. Bayanin na ƙunshe ne cikin sanarwar da Shugaban sadarwa na kamfanin, Garbadeen Muhammad, ya fitar ranar Juma'a. “Dole a gaggauta aiwatar da aikin, saboda duniya na karkata…
Read More