Editor

9513 Posts
Masarautar Katsina ta tuɓe Makamanta, Sule Idris

Masarautar Katsina ta tuɓe Makamanta, Sule Idris

Daga BASHIR ISAH Masarautar Katsina a Jihar Katsina, ta tuɓe Alh. Idris Sule Idris a matsayin Makaman Makamanta. Sanarwar haka na ƙunshe ne cikin wasiƙar da masarautar ta aike wa basaraken mai ɗauke da lamba KEC/O12/BKRLG/NOL.III/87 da kuma kwanan wata 19 ga Janairu, 2023. Wasiƙar wadda ta samu sa hannun Wakilin Sarki kuma Ƙauran Katsina, Alh. Aminu Nuhu Abdulkadir, ta nuna Masarautar ta ɗauki wannan mataki ne saboda ƙorafe-ƙorafen da aka samu a kan wanda lamarin ya shafa. A cewar wasiƙar, "Bisa ga takardar da Majalisar Mai Martaba Sarkin Katsina, Alh. Dr Abdulmumini Kabir Usman CFR, ta samu daga Ofishin…
Read More
Samar da maƙabartar Kiristoci a Bauchi: Gwamnati ta buƙaci jama’a su kai zuciya nesa

Samar da maƙabartar Kiristoci a Bauchi: Gwamnati ta buƙaci jama’a su kai zuciya nesa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamnatin Jihar Bauchi ta buƙaci al'ummomin Musulmi da na Kiristoci mazauna unguwannin Yolan Bayara dake cikin gundumar Miri ta Ƙaramar Hukumar da su riƙa kai wa zukatunsu nesa da zummar wanzar da zaman lafiya, mutunta juna, yakana, tare da shure bambance-bambance dake a tsakanin domin nusar da cigaban jiha da ƙasa baki ɗaya. Mai bai wa gwamnan jiha shawarwari akan kafofin watsa labarai da yayatawa, Mukhtar Gidado Mohammed shine ya gabatar da wannan buƙata ta gwamnatin jiha dangane da taƙaddama dake gudana a tsakanin al’ummomin guda biyu, yana mai cewar, filin maƙabarta da ake taƙaddama…
Read More
Keyamo ya yi ƙarar EFCC da ICPC a kotu, ya nemi su tuhumi Atiku

Keyamo ya yi ƙarar EFCC da ICPC a kotu, ya nemi su tuhumi Atiku

Daga AMINA YUSUF ALI Festus Keyamo, mai magana da yawun majalisar kamfe ta jam'iyyar APC, ya shigar da ƙara a kan hukumar hana cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), yana neman kotu ta kama Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP na shugabancin Nijeriya. A cikin ƙarar, Festus Keyamo wanda lauya ne mai muƙamin SAN ya haɗa da dokar Hukumar daƙile laifukan cin hanci da makamantansu (ICPC) Hukumar kula da dokar ɗa'ar aiki (CCB) a cikin ƙarar, bayan wa'adin awoyi 72 da ya bayar sun cika. Keyamo, lauya mai muƙamin SAN, ya ba da…
Read More
Mace mafi tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 118

Mace mafi tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 118

Matar da ta fi tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 118 a birnin Toulon da ke yankin yammacin Faransa kamar yadda magajin garin ya sanar a hukumance. An haifi Lucile Randon da ta kasance malamar majami’a a ranar 11 ga watan Fabairun shekarar 1904, wato bayan shekaru 10 da kawo ƙarshen yaƙin duniya na farko, yayin da aka sanya ta a cikin jerin mutane mafiya tsufa a duniya a cikin watan Afrilun bara. Bafaranshiyar ta yi aiki a matsayin malama mai koyarwa a gida a lokacin da take matashiya, wato gabanin ta mayar da hankali kacokan kan hidimar…
Read More
‘Yan bindiga sun sace ɗaliban firame a Nasarawa

‘Yan bindiga sun sace ɗaliban firame a Nasarawa

Daga BASHIR ISAH Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari tare da yin awon gaba da ɗaliban da ba a tantance yawansu ba a wata makarantar firamare da ke ƙauyen Alwaza cikin Ƙaramar Hukumar Doma, Jihar Nasarawa. Jaridar Intelrigion ta rawaito maharan sun yi wa makarantar kwanton ɓauna ne a lokacin da yaran ke ƙoƙarin haɗuwa da safiyar Juma'a. Ya zuwa haɗa wannan rahoto, ba a kai ga sanin su wane ne maharan da kuma adadin yaran da suka sace ɗin ba. Da aka nemi jin ta bakinsa kan lamarin, mai magana da yawun 'yan sandan jihar,…
Read More
Aston Villa ta cimma yarjejeniyar ɗaukar Duran

