Editor

9513 Posts
Yadda ‘yan siyasa ke barazana ga sarautun gargajiya

Yadda ‘yan siyasa ke barazana ga sarautun gargajiya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A baya na taɓa yin wani rubutu mai kama da wannan, kuma a wannan shafi da ke tsokaci kan al'amuran yau da kullum, inda na nuna irin ƙalubalen da masu masarautun gargajiya ke fuskanta a hannun 'yan siyasa da masu mulki. To, abubuwa dai sai cigaba suke yi, ana cigaba da warware rawunan wasu sarakuna da masu riƙe da sarautun gargajiya saboda dalilai na siyasa. Sarakuna da dama na cikin zaman ɗar-ɗar saboda makomar rawanin su, musamman a jihohin da aka raba gari tsakanin jam'iyyar da Gwamna ke yi da kuma jam'iyyar da aka fahimci Sarki…
Read More
Yau Emefiele zai bayyana gaban kotu kan badaƙalar Dala miliyan 53

Yau Emefiele zai bayyana gaban kotu kan badaƙalar Dala miliyan 53

Daga WAKILINMU A wannan Larabar ake sa ran Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, zai bayyana a gaban Babbar Kotun Abuja dangane da shari'ar sama da Dalar Amurka miliyan 53 na kudaden ‘Paris Club’. A wata ƙara da aka shigar gaban kotun ranar 20 ga watan Oktoban 2022, Alkalin kotun, Mai Shari'a Inyang Ekwo ya bai wa Emefiele odar ya bayyana a gaban kotun ran 18 ga Janairu don sauraron shari'ar. Umarnin kotun ya biyo bayan ƙarar da lauya Joe Agi, ya shigar ne kan kamfanin Linas International Ltd da Ministar Kudi da CBN ta hannun lauyoyinsa, Isaac Ekpa…
Read More
Akwai masu fakewa da addini wajen cimma manufofinsu na siyasa – Buhari

Akwai masu fakewa da addini wajen cimma manufofinsu na siyasa – Buhari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya faɗa ranar Talata cewa, akwai masu fakewa da addini domin cimma manufofinsu a ɓangaren tattalin arziki da siyasa. Buhari ya ce akwai buƙatar ci gaba da bai wa fannin ilimi muhimmanci domin tafiya da galibin jama'a. Shugaban ya yi waɗannan kalaman ne a birnin Nouakchott, Mauritania, yayin da suke ganawa da Rashad Hussain, Jakadan Amurka kan 'yancin harkokin addini. Yayin tattaunawar tasu, Buhari ya tuno ganawarsa da tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump a fadar White House inda ya ce Trump ɗin ya tambaye shi kan cewa: “Me ya sa kake kashe Kiristoci…
Read More
Taƙaddama tsakanin surukai a ƙasar Hausa: Ina mafita?

Taƙaddama tsakanin surukai a ƙasar Hausa: Ina mafita?

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako za mu kawo muku wasu ƙarin dalilan da suke kawo lalacewar alaƙa tsakanin surukai a ƙasar Hausa, ta yadda surukuta a ƙasar Hausa ta zama kamar gaba a tsakaninsu. Kowa kishi da hassada yake wa ɗanuwansa. Ga rainin wayo, abin ba a magana. A wancan rubutun da na yi a baya, mun kawo wasu daga cikin dalilan da suka sa hakan take faruwa domin masu karatu su yi alƙalanci su gano wai shin ma laifin wanene? To a yanzu za mu ci…
Read More
Rashe-rashen da aka yi a masana’antun finafinan Nijeriya cikin 2022 (2)

Rashe-rashen da aka yi a masana’antun finafinan Nijeriya cikin 2022 (2)

Daga AISHA ASAS A satin da ya gabata, idan mai karatu bai manta ba, mun fara da kawo rashe-rashen da aka yi a masana'antar fim ta Arewacin Nijeriya, wato Kannywood. A wannan satin, za mu ci gaba ne ta hanyar kawo na ɓangaren takwarorinsu da ke Kudu, wato Nollywood: Idan muka juya ɓangaren masana’antar fim ta Kudu, wato Nollywood, shekarar 2022 ta tafi bayan ta bar masu tabo na daga mutuwar matasa da kuma tsofafi daga cikin wannan masana’anta. Daga watan Junairu zuwa Disamba, an ruwaito mutuwar iyalan wannan masana’anta har 17, waɗanda kansu za mu yi waiwaye da kuma…
Read More
Masarautar Burumawa (2)

