22
Jan
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin shugaba Muhammadu Buhari na iya fara cire tallafin man fetur sannu a hankali daga watan Afrilun 2023, kimanin watanni uku gabanin shirin farko na dakatar da shugaban na kashe kuɗaɗe. Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, Hajiya Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Talata yayin wata tattaunawa da ta yi da gidan talabijin na ARISE a gefen taron tattalin arzikin duniya da aka gudanar a birnin Davos na ƙasar Switzerland. Ta bayyana cewa, cire tallafin da alama matsayin duk masu neman shugabancin qasar ne a yaƙin neman zaɓensu na siyasa a…