Aston Villa ta cimma yarjejeniyar ɗaukar Duran

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Aston Villa ta cimma yarjejeniyar ɗaukar ɗan ƙwallon tawagar Colombia, Jhon Duran daga Chicago Fire. Duran, mai shekara 19, ya ci ƙwallo takwas ya kuma bayar da shida aka zura a raga a wasa 28 da ya yi wa Chicago. Kammala yarjejeniyar ta alakanta idan an auna koshin lafiyar ɗan wasan, sannan idan ya samu takardar shaidar aiki a Burtaniya. Ɗan ƙwallon zai yi takara a gurbi ɗaya da Ollie Watkins da Danny Ings a ƙungiyar da Unai Emery ke jan ragama, bayan da 'yan wasan biyu suka ci ƙwallo bakwai a tsakaninsu. Duran ya buga…
Read More
An kuɓutar da basaraken da aka yi garkuwa da shi a Filato

An kuɓutar da basaraken da aka yi garkuwa da shi a Filato

Daga BASHIR ISAH Bayanai daga Jihar Filato sun ce an kuɓutar da Sarkin Agwan Izere, Dr. Isaac Azi Waziri, wanda aka yi garkuwa da shi da sanyin safiyar Juma'a. Blueprint ta rawaito maharan sun yi garkuwa da basaraken ne a fadarsa da ke gundumar Shere a shiyyar Jos ta Gabas. Kakakin 'yan sandan Jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ya tabbatar da kuɓutar da Sarkin. Haka nan, ya ce an cafke wasu mutum biyu da ake zargin masu garkuwa ne da mutane a yankin.
Read More
Ministar Jinƙai, Sadiya Farouq, ta jaddada ƙudirinta na yin aiki da ƙungiyar haɗin gwiwar ma’aikatar

Ministar Jinƙai, Sadiya Farouq, ta jaddada ƙudirinta na yin aiki da ƙungiyar haɗin gwiwar ma’aikatar

Daga WAKILINMU Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwar Jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta jaddada ƙudirinta na kyautata hulɗar aiki da ƙungiyar haɗin gwiwa domin aiwatar da aikin ma’aikatar yadda ya kamata. Ministar ta bayyana hakan ne a yayin wani biki da ma'aikatar ta shirya mai taken: 'Makon Farko na Ƙungiya' a ranar 22 ga watan Disamba, 2022, a ɗakin taro na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya dake Abuja.  Ministar wadda ta samu wakilcin babban sakatare, Dr Nasir Sani Gwarzo, ta yaba wa ƙungiyar bisa aiki tuƙuru da kuma mutunta jami'an gudanarwa. Ta bayyana cewa, horarwa haƙƙi ne ga dukkan…
Read More
Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Azare ta ɗauki ɗaliban farko guda 760

Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Azare ta ɗauki ɗaliban farko guda 760

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Sabuwar Jami’ar Kimiyyar Ilimin Kiwon Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da take da mazauni a garin Azare cikin Jihar Bauchi ta ƙaddamar da ɗalibanta na farko guda 760 na zagon karatu na shekarun 2021/2022 da 2022/2023. Da yake yin matsakaicin jawabin fara karatun ɗaliban a garin Azare, muƙaddashin shugaban jami’ar, Farfesa Bala Mohammed Audu ya ce Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ne ya kafa jami’ar a watan Yuni na shekara ta 2021, kazalika an naɗa shugabanninta ne bada wani ɓata lokaci ba a ranar 27 ga watan Janairu na shekara ta 2022. “Yau muna yin jawabin fara…
Read More
CBN ya yi barazanar takunkumi ga bankunan dake raba tsofaffin takardun kuɗi

CBN ya yi barazanar takunkumi ga bankunan dake raba tsofaffin takardun kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sha alwashin hukunta bankunan da ke ci gaba da cika na’urorinsu na ATM da tsofaffin takardun kuɗi na Naira, a daidai lokacin da wa’adin cire kuɗaɗen ya gabato. Daraktan Sashen Kula da Harkokin Shari’a na CBN, Kofo Salam-Alada, wanda ya bayyana haka a wani taron wayar da kan jama’a a ranar Laraba 18 ga watan Janairu, 2023, a Kasuwar Computer Village da ke Legas, ya ce bankin ƙoli ya riga ya sanya ido ga bankuna kan lamarin. Daraktan wanda ya wakilci Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce babban bankin na da…
Read More