25
Jan
Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP a Jihar Abia, Farfesa Uchenna Ikonne, ya riga mu gidan gaskiya. Wannan na zuwa ne yayin da ya rage ƙasa da wata biyu kafin zaɓen 2023. Babban ɗan marigayin, Chikezie Uche-Ikonne ne ya tabbatar da rasuwar marigayin a ranar Laraba. “Cikin alhini nake sanar da rasuwar mahaifina, Farfesa Eleazar Uchenna Ikonne, wanda ya rasu a Babban Asibitin Ƙasa da ke Abuja,” in ji Uche-Ikonne. Sanarwar ta nuna ɗan takarar ya rasu ne da misalin ƙarfe 4:00 na asuba bayan fama da taƙaitaccen rashin lafiya. Ta ƙara da cewa nan gaba za…
