20
Jan
Dag WAKILINMU Wata kotu mai zamanta a Dei-Dei, Abuja, ta yanke wa wani matashi mai suna Anas Ibrahim, hukuncin sharar masallaci na tsawon wata shida bayan kama shi da laifin bai wa ɓarayi masauki. Wani mai suna Ibrahim da ke kasuwar kayan gwari a Zuɓa ya amsa tuhumar cewa yana ɗaya daga wani gungun ɓarayi tare da roƙon kotu ta yi masa sassauci. Alƙalin kotun, Saminu Suleiman, ya bai wa mai laifin umarnin ya share Babban Masallacin Zuɓa na wata shida ko kuma ya biya tarar N20,000. Tun da farko, lauyan mai gabatar da ƙara, Chinedu Ogada, ya faɗa wa…
