Editor

9513 Posts
Gwamna Tambuwal ya yaba wa Shugaba Buhari bisa kawo ƙarshen matsalar tsaro

Gwamna Tambuwal ya yaba wa Shugaba Buhari bisa kawo ƙarshen matsalar tsaro

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yaba wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bisa ƙoƙarinsa na haɗa guiwa da jihohin ƙasar nan domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan. Gwamna Tambuwal, wanda shine shugaban dandalin gwamnonin ƙasar nan, haka ma ya jinjina wa rundunar sojin ƙasar nan, bisa haɗa guiwa da gwamnonin jihohin ƙasar nan domin yaƙi da wannan matsalar. Tambuwal ya bayyana hakan ne dai lokacin da ya karvi baƙuncin manyan jami’an soji mahalarta kwas na 45 na kwalejin soji dake Jaji Kaduna suka kai masa ziyarar godiya na zaɓar Sakkwato domin gabatar da lamuransu.…
Read More
Ganduje ya buƙaci Buhari ya ɗage ziyarar Kano saboda matsin da canjin kuɗi ya haifar

Ganduje ya buƙaci Buhari ya ɗage ziyarar Kano saboda matsin da canjin kuɗi ya haifar

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar cewa ya aike wa Fadar Shugaban wasiƙar neman ɗage ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya kaiwa jihar. Ganduje ya ce ya yi hakan ne saboda matsin da jihar ta faɗa sakamako wa’adin daina amfani da tsoffin takardun Naira da CBN ya ƙayyade. Ya ƙara da cewa, batu tsaro ma na daga cikin dalilan da suka sanya ya buqaci ɗage ziyarar ta Buhari zuwa jihar. Gunduje ya bayyana haka ne a lokacin tattaunawarsu tare da malamai da ‘yan majalisa da shugabannin siyasa da kuma ’yan kasuwar jihar a Fadar Gwamnatin…
Read More
INEC ta ƙara wa’adin karɓar Katin Zaɓe

INEC ta ƙara wa’adin karɓar Katin Zaɓe

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tsawaita wa'adin karɓar Katin Zaɓe a faɗin ƙasar. Bayanin ƙarin wa'adin na ƙunshe ne cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na hukumar, Festus Okoye, ya fitar ranar Asabar. A cewar Okoye yanzu za a ci gaba da karɓar Katin Zaɓen daga 29 ga Janairu zuwa 5 ga Fabrairu, 2023. “Hukumar ta yi zama a rana Asabar, kwana ɗaya bayan tattaunawar da ta yi da kwamishinoninta na jihohi 36 haɗi da Abuja inda aka tattauna wasu muhimman batutuwa dangane da shirin karɓar Katin Zaɓen da ke gudana a ofisoshin hukumar a tsakanin…
Read More
Farashin litar fetur ta zama ‘kasuwa ta yi halinta’!

Farashin litar fetur ta zama ‘kasuwa ta yi halinta’!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Gaskiya yanzu ba wanda zai ce ga tsayeyyen farashin litar man fetur a gidajen man fetur a Nijeriya kawai ya danganta ga inda mutum ya ke da zama wato a cikin birane ne ko a manyan hanyoyin da ke tsakanin jihohi. Duk wata tsadar da a ka ambatawa mai ban tsoro ta tabbata. Dama can ai a na maganar in an janye dukkan tallafi litar fetur za ta haura Naira 300. Yanzu wannan ba sabon labari ba ne a wajen masu sayan man. Wato lamarin nan ya zama gidan kowa na hulɗa da fetur kai tsaye…
Read More
Gargaɗi akan zaɓen 2023

Gargaɗi akan zaɓen 2023

A daidai lokacin da ake tunkarar babban zaɓen ƙasar na 2023, Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), Tarayyar Turai (EU) da Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) sun yi gargaɗi game da tashe-tashen hankula a lokacin zaɓe da sauran laifuffuka da ka iya kawo cikas ga gudanar da zaɓen. Ƙungiyoyin sun yi magana kan illolin tashe-tashen hankula a lokacin zaɓen da kuma yin gargaɗin cewa illar na iya yin muni ga yankin da ma nahiyar Afirka bakiɗaya. Sun kuma jaddada cewa idan aka samu tarzoma a yayin zaɓen, babu wata ƙasa a yammacin Afirka da za ta iya shawo kan…
Read More
Nasarawa 2023: Kada ku bari a ruɗe ku da siyasar addini – Yakubu Maidoya

