Editor

9513 Posts
Gwamnatin APC ta cika dukkanin alƙawuran da ta ɗauka wa ‘yan Nijeriya – Buhari

Gwamnatin APC ta cika dukkanin alƙawuran da ta ɗauka wa ‘yan Nijeriya – Buhari

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa a ƙarƙashin jam'iyyar APC ta cika dukkanin alƙawuran da ta ɗauka wa yan Nijeriya a lokacin yaqin neman zaɓe, saboda haka ya kamata 'yan Nijeriya su zaɓi Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima, kuma jama'ar Yobe su sake zaɓar Gwamna Mai Mala Buni a karo na biyu tare da baki ɗayan 'yan takarar jam'iyyar a babban zaven 2023 mai zuwa. Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ga cincirindon magoya bayan Jam'iyyar APC, ranar Talata a taron gangamin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa wanda jam'iyyar ta…
Read More
Portugal ta kulla yarjejeniya da tsohon kocin Belgium

Portugal ta kulla yarjejeniya da tsohon kocin Belgium

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Portugal ta naɗa tsohon kocin Belgium, Roberto Martinez a matsayin sabon mai horasr da ’yan wasanta. Martinez, mai shekaru 49, ya maye gurbin Fernando Santos, wanda ya ajiye aikinsa bayan da Portugal ta sha kashi a hannun Morocco a wasan daf da na kusa da ƙarshe na gasar kofin duniya. Martinez ya ajiye aikin horar da Belgium ne bayan fitar da su daga gasar ta cin kofin duniya a Ƙatar a matakin rukuni, yana mai cewa ya yanke shawarar kawo ƙarshen wa’adinsa na shekaru shida ne tun a shekarun baya, dan haka da ma zai rabu…
Read More
Iran ta yanke wa Alireza Akbari hukuncin kisa bisa laifin zagon-ƙasa

Iran ta yanke wa Alireza Akbari hukuncin kisa bisa laifin zagon-ƙasa

Kakakin Hukumar Shari'ar Ƙasar Iran ya yanke hukuncin kisa kan wani mutum da aka samu da laifin aikata leƙen asiri, kamar yadda hukumar shari'a ta sanar a ranar Laraba da ta gabata. Hukumar ta yankewa Alireza Akbari hukuncin kisa bisa laifin cin hanci da rashawa a doron ƙasa da kuma zagon ƙasa ga tsaron ƙasar saboda yada bayanan sirri suka tabbatar. Har wa yau, ba ta bayar da cikakken bayani kan ranar da aka kama shi da kuma yanke irin ba, wanda kotun koli ta tabbatar da hakan. A farkon watan Janairu, an zartar da hukuncin kisa ga wasu Iraniyawa…
Read More
Gwamnatin Katsina ta ɗauki matakin bunƙasa noman mangwaro a faɗin jihar

Gwamnatin Katsina ta ɗauki matakin bunƙasa noman mangwaro a faɗin jihar

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari, ta ɗauki matakin bunƙasa ayyukan noman mangwaro a faɗin Jihar Katsina. Shugaban ƙungiyar masu noma da sarrafa mangwaro, ya ce an shirya horon ne domin a ƙarfafa guiwa tsakanin manoman mangwaro don inganta samar da kuɗaɗen shiga a jihar Katsina. Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir M.D na hukumar KATARDA, wanda ya samu wakilcin Alhaji Abubakar Dabo, ya bayyana cewa, taron zai taimaka matuqa ga mahalartan domin su samu ilimi na yadda ake dasa gami da rainon itatuwan mangwaro ya zuwa girmansu a zamanance. Ya ce hakan zai taimaka…
Read More
Ka yi kaɗan ka rushe sabbin masarautun Jihar Kano – Ganduje ga Abba Gida-Gida

Ka yi kaɗan ka rushe sabbin masarautun Jihar Kano – Ganduje ga Abba Gida-Gida

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kano ta shaida wa jam’iyyar adawa ta New Nigeria People’s Party, NNPP cewa shirinta na mayar da tsohon birnin ga tsohon masarautu tare da kakkave sabbin masarautu ba zai tava yiwuwa ba. Gwamnatin ta ce sabunta sheqar da ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya yi na sallamar sabbin masarautu idan aka zaɓe shi, hakan na nufin ba zai yi aiki da dokar kafa sabuwar masarautu da kuma shawarar da jama’a suka yanke. Gwamna Ganduje ta bakin Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na…
Read More
Direbobin tanka sun toshe hanyar Zariya-Kano bayan kashe abokin aikinsu

