Editor

9513 Posts
Atiku zai cefanar da komai na Nijeriya ga ‘yan kasuwa, ka da ku zaɓe shi – Gargaɗin Tinubu ga ‘ya Nijeriya

Atiku zai cefanar da komai na Nijeriya ga ‘yan kasuwa, ka da ku zaɓe shi – Gargaɗin Tinubu ga ‘ya Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja “Atiku…baya son gina kasa mai inganci a maimakon haka zai gwammace ya sayar da hakin ku na haihuwa ga manyan magina,” in ji Mista Tinubu. Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya sake caccakar Atiku Abubakar, yana mai cewa ɗan takarar Jam’iyyar PDP ba zai iya zama Shugaban Nijeriya ba. Tinubu, wanda ya yi magana a taron yaqin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC a Ondo, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai sayar da Nijeriya ga ‘yan kasuwa mafi girma idan an bar shi ya yi mulki. “Atiku…
Read More
2023: Kar ku zaɓi masu yanka filin masallatai – Gargaɗin Kahlifa Sunusi

2023: Kar ku zaɓi masu yanka filin masallatai – Gargaɗin Kahlifa Sunusi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Khalifan Tijjaniya, kuma tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Lamido na II a wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumuntar zamani an hango Muhammadu Sanusi Lamido yana bai wa masu zave shawara kan yadda za su jajirce wajen zaɓen waɗanda suke so ba wanda ya kwashe musu kuɗi ba. Lamido yana cewa ka da mutane su zaɓi mutanen da za su kwashe musu kuɗinsu, "mutum ya shekara huɗu yana sayar da filayenku, yana sayar da masallatai, yana sayar da makabartunku, yana sayar da makarantunku, yana sayar da ganuwarku da asibitocinku ya tara kuɗi ya…
Read More
Raha nake yi, cewar matar da ta ce ta tara Naira biliyan guda da cinikoin ƙuli-ƙuli

Raha nake yi, cewar matar da ta ce ta tara Naira biliyan guda da cinikoin ƙuli-ƙuli

Daga AMINA YUSUF ALI Wata matashiyar mai suna Angela Job Emodiae, wacce ta yi ikirarin cewa ta haɗa Naira biliyan guda a cinikin ƙuli-ƙuli, ta yi amanta ta lashe. Inda ta bayyana cewa ta faɗa ne kawai don saboda raha.   Idan za a iya tunawa, a ranar Asabar ɗin da ta gabata ne, 7 ga watan Janairun 2023 matashiyar mai suna Angela wacce take zaune a garin Jos ta jihar Filato, mamallakiyar kamfanin Anjees Food, ta wallafa a shafinta na dandalin Fesbuk cewa, ta haɗa Naira biliyan guda a kan cinikin ƙuli-ƙuli. Sannan ta ƙara da cewa, a wannan shekara…
Read More
An naɗa Musulmin da ba ɗan jiha ba muƙamin kwamishina a Kuros Riba

An naɗa Musulmin da ba ɗan jiha ba muƙamin kwamishina a Kuros Riba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A karon farko an naɗa Musulmi ba da ɗan asalin jihar ba tare da rantsar da shi a matsayin kwamishina kuma memba a majalisar zartarwa ta Jihar Kuros Ribas da ke Kudancin Nijeriya. An naɗa Farfesa Ben Ayade, ya rantsar da Alhaji Adamu Uba Musa, Dr. Janet Ekpenyong, da wasu mutane goma sha ɗaya a matsayin sabbin kwamishinonin kula da harkokin gwamnatoci da lafiya a ranar Talata. Bayan faruwar haka, Alhaji Musa ya zama Musulmi na farko da ba ɗan asalin jihar ba da aka naɗa a matsayin Kwamishina a jihar. Gwamnan ya kuma yi amfani…
Read More
Ganduje ya nemi ICPC, EFCC da Majalisar Tarayyar su binciki Hukumar Alhazai

Ganduje ya nemi ICPC, EFCC da Majalisar Tarayyar su binciki Hukumar Alhazai

Daga AMINA YUSUF ALI Ƙungiyar gamayyar ƙungiyoyi masu zaman kansu (CSO), sun goyi bayan kiran da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi, inda ya nemi hukuma mai zaman kanta ta hukunta laifin cin hanci da rashawa da laifuka masu alaqa da hakan (ICPC), da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa  (EFCC), da kuma Majalisar tarayyar ƙasar nan a kan su yi bincike a kan hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) game da kuɗaɗen tafiyar da harkar alhazai na shekarar 2022, da kuma kwangilolin da aka ba hukumar. Gwamna Ganduje ya yi wannan…
Read More
Wutar lantarki ta yi ajalin ma’aurata da ‘ya’yansu a Zariya