Nasarawa 2023: Kada ku bari a ruɗe ku da siyasar addini – Yakubu Maidoya

Daga JOHN D. WADA, Lafia A ci gaba da ziyartar lungu-lungu da sako-sakon Jihar Nasarawa da ɗan takarar Jam’iyyar NNPP na kujerar gwamnan jihar, alhaji Abdullahi Yakubu Maidoya, ke yi a yanzu don gudanar da kamfen ɗinsa, ɗan takarar ya yi kira musamman ga mabiya addinai daban-daban, musamman Musulmi da Kiristoci cewa kada su bari wasu gurɓatattun ‘yan siyasa waɗanda ke son kansu kaɗai marasa kishin ƙasa suna ruɗin su da batun addini don cimma mummunar burinsu a wannan lokacin zaɓe. Honorabu Abdullahi Yakubu Maidoya ya yi wannan kira ne a jawabinsa a lokacin da ya gana da wasu shugabannin…
Read More
Messi na take-taken komawa Barcelona – Rahoto

Messi na take-taken komawa Barcelona – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu na ganin cewa Lionel Messi zai tsawaita kwantiraginsa da ƙungiyar PSG, amma kuma wasu rahotanni na nuna cewa ɗan wasan na Argentina na shirin komawa tsohuwar ƙungiyarsa ta Barcelona. A cewar wani marubucin labarin wasanni na ƙasar Spain Gerard Romero, akwai shakku game da batun tsawaita zaman Messi a PSG. Ya ce, nasarar da ɗan wasan ya samu ta lashe kofin duniya, ta sauya masa tunani musamman yadda yanzu ya daina fifita lamuran wasa akan wasu abubuwa. A ’yan makwannin da suka gabata ne dai aka fara saran ɗan wasan mai shekaru 35 zai cimma…
Read More
‘Yan bindiga sun fille kan shugaban ƙaramar hukuma a Imo

‘Yan bindiga sun fille kan shugaban ƙaramar hukuma a Imo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu 'yan bindiga a Jihar Imo da ke Kudu maso gabashin Nijeriya sun sare kan wani shugaban ƙaramar hukumar Ideato ta Arewa a jihar, bayan da suka sace shi a ranar Juma'ar da ta gabata. 'Yan bindigar dai sun saki wasu hotunan bidiyo da ke nuna yadda suka ɗaure shugaban qaramar hukumar a hannaye, da kuma yadda suka halaka shi, bayan sun karvi kuɗin fansa don su sako shi. Wata majiya a rundunar 'yan sandan Nijeriya ta jihar Imo, ta tabbatar wa BBC labarin kisan gillar da 'yan bindigar suka yi wa shugaban riƙo…
Read More
Mun ɗaura ɗamarar kawo sauyi ga ‘yan kasuwa a Kano – Alkamatu

Mun ɗaura ɗamarar kawo sauyi ga ‘yan kasuwa a Kano – Alkamatu

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano Shugaban Kamfanin Alkamatu Brain Box Solution, wato matashin nan mai rajin ganin matasa da sauran al'umma sun samu damar tsayawa da ƙafafunsu, Kwamared Alkamatu Hussain Abdulkadir ya ce shirinsu ya kankama na ganin a taimaka wajen kanikancin kasuwancisu. Alkamatu ya ce lallai babu abinda ke gabansu yanzu haka da ya wuce ganin yankin Arewa ya ci gaba wajen harkokin kasuwanci da sauran hanyoyin dogaro da kai. Matashin da yake taka rawar gani wajen taimakon jama'a a Jihar Kano dama makwabtan jihohin Kano ya tabbatar da cewa sanin kowa ne kamar yadda ɗan Adam da…
Read More
Tsohon gwamnan Adamawa, Bindow ya fice daga APC

Tsohon gwamnan Adamawa, Bindow ya fice daga APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan Jihar Adamawa, Sanata Muhammad Umar Jibrilla Bindow, ya fice daga Jam’iyyar APC. Bindow ya fice daga jam’iyyar ne a hukumance ta wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban Jam’iyyar APC na gundumar Kolere, ƙaramar hukumar Mubi ta Arewa a Jihar Adamawa, mai kwanan wata 20 ga watan Janairu, 2023, wacce Manhaja ta samu kofi a ranar Talata. Bindow, wanda bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba, ya ƙara da cewa "magoya bayansa masu aminci’ a faɗin jihar za su bi shi wajen ficewa daga Jam’iyyar APC ta yadda za su jajirce wajen…
Read More