Editor

9513 Posts
NUJ ta cire ma’aikatan NOA daga jerin ‘ya’yanta

NUJ ta cire ma’aikatan NOA daga jerin ‘ya’yanta

Daga RABIU SANUSI a Kano Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) ta cire ma'aikatan Hukumar Wayar Da Kai ta Ƙasa (NOA) daga cikin jerin 'ya'yanta tare da aiki da ita. Batun na zuwa ne daga shugaban NUJ na Ƙasa, Mr Chris Isuzugo, a yayin taron wakilan ƙungiyar na ƙasa da aka gudanar a ranakun Laraba da Alhamis a Jihar Kano cikin makon nan. Taron wakilan na musamman ya gudana ne a ɗakin taro na The Afficent Event Center da ke Nasarawa GRA a Ƙaramar Hukumar Nasarawa a cikin Birnin Kano. Hakan ya biyo bayan amincewar wakilan ƙungiyar a taron, yayin…
Read More
CBN ya wayar da kan masu ta’ammali da POS a Zamfara

CBN ya wayar da kan masu ta’ammali da POS a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Babban Bankin Najeriya CBN ya gudanar da taron wayar da kan jama’a na kwana ɗaya ga ƙungiyoyin dake harkokin kasuwancin POS reshen jihar Zamfara kan mahimmancin shirin eNaira da canjin kuɗaɗen da ake ciki. Taron wanda ya gudana a ɗakin taro na Maryam da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara ranar Alhamis wanda ƙungiyar masu gudanar da POS reshen jihar Zamfara suka shirya a hukumance. A nasa jawabin, Shugaban Babban Bankin na CBN reshen Gusau, Malam Buhari Abbas, ya ce ɗaya daga cikin dalilan bullo da tsarin eNaira da kuma sauya fasalin wasu kudaden Najeriya…
Read More
Jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ya gamu da cikas

Jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ya gamu da cikas

Daga WAKILINMU Jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ya yi hatsari a yankin Kubwa da ke Abuja. Lamarin ya faru ne ranar Juma’a a lokacin da jirgin ya kusa kaiwa tashar da zai tsaya a Abuja. Bayanai sun nuna ƙafafun kan jirgin ne suka goce daga kan layi lamarin da ya haifar da jirkicewar kan jirgin gefe guda. Sai dai babu wani cikakken bayani da ke nuna an jikkata a hatsarin. Babban Daraktan Jukumar Sufurin Jirgin Ƙasa (NRC), Injiniya Fidet Okhiria ya tabbatar da aukuwar lamarin. Tare da cewa suna kan tattara bayanai kan abin da ya faru. Wannan al'amari na…
Read More
Boko Haram ta kashe mayaƙanta sama da 300 da suka yi niyyar miƙa wuya a Borno

Boko Haram ta kashe mayaƙanta sama da 300 da suka yi niyyar miƙa wuya a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu kwamandojin Boko Haram/ISWAP da ba su tuba ba sun kashe dakarunsu sama da 300 da iyalansu da ke fitowa daga dajin Sambisa da nufin miƙa wuya a Jihar Borno. Kwamandojin dai sun katse hanzarin mayaƙan ne da nufin kawo cikas kan ƙoƙarin tattaunawar da suke yi da gwamnatin jihar. Mai ba gwamnan Jihar Borno shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Ishaq Abdullahi (mai ritaya), ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Maiduguri ranar Alhamis. A cewarsa, sama da mayaƙan Boko Haram 90,000 da iyalansu ne ya zuwa yanzu suka…
Read More
INEC za ta yi haɗaka da ƙungiyoyin sufuri kan zirga-zirga ranar zaɓe

INEC za ta yi haɗaka da ƙungiyoyin sufuri kan zirga-zirga ranar zaɓe

Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da lokacin babban zaɓe yake ƙara ƙaratowa, Hukumar Zaɓe Mai zaman kanta (INEC) ta haɗa gwiwa da direbobi, mamallakan motocin haya, da sauran ma'aikatan tashar mota a jihar Oyo domin a samo hanyar da za a tafiyar da hada-hadar sufurin mutane da kaya a ranar zaɓe mai zuwa.  Wannan shi ne dalilin da ya sanya hukumar ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki don tattaunawa a kan haka.  Dakta Adeniran Tella, Bature Zaven na jihar Oyo (REC) da kuma INEC, su suka sanar da haka ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron…
Read More
Kwamishinan ‘Yan Sandan Kebbi ya ɗabbaƙa gasar Alƙur’ani tsakanin jami’an ‘yan sanda