Wutar lantarki ta yi ajalin ma’aurata da ‘ya’yansu a Zariya

Daga WAKILINMU Aƙalla mutum huɗu sun mutu sakamakon wutar lantarki da aka kawo da ƙarfi a rukunin gidaje da ke Ƙofar Gayan a Zariya, Jihar Kaduna. Wani ganau mai suna Malam Sagir Nata'atala, ya ce iftila'in ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren Juma'a bayan da aka maido da wutar lantarki a yankin. Ya ce marigayan ma'aurata ne sai kuma 'ya'yansu biyu wanda dukkansu gobarar ta yi ajalinsu. Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Shugaban Kwana-kwana na shiyyar Kaduna, Malam Umar Bello, ya ce gobarar ba ta rasa nasaba da tartsatsin wutar lantarki sakamakon maido da wutar da…
Read More
Yanayin albashin Messi idan Al-Hilal ta samu nasarar saye shi

Yanayin albashin Messi idan Al-Hilal ta samu nasarar saye shi

Ga yadda albashin Lionel Messi zai kasance idan kulob ɗin Al-Hilal ta samu nasarar saye shi: Shekara: Biliyan N161.8 Wata: Biliyan N13.4 Mako: Biliyan N3.3bn Rana: Miliyan N481.7 Awa: Miliyan N20.7 Manhaja ta rawaito ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al-Hilal da ke Saudiyya na zawarcin ɗan wasan inda ta ce a shirye take ta biya shi Dalar Amurka miliyan 385 kwatankwacin biliyan N161.8 duk shekara.
Read More
Hisbah ta kama bokan da ya yi wa wata mata ciki a Kano

Hisbah ta kama bokan da ya yi wa wata mata ciki a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani boka da ake zargi da yi wa wata mata ciki bayan ta je wajen sa neman magani. Bokan mai suna Muhammad Mansur, mazaunin Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu an kama shi bayan matar da ba a bayyana sunanta ba, ta kai qara tana neman a bi mata haqqin ɗauke da cikin wata bakwai. Rahotanni daga garin na nuna cewa bokan ya yi fice wajen yaudarar mata, ciki har da matan aure. Bokan na yaudarar mata ta hanyar shaida masu cewa idan suka kwana da shi zai ba su…
Read More
‘Yan ta’adda sun kashe jami’an NSCDC bakwai a wajen haƙar ma’adinai a Birnin Gwari

‘Yan ta’adda sun kashe jami’an NSCDC bakwai a wajen haƙar ma’adinai a Birnin Gwari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu da ake kyautata zaton 'yan fashin daji ne sun kai hari kan jami’an hukumar tsaron farar hula, NSCDC, inda su ka kashe bakwai daga cikinsu a wani wurin haƙar ma’adinai, a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna. Wata majiya ta shaida wa Daily Nigerian cewa ‘yan bindigar sun rasa mamba guda ɗaya a yayin wani artabu da 'yan bindigar a wurin haƙar ma’adinai da wasu ‘yan ƙasashen waje ke gudanarwa a ƙaramar hukumar. A cewar majiyar, tuni aka ajiye gawarwakin jami’an a asibitin ƙwararru na Barau Dikko da ke cikin babban birnin…
Read More
Al-Hilal na zawarcin Messi kan biliyan N161.8 a shekara

Al-Hilal na zawarcin Messi kan biliyan N161.8 a shekara

Daga BASHIR ISAH Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Saudiyya, wato Al-Hilal, na zawarcin gwarzon ɗan wasan nan na Argentina, Lionel Messi kan kuɗi Dalar Amurka miliyan 385, kwatankwacin Naira biliyan 161.8. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da babbar abokiyar hamayyar Al-Hila ɗin, wato Al-Nassr ta saye shahararren ɗan wasan nan Cristiano Ronaldo. Da alama dai, Saudiyya ta ba da himma wajen ganin ta mallake gwarazan da ake ji da su a duniyar ƙwallon ƙafa. Domin saye Messi, dole Al-Hilal ta yi aman Dala miliyan $385, farashin da ake ganin ba kowa zai iya biya a kan ɗan wasan ba.…
Read More