Editor

9513 Posts
An cafke mutum 15 kan zargin fashi da ƙwacen waya a Zamfara

An cafke mutum 15 kan zargin fashi da ƙwacen waya a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a, Gusau Kwamitin Yaƙi da ‘Yan Daba na Jihar Zamfara ya kama wasu mutum 15 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da fashi da makami, sace-sacen waya da sauransu a Gusau, babban birnin jihar. Kwamandan kwamitin, Bello Mohammed Bakyasuwa ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a ofishinsa ranar Litinin. A cewarsa, an gabatar da waɗanda ake zargin a gaban majalisar tuntuɓar malamai ta jihar domin yi musu nasiha da ja-gora domin su zama jakadu nagari a yankunansu. Bakyasuwa ya bayyana cewa, kwamitinsa ba zai yi ƙasa a…
Read More
So kaɗai ba ya iya riƙe aure

So kaɗai ba ya iya riƙe aure

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon! Duk da dai Hausawa sun ce: "so Aljannar Duniya". Haka kuma sun ce; "so gishirin rayuwa". To amma masu dabara, zaman lafiya da maslaha da dacewar halayya suka zaɓa. Matasa kada ku yaudaru da waɗancan kalamai. Duk kuwa da zaqinsu kamar zuma sabuwa! Ku buɓe idanu da kunnuwa ku kalli gabanku. Ku guje wa yin aure don so kawai. Idan ka zavi dacewar halayya da tsarin rayuwa sai ka ga bayan an yi aure, soyayyar ta ginu a hankali. Ba a ce kada a yi auren soyayya ba, kuma…
Read More
Gangamin APC a Bauchi ya gamu da cikas, Buhari da Tinubu ba su yi jawabi ba

Gangamin APC a Bauchi ya gamu da cikas, Buhari da Tinubu ba su yi jawabi ba

Daga WAKILINMU Taron yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasa na Jam'iyyar APC a Jihar Bauchi ya gamu da cikas sakamakon ɗaukewar wutar lantarki da kayan amsa-kuwa. Wannan ya sa taron ya gudana ba tare da jin abin da masu ruwa da tsaki da suka samu yin jawabi a wajen taron ke faɗa ba Wannan matsalar in ji majiyarmu, ta faru ne saboda akasin ɗaukewar na'urorin magana sakamon ɗaukewar wutar lantarki. News Point Nigeria ta ruwaito cewa, har aka waste taron wanda ya gudana ranar Litinin a Filin Wasannin Motsa Jiki na Abubakar Tafawa Ɓalewa, Bauchi, Shugaba Buhari da ɗan takarar shugabancin…
Read More
Kotu ta bai wa DSS umarnin gurfanar da Tukur Mamu ko ta sake shi

Kotu ta bai wa DSS umarnin gurfanar da Tukur Mamu ko ta sake shi

Daga WAKILINMU Babbar Kotun Jihar Kaduna ƙarƙashin Mai Shari'a E. Andow, ta umarci hukumar tsaro ta DSS da ta gurfanar da Tukur Mamu ko kuma ta sake shi tare da wani mutum da take tsare da su. Umarnin na kotu na ƙunshe cikin takardar da aka raba wa manema labarai mai ɗauke da lambar ƙara KDM/KAD/1442/2022. Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da Tukur Mamu, Faisal Tukur Mamu, Ibrahim Hussain Tinja, Abdullahi Mashi, Mubarak Hussain Tinja da kuma Yahaya Bello. Yayin da DSS da Babban Lauyan Tarayya su ne waɗanda umarnin kotun ya rataya a wuyansu. Yayin zaman kotun, Mai…
Read More
Yadda mutuwar Jarumi Kamal Aboki ke shirin sauya akalar rayuwar matasa

Yadda mutuwar Jarumi Kamal Aboki ke shirin sauya akalar rayuwar matasa

Daga AISHA ASAS A ranar Litinin, 16 ga wannan watan ne labarin mutuwar jarumin barkwanci Kamal Aboki ta yi dirar mikiya a tsakanin kafefen sada zumunta da kuma masana'antar fim ta Kannywood, sakamakon kasancewar mutuwar ta fuju'a, wato ba-zata. An ruwaito cewa, Kamal ya mutu ne sakamakon hatsarin mota da ya yi a hanyar Maiduguri zuwa Kano. Wannan mutuwa ta matashi Kamal Aboki da ke tsaka da cin gajiyar lokacinsa ta ɗaga hankalin 'yan ciki da wajen masana'antar Kannywood. Za ka amince da hakan idan ka yi duba da yadda kafafen sada zumunta irin su Facebook, Instagram da kuma TikTok…
Read More
Magidanci ya kashe matarsa kan cinye masa burodi