Direbobin tanka sun toshe hanyar Zariya-Kano bayan kashe abokin aikinsu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Direbobin tanka sun toshe babbar hanyar Zariya zuwa Kano a ranar Laraba don nuna tsantsan vacin ransu kan kashe ɗaya daga cikinsu da wani soja ya yi. Lamarin ya faru ne wajen misalin ƙarfe 3:30 na yamma, lokacin da direbobin suka haddasa mummunan cunkoson ababen hawa sakamakon rufe hanyar na tsawon sa’o’i. Ba a gano asalin abin da ya kai har sojan, wanda ke aiki tare da wani kamfanin gine-gine, ya kashe direban ba. Sai dai bayanai sun nuna lamarin ya faru ne a kusa da garin Tashar Yari da ke Ƙaramar Hukumar Makarfi ta Jihar…
Read More
Darajojin Ahlul Baiti a cikin hadisai

Darajojin Ahlul Baiti a cikin hadisai

Daga MUHAMMED BALA GARBA Akwai Hadisai da dama da suka yi magana a kan martabobi da darajojin Ahlul Baiti. Za mu takaita kan wasu hadissai ingantattu guda bakwai (7). Amma bari mu soma da waɗannan guda biyu waɗanda suke bayyana fifikon dangin Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) baki ɗaya akan sauran mutane. Tirmizi ya rawaito falalar Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) cewa: Abbas (Allah ya ƙara masa yarda) ya ce: “Na ce wa Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam), Ƙuraishawa sun zauna suna bitar tarihin gidansu. Sai suka kwatantaka da muruccin kan dutse. Sai Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Da Allah ya…
Read More
Akwai ƙalubale ga marubutan da suka dogara da rubutu kawai – Safna Jawabi

Akwai ƙalubale ga marubutan da suka dogara da rubutu kawai – Safna Jawabi

"Sanadin ababen da ke ƙunshe a zuciyata na fara rubutu" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Mata marubuta sun daɗe suna ba da gagarumar gudunmawa a vangaren cigaban adabi da harkokin rayuwa, saboda burin su na ganin sun kawo gyara a cikin al'umma da irin damar da suke da ita. Safna Aliyu Jawabi wata fitacciyar marubuciyar yanar gizo ce, daga Jihar Neja, wacce ta yi suna wajen fitar da littattafai da ke cike da darussa masu muhimmanci. A zantawarta da wakilin Manhaja a Jos, Safna ta shaida masa cewa, burinta na amfani da muryarta wajen kawo sauyi a rayuwar al'umma shi ya…
Read More
Abduljabbar ya ƙalubalanci hukuncin kisa da kotu ta yanke masa

Abduljabbar ya ƙalubalanci hukuncin kisa da kotu ta yanke masa

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Malam Abduljabbar Nasir Kabara wanda Kotu ta zartar wa da hukuncin kisa ta hanyar rataya ya ce bai gamsu da hukuncin da aka yi masa ba gaba ɗaya. Wannan na ƙunshe ne cikin wata takarda da lauyansa ya miƙa wa Babbar Kotun Jihar Kano. Cikin takardar, ya ce "Ni Abduljabbar ban gamsu da hukuncin da Kotun Shari’ar Musulunci ta Ƙofar Kudu ta yanke a kaina ba, a shari’a mai lamba CR/01/2021 da aka zartar ranar 15th Disamba, 2022, ƙarƙashin Alƙali Ibrahim Sarki Yola." Abduljabbar ya ɗaukaka ƙara zuwa Babbar Kotun jihar Kano bisa dalilin da ya…
Read More
Yadda karatun jami’a ke neman zama ƙwalele ga talakan Nijeriya

Yadda karatun jami’a ke neman zama ƙwalele ga talakan Nijeriya

Daga HARUNA UMAR JOS Ga dukkan alamu, shekarar 2022 ita ce shekarar ƙarshe da yaron talaka a Nijeriya zai tafi ƙaro karatu a jami'a (University), ganin yadda wasu takardu masu alaqa da wasu daga cikin jami'oin ke nuna yadda ake shirin ninka kuɗin makaranta, ko ma dai na ce an ninka! Ta iya yiwuwa wannan lamari yana da alaƙa da artabun da ke tsakanin gwamnati da malaman jami'o'i. Ko ma dai menene, da gwamnati da ku malamai, ku tuna fa wannan dambarwa taku a kan 'ya'yan talakawa take ƙarewa. Tana ƙarewa ne a kan mutanen da suke neman na sa…
Read More