27
Jan
•Yadda al’amura suka kwaɓe Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya ce, zai bayar da umarnin a cafko masa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, da manajan daraktocin bankuna bisa kunnen uwar shegu kan sammacin da majalisar ta aika musu kan batun canjin sababbin takardun kuɗi. Kakakin Majalisar ya bayyana hakan a zauren majalisar jiya Alhamis, 26 ga Janairu, 2023, yana mai cewa, maimakon majalisar ta ɗage zamanta zuwa ranar 28 ga Fabrairu, 2023, bayan kammala zaven Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa, kamar yadda tun da fari aka tsara,…
