Editor

9513 Posts
Matsalar jinyar ƙwaƙwalwa ce ke kai mata ga kashe mazajensu – Saratu G Abdul

Matsalar jinyar ƙwaƙwalwa ce ke kai mata ga kashe mazajensu – Saratu G Abdul

"Matsalar ƙwaƙwalwa cuta ce da ba a fiya damuwa wajen magance ta ba" "Ana yi wa matsalar ƙwaƙwalwa gurguwar ma'ana" Daga ABUBAKAR M. TAHEER Hajiya Saratu Garba Abdullahi ƙwararriya malamar jinya ce wadda ta ke koyarwa a Tsangayar Koyon Aikin Jinya na Jami'ar Bayero dake Kano. Sai dai a halin yanzu ta ke Ƙasar Amurka tana digirin na uku, wato PHD, kan Nursing Research. A cikin wannan tattaunawa ta musamman da ta yi da wakilin Manhaja a Haɗeja, ta kawo irin matsalolin dake damun ƙwaƙwalen mutane, waɗanda ke sanadin faɗawa a babbar matsala ko aikata aikin danasani ba tare da…
Read More
Taimakon jin ƙai a lokacin sanyi

Taimakon jin ƙai a lokacin sanyi

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A lokacin ƙarshen shekara tsakanin watannin Nuwamba da Disamba har zuwa Maris, a kan samu canjin yanayi da ke juyawa zuwa sanyi ke kasancewa da tsanani a wani wajen lokaci zuwa lokaci. A bana dai Hukumar Kula da Yanayin Muhalli ta Ƙasa, Nimet ta bayyana cewa, za a samu yanayin sanyi da hazo mai tsanani a wasu jihohin Arewa wanda ya taso daga yankin hamadar ƙasashen Chadi da Nijar. A cewar rahoton hazon da ke haɗe da ƙura zai shafi jihohin Borno, Yobe, Gombe, Katsina, Kano, Kaduna, da Jigawa za su samu hazo sosai, yayin da…
Read More
‘Yan sandan sun cafke ‘yan bindiga 2, sun ƙwace tarin alburusai a Zamfara

‘Yan sandan sun cafke ‘yan bindiga 2, sun ƙwace tarin alburusai a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama wasu da ake zargin masu yi 'yan bindiga safarar makamai ne a jihar. Kakakin rundunar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau ranar Talata. A cewarsa, abubuwan da aka ƙwato daga wajensu sun haɗa da harsashi guda 325 da kuma bindigar Ak47 guda ɗaya. “A ranar 8 ga Janairu, 2023 ne jami’an ‘yan sanda suka kama wasu ‘yan bindiga biyu, Emmanuel Emmanuel da takwararsa Nana Ibrahim a kan hanyar Gusau, Wanke zuwa Dansadau, da harsasai 325 da…
Read More
An cafke ‘yan bangar siyasa 50 a Zamfara

An cafke ‘yan bangar siyasa 50 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jami’an kwamitin yaƙi da ‘yan dabar siyasa a Jihar Zamfara sun kama wasu 'yan bangar siyasa magoya bayan Kam’iyyar PDP aƙalla mutum 50 a garin Gusau, babban birnin jihar. Shugaban kwamitin, Bello Mohammed Bakyasuwa ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a ofishinsa ga manema labarai ranar Talata. Bello ya ce, sama da mutum 30 daga cikinsu an same su da muggan makamai yayin gangamin siyasar ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Dr. Dauda Lawal Dare a Gusau. Ya ƙara da cewa, an kama su ne a…
Read More
Ɗan uwan ɗan sanda ya kashe shi ya sace bindigarsa

Ɗan uwan ɗan sanda ya kashe shi ya sace bindigarsa

Wani ɗan uwan wani ɗan sanda ya harbe shi har lahira sannan ya tsare da bindigarsa ta aiki. Ɗan sandan da ke gadin wani banki ya gamu da ajalinsa a hannun ɗan uwan nasa ne a yayin da suke shirin cin abincin rana a harabar bankin da ɗan sandan yake gadi. Majiyarmu ta ce, “abin ya faru da ɗan sandan mai muƙamin kofur ne a ranar Laraba lokacin da ɗan sandan ke wanke cokulan da za su ci abinci, bayan ya bar bindigarsa a bisa benci. “Sai makashin nasa ya ɗauki bindigar ya matsa kunamar sosai inda ya ɗirka masa…
Read More
Rashe-rashen da aka yi a masana’antun finafinan Nijeriya cikin 2022 (1)

