23
Jan
Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Tun da a ka fara mulkin dimokraɗiyya a Nijeriya wanda ya samo asali daga samun ’yancin ƙasar a 1960 an samu mulkin farar hula a zaɓuka daban-daban inda gabanin zaɓen 1999 an samu shigowar sojoji ne da su ka kifar da gwamnatin farar hula. A ranar 15 ga watan Janairun 1966 sojoji ’yan zubar da jini sun kifar da gwamnatin firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa wanda hakan ya jawo yankewar mulkin farar hula har sai a 1979 inda a ka gudanar da zave marigayi Shehu Shagari ya lashe a qarqashin jam’iyyar NPN mai alamar masara. A…
