Gargaɗi akan zaɓen 2023

A daidai lokacin da ake tunkarar babban zaɓen ƙasar na 2023, Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), Tarayyar Turai (EU) da Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) sun yi gargaɗi game da tashe-tashen hankula a lokacin zaɓe da sauran laifuffuka da ka iya kawo cikas ga gudanar da zaɓen.

Ƙungiyoyin sun yi magana kan illolin tashe-tashen hankula a lokacin zaɓen da kuma yin gargaɗin cewa illar na iya yin muni ga yankin da ma nahiyar Afirka bakiɗaya. Sun kuma jaddada cewa idan aka samu tarzoma a yayin zaɓen, babu wata ƙasa a yammacin Afirka da za ta iya shawo kan matsalar ’yan gudun hijira.

Idan har ba a hanzarta magance ƙalubalen tsaro na ƙasar ba, EU ta ce hakan na iya yin barazana ga zaɓen 2023. Jagoran tawagar EU na tallafawa mulkin dumokuraɗiyya a Nijeriya, kashi na biyu, Rudolf Elbling, ya ba da shawarar cewa ya kamata a yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa babu abin da zai kawo cikas ga zaɓen.

Tun da farko a birnin Jos na Jihar Filato, Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyar ECOWAS suka yi wani horon shiga tsakani da tattaunawa tare da kwamitin ba da shawara na jam’iyyu (IPAC) da sauran masu ruwa da tsaki, inda suka buƙaci Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zaɓe kuma cikin lumana.

Sa’adatu Sha’abu, wacce ta wakilci ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da yammacin Afirka da Sahel (UNOWAS), ta buƙaci ‘yan siyasa da magoya bayansu da su tafiyar da lamuran kamar yadda doka ta tanada.

Bai kamata a yi watsi da damuwar ƙungiyoyin ba kan babban zave mai zuwa. Yakamata Gwamnatin Tarayya ta gaggauta magance su kafin babban zaɓen 2023.

Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a Cibiyar Kula da Harkokin Ƙasa da Ƙasa (Chatham House) da ke Landan, ya bayyana muhimmancin zave ga Nijeriya da Afirka. Ya kuma yi amfani da wannan damar wajen tabbatar wa al’ummar duniya cewa alƙalan zaɓen za su gudanar da sahihin zaɓe da gaskiya.

A cewar Yakubu, bisa alƙaluman da aka tattara daga hukumomin zaɓe da ma’aikatun cikin gida a wasu jihohi 14 na yammacin Afirka, yawan masu kaɗa ƙuri’a a Nijeriya a halin yanzu ya kai miliyan 93.4, fiye da miliyan 76.7 da aka yi wa rajista a duk sauran ƙasashen duniya.

Hakan na nufin samun babban zaɓe a Nojeriya tamkar gudanar da zaɓe ne a faɗin Afirka ta Yamma da ma sauran ƙasashen duniya. Wannan, a cewarsa, dole Nijeriya ta yi daidai don kauce wa sakamako mara kyau.

Don haka ya dace Gwamnatin Tarayya da INEC da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen gudanar da zaɓen su gudanar da zaɓe mafi inganci da ba a taɓa yi a tarihin ƙasar nan ba.

Don haka dole ne dukkan hannaye su kasance a wuri ɗaya don tabbatar da ingantaccen zave. Zaɓen 2023 na da matuqar muhimmanci ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya, musamman masu zave. Yunƙurin da ‘yan Nijeriya ke nunawa ya zuwa yanzu wajen tattara katunan zaɓe na dindindin na nuni da hakan.

Muna kira ga INEC da ta tabbatar da cewa sakamakon zaɓen ya nuna muradin ɗaukacin ’yan Nijeriya. Ya kamata a ƙirga ƙuri’unsu. Hanya mafi kyau na tabbatar da cewa ba a samu tashin hankali a lolacin zaɓe ba ita ce gudanar da sahihin zaɓe.

Sai dai hare-haren da ake kai wa ofisoshin INEC da wasu sassa na ƙasar na haifar da fargaba. Alƙaluman da aka samu sun nuna cewa tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022, Hukumar ta fuskanci hare-hare 50 a cibiyoyinta. A wasu hare-haren dai jami’an INEC sun jikkata ko kuma an kashe su. Na baya-bayan nan dai shi ne harin da aka kai ofishin INEC a jihar Enugu inda aka kashe wani ɗan sanda.

Samun sahihin zaɓe nauyi ne na gamayya na gwamnati, INEC, hukumomin tsaro, jam’iyyun siyasa da magoya bayansu. A bar gwamnati ta samar da yanayi mai kyau ga masu zaɓe su je su kaɗa ƙuri’a ba tare da fargaba ba.

A samar da isasshen tsaro a lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓen. Rundunar ’yan sandan Nijeriya da sauran jami’an tsaro da ke gudanar da atisayen na buƙatar a samar masu da isassun kayan aiki.

Yana da kyau shugaban hukumar zaɓe ta INEC ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya a shirye hukumar take ta shirya sahihin zaɓe na gaskiya. ’Yan Nijeriya ba sa tsammanin wani abu akasin haka.

Cimma wannan buri zai kasance daidai da alƙawarin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi na gudanar da zaɓe na gaskiya a ƙasar. Dole ne hukumar zaɓe ta tabbatar da tura isassun na’urar ‘Bimodal Voter Accreditation System’ (BVAS), da sauran na’urorin fasaha don gudanar da zaɓe a dukkan rumfunan zave a ƙasar.