Rashe-rashen da aka yi a masana’antun finafinan Nijeriya cikin 2022 (1)

Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da haɗuwar farko a sabuwar shekara cikin wannan shafi na Nishaɗi. Barka da ganin sabuwar shekara. Muna taya masoyan Manhaja murnar ganin shekarar 2023, Allah Ya linka mana alkhairan da muka samu a baya, Ya zaunar da mu lafiya a ƙasarmu, Ya azurta mu, Ya bamu cikar burikanmu. Masu iya magana dai na cewa, waiwaye adon tafiya. Wannan ne ya sa muka yi sha'awar waiwayawa shekarar da muka take, don share fage wurin kawo maku ƙayatattun labarai da tattaunawa tsakanin Manhaja da masu ruwa da tsaki a harkar finafinai har ma da su kansu…
Read More
Mu’assasin AMAA, Peace Anyiam-Osigwe ta rasu

Mu’assasin AMAA, Peace Anyiam-Osigwe ta rasu

Daga WAKILINMU Gwarzuwar shirya fina-finai a Nijeriya kuma mu'assasin Cibiyar ba da Kyaututtuka Kan Shirya Fina-finan Afirka (AMAA), Peace Anyiam-Osigwe, ta kwanta dama. Fitaccen darakta, Obi Emelonye ne ya tabbatar da rasuwar tata a shafinsa na Instagram da safiyar Talata. An ga yadda ya wallafa hotonta haɗi da saƙon ban-bakwana a shafin nasa. Kafin rasuwarta, marigayiyar ita ce Shugabar ƙungiyar masu shirya fina-finai ta 'Association of Movie Producer.'
Read More
Tsoffin ɗaliban sakandiren Gwarzo sun yi taron jaddada zumunci

Tsoffin ɗaliban sakandiren Gwarzo sun yi taron jaddada zumunci

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Ƙungiyar Tsofaffin Daliban Makarantar Sakandire ta Gwarzo sun gudanarda taron sada zumunci. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Bashir Abba Shariff a yayin taron da aka yi a ɗakin karatu na Murtala Muhammad ya ce basu tava haɗuwa irin na wannan lokacin ba, domin duk wanda suka rage a raye, sun zo taron daga sassa daban-daban na kiasar nan harma akwai wanda yazo daga ƙasar Ghana. Ya ce, maƙasudin taron shine don a farfaɗo da dangantaka ta asali mai ɗorewa a tsakaninsu dan ta cigaba da yaɗo duk da cewa kusan kaso 27 na daga cikinsu sun rasu,…
Read More
Masarautar Burumawa (1)

Masarautar Burumawa (1)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yau Manhaja za ta duba irin gwagwarmayar da ’ya’yan ƙabilar Burumawa suka yi wajen kafa masarautarsu a Jihar Filato. Burumawa, ƙabila ce wacce ta fi yawa a Ƙaramar Hukumar Kanam da ke Jihar Filato, yawanta ya kai kashi 80 cikin 100 na jama’ar ƙaramar hukumar. Haka kuma ana samun su a Ƙaramar Hukumar Wase, inda a can yawansu ya kai kashi 40 cikin 100 na jama’ar ƙaramar hukumar. Sannan ana samun su a garuruwan ƙananan hukumomin Lantang da Shendem da Kua’an-Pan da sauransu a Jihar Filato da wasu yankunan Tsakiyar Nijeriya kamar Wukari a Jihar…
Read More
Samar da zaman lafiya haƙƙi ne a kanmu, inji Fasto Buru‎

Samar da zaman lafiya haƙƙi ne a kanmu, inji Fasto Buru‎

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Cocin CEIFM da ke yankin Sabon Tasha a Jihar Kaduna, kuma Shugaban Ƙungiyar Samar da Zaman Lafiya da Sasanci ta Ƙasa ‘Peace Revival And Reconciliation Foundation’, Fasto Yohanna Buru, ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a samar da zaman lafiya a Jihar kaduna da ma ƙasar baki ɗaya.‎Yohanna Buru, wanda malamin addinin Kirista ne, ya ce, baya goyon bayan yadda ake musguna wa ’yan jaridu a Nijeirya da kuma yadda malaman addinai suke shiga cikin siyasa, wanda hakan yana da haɗarin gaske. A cewarsa, haƙƙin malamai ne faɗin gaskiya ga ɗaukacin mabiyansu, ba…
Read More