Kwamishinan ‘Yan Sandan Kebbi ya ɗabbaƙa gasar Alƙur’ani tsakanin jami’an ‘yan sanda

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kebbi ya ɗabbaƙa gasar Alƙur'ani tsakanin jami'an 'yan sanda a jihar, inda mahalarta gasar karatun Alƙur'ani goma sha takwas ne daga sassa daba -daban na rundunar 'yan sandan jihar Kebbi suka shiga gasar karatun Alƙur'ani da kwamishinan 'yan sandan jihar Kebbi Alhaji Magaji Kontagora ya ɗabbaƙa. Da ya ke jawabi yayin buɗe gasar karatun, Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Kebbi ya ce dalilin shirya wannan gasar tare da ɗaukar nauyin ta shi ne akwai buƙatar 'yan sanda su ƙara samun kusanci da mahaliccinsu domin samun tsira ranar lahira. Haka zalika akwai…
Read More
Na san yadda za a daina yunwa Afrika – Buhari

Na san yadda za a daina yunwa Afrika – Buhari

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi iƙirarin cewa, ya san hanyoyin da za a bi wajen daina ƙarancin abinci a Nahiyar Afrika, har ma a riƙa fita da shi zuwa lasashen duniya, ya na mai kira ga shugabannin ƙasasshen Afrika da su himmatu wajen bunƙasa harkokin noma da kiwo a nahiyar. Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a Jawabin Fatan Alheri da ya gabatar a Taron Ƙara Wa Juna Sani na Shugabannin Gwamnatocin Afrika da aka gudanar shekaranjiya Laraba a Dakar, Babban Birnin Ƙasar Senegal, yana mai yabawa da ƙwazon bankunan Bankin Cigaba na…
Read More
An yi wa Buhari bore a Katsina

An yi wa Buhari bore a Katsina

*Matasa sun yi ƙone-ƙone kan babbar hanyar da Shugaban Ƙasa ya buɗe Daga UMAR GARBA a Katsina Wasu matasa da ake kyautata zaton ’yan bangar siyasa ne, sun yi zanga-zanga tare da ƙona tayoyi akan hanyar Yahaya Madaki dake birnin Katsina, Babban Birnin Jihar Katsina a jiya Alhamis. Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya buɗe wasu tagwayen hanyoyin gadar ƙasa a yayin ziyarar aiki da ya kai jihar tasa ta haihuwa. Matasan, waɗanda suka hau kan hanyar, sun yi ta ihu tare da faɗin “ba ma yi! Ba ma yin jam'iyyar APC!” kamar yadda…
Read More
Fasalin Naira: ‘Yan siyasa da bankuna suka haddasa ruɗani, inji ‘yan kasuwa a Kebbi

Fasalin Naira: ‘Yan siyasa da bankuna suka haddasa ruɗani, inji ‘yan kasuwa a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Watanni uku da Gwamnatin Tarayayr Nijeriya ko kuma Babban Bankin Ƙasa ya bayar a matsayin lokacin ƙarshen wa'adin amfani da tsofaffin takardun kuɗi na Naira 200 da 500 da kuma Naira 1000 da aka canja wa launi zai cika ranar Talata mai zuwa, wacce ta yi daidai da 31 ga watan Janairun wannan shekarar ta 2023 ya haifar da ruɗani a wajen al'umma musamman masu ƙaramin ƙarfi wanda yanzu haka ya sanya waɗansu 'yan kasuwa rufe shaguna da kuma daina waɗansu sana'o'i saboda kaucewa makarowa da kuɗaɗen a hannu zuwa ranar ƙarshe. Waɗansu 'yan kasuwa…
Read More
2023: Sauya fasalin Naira da ƙarancin fetur ba za su hana nasarata ba – Tinubu

2023: Sauya fasalin Naira da ƙarancin fetur ba za su hana nasarata ba – Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi zargin matsalar ƙarancin man fetur da ake fuskanta da sauya fasalin wasu takardun Naira da aka yi, take-taken neman wargaza zaɓen 2023 ne kawai. Tinubu ya bayyana haka ne yayin gangamin yaqin neman zaɓen APC da ya gudana ranar Laraba a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun. “Ba sa son zaɓen ya gudana. So suke su wargaza shi. Za ku bari hakan ta faru?” inji Tinubu. Ɗan takarar ya ce, yana da yaƙinin matsalar ƙarancin fetur ba za ta hana ’yan Nijeriya zuwa kaxa…
Read More