Masarautar Burumawa (2)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A makon jiya ne muka fara kawo kashi na farko na tarihin Masarautar Burumawa da ke Jihar Filato, to yau cikin ikon Allah za mu kawo kashi na biyu. Taron ’yan jarida na duniya A ranar 15 ga Afrilun 1986, al’ummar Burumawa suka gudanar da taron ’yan jarida a garin Jos, taron da ya samu halartar wakilan jaridu da gidajen rediyo da dama ciki har da na ƙasashen waje. Bayan karanta tarkardar bayan taro da Sallah Dashe ya yi a matsayinsa na Shugaban Ƙungiyar Ci gaban Burumawa, jawabin ya samu yayatawar jaridu sosai ciki har da…
Read More
CBN ya samar da katin ATM na bai ɗaya

CBN ya samar da katin ATM na bai ɗaya

Daga BASHIR ISAH A matsayin ɓangaren na ƙoƙarin da yake yi na inganta sha'anin hada-hadar kuɗi a ƙasar nan, Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya samar da katin cire kuɗi (ATM) na bai ɗaya. CBN ya ce da wannan sabon katin na ATM, za a sadar da ko asusuwa nawa mutum ke da su da katin ta yadda za a iya amfani da katin wajen cire kuɗi a na'urorin ATM a bankuna daban-daban da sauransu. Katin mai taken '1 BVN = 1 ATM CARD' in ji CBN, zai yi aiki ne a tsakanin bankunan da ke mabobi a tsarin mu'amalar bankuna,…
Read More
Emefiele ya koma bakin aiki bayan kammala hutu

Emefiele ya koma bakin aiki bayan kammala hutu

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya koma bakin aiki bayan kammala hutun da ya ɗauka. Sanarwar da CBN ya fitar ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Daraktan sadarwa na bankin, Osita Nwanisobi, ta ce a Disamban da ya shuɗe Emefiele ya ɗauki hutu. Kuma ya dawo bakin aiki da sabbin dabaru kafin taron farko na Kwamitin Dokar Kuɗi (MPC) wanda zai gudana ran 23 zuwa 24 ga Janairun 2023. Sanarwar ta ƙara da cewa, Emefiele na jaddada ƙoƙarinsa wajen aiwatar da ayyukan da suka rataya a kansa daidai da doka da kuma umarnin Shugaban…
Read More
Mace da kwalliya aka san ta

Mace da kwalliya aka san ta

Daga MARYAM Mace da kwalliya aka san ta, wacce ba ta kwalliya ba ta cika mace a zahirin ta ba. Babu mace mummuna sai dai macen da ba ta kwalliya. Sai dai kwalliyar ma kala-kala ce, wasu kwalliyar suna suka tara, don ba zai yiwu a shafa foundation a fuskar da ba ta da haske a yi tsammanin samun kwalliyar raɗau ba. In na ce haske ba ina nufin farin fata ba, ina nufin ƙyalli na gyara. Yawancin mutanenmu suna tsorata da maganar kayan gyaran jiki don tsadar su, a rashin saninsu da kuɗi ƙalilan za su samu biyan buƙata…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: DSS ta ƙaryata mamaye CBN

Da Ɗumi-ɗumi: DSS ta ƙaryata mamaye CBN

Hukumar tsaro ta DSS ta ce, ba ta mamaye hedikwatar CBN da ke Abuja ba kamar yadda rahoto ya karaɗe wasu kafafen yaɗa labarai. DSS ta bayyana haka ne cikin taƙaitacciyar sanarwar da ta fitar ta bakin kakakinta, Peter Afunanya, ranar Litinin a Abuja. Afunanya ya ce hankalin DSS ya kai kan wani rahoton ƙarya da aka yaɗa wanda ke nuni da jami'an hukumar sun mamaye hedikwatar CBN da ke Abuja. Tun farko Daily Nigerian ta rawaito jami'an DSS sun mamaye CBN tare da karɓe ikon ofishin Gwamnan bankin, Godwin Emefiele, inda aka ce sun hana ma'aikata shiga ofishin.
Read More