26
Jan
….Ta buƙaci Gwamnatin jihar ta gaggauta janye matakin hanin Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Masu Motocin Haya ta Ƙasa (RTEAN) ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Legas da ta gaggauta janye matakin hana motocin fasinja da suka fito daga Arewa shiga jihar. Cikin sanarwar manema labaraida ya fitar ranar Alhamis, Babban Sakataren RTEAN, Kwamred Yusuf Ibrahim Adeniyi, ya ce ƙungiyar ta samu labari daga reshenta na Jihar Kwara da wasu jihohin Arewa cewa Gwamnatin Legas ta ɗauki matakin hana motocin fasinja da suka fito daga Arewa shiga jihar. Ya ce, "Umarnin hakan ya fito ne daga jami'in Gwamnatin Jihar, Seyi Bamigbose…