Magidanci ya kashe matarsa kan cinye masa burodi

Wani magidanci ya kashe matarsa ta hanyar lakaɗa mata duka. Mutumin mai suna Wilson Uwaechina rahotanni sun ce ya kashe uwargidan ta sa ce mai suna Ogochukwu Anene saboda burodi. Bayanai sun ce marigayiyar ’yar asalin ƙauyen Umuokpu da ke yankin Ƙaramar Hukumar Akwa a Jihar Anambra, tana auren mijin nata ne mai suna Wilson Uwaechina daga jihar Enugu. Shaidun gani da ido sun ce tun farko rikici ya kaure tsakanin ma’auratan biyu ne akan gutsirin burodi. Mahaifiyar marigayiyar ta shaida wa manema labarai cewa, mista Wilson Uwaechina ya cinye gutsirin burodi da ta sayowa ’ya’yansu ne bayan da ta…
Read More
Zan rushe duk wani gini da aka yi a jikin badala idan na zama Gwamnan Kano – Dawisu

Zan rushe duk wani gini da aka yi a jikin badala idan na zama Gwamnan Kano – Dawisu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ɗan takarar Gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai da aka sani da Ɗawisu, ya bayyana cewa idan ya samu damar zama Gwamnan Jihar Kano zai rushe duk gine ginen da aka yi a jikin Badala a jihar. Salihu ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi a muhawarar ‘yan takarar Gwamna da ya gudana a ranar Lahadi a gidan Munbayya da ke Kano. Taron wanda Jami’ar Bayero da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu suka shirya ya samu halarta kusan mafi yawan 'yan takara na jam'iyyu daban-daban a Kano.
Read More
Ni’imarki, darajarki (1)

Ni’imarki, darajarki (1)

Daga AISHA ASAS Ni’ma na ɗaya daga cikin halittun da Allah ke yi waɗanda ke iya ƙaruwa ko raguwa, kuma ba a haramta ki nemi ƙarin ta ba matuƙar kin bi hanyoyi da suka dace. Abin haushi da takaici, a wannan zamanin ba abin da mata suka sa wa gaba face neman aljihun miji ko mallaka, ki dinga juya shi kamar waina. Wannan shi ne dalilin dake tsunduma mata da dama a halaka da sunan neman maganin ƙarin ni'ima, sakamakon ido rufe suke karɓar duk abinda aka zo masu da shi, matuƙar da sunan ni'ima ce. Idan kina cikin jerin…
Read More
Sai an samu ingantaccen tsari FACAN za ta yi nassara a Nijeriya – Alhaji Husaini

Sai an samu ingantaccen tsari FACAN za ta yi nassara a Nijeriya – Alhaji Husaini

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Alhaji Hussaini Saleh Ahamad, Shugaban Ƙungiyar Masu Ƙungiyar Fitar da Kayan Albarkatun Gona daga Nijeriya na Ƙasa (FACAN) ya ce, tsarin nan na 'commodities and export Department' (CID) da ake ƙoƙarin mayar da shi ta hanyar fasahar sadarwa ta zamani ba zai yi nasara ba sai an samu ingantaciyar wutar lantarki da ingantaciyar hanyar sadarwa ta zamani wato sabis sanan shirin zai samu kyakyawar nassara a Nijeriya. Shugaban ƙungiyar masu futar da amfanin gona da sauran kayayyakin waje shi ne ya bayana haka a lokacin bitar yini guda da ma'aikatar ciniki da masana'antu ta shirya…
Read More
Ƙungiyar Masana Harkar Gini sun gudanar da taron shekara a Kano

Ƙungiyar Masana Harkar Gini sun gudanar da taron shekara a Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Ƙungiyar Masana Harkar Gine-gine na Ƙasa (NIOB), reshen Jihar Kano, sun gudanar da taron shekara. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Muhammad' Sa'ad Umar ya ce, taron na shekara ne kamar yanda dokar qungiyarsu ta ƙasa ta tanada don a wayarda kan mutane sannan kuma a ƙarawa juna sani akan abinda ya shafi sabbin abubuwa da ya shafi gini. Sannan kuma a tattauna babbar matsalar dake ci musu tuwo a kwarya ta rushewar gine-gine a ƙasar nan gaba ɗaya musamman jihar Kano. Alhaji Muhammed Sa'ad Umar ya bada misali da cewa akwai gini da ya rushe na kan…
Read More