Farashin litar fetur ta zama ‘kasuwa ta yi halinta’!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Gaskiya yanzu ba wanda zai ce ga tsayeyyen farashin litar man fetur a gidajen man fetur a Nijeriya kawai ya danganta ga inda mutum ya ke da zama wato a cikin birane ne ko a manyan hanyoyin da ke tsakanin jihohi.

Duk wata tsadar da a ka ambatawa mai ban tsoro ta tabbata. Dama can ai a na maganar in an janye dukkan tallafi litar fetur za ta haura Naira 300. Yanzu wannan ba sabon labari ba ne a wajen masu sayan man. Wato lamarin nan ya zama gidan kowa na hulɗa da fetur kai tsaye ko a kaikaice don muhimmancin man wajen lamuran sufuri.

Don haka da zarar an samu ƙaruwar farashin man fetur to za a gani daga ƙarin farashin muhimman kayana masarufi. Tun hawan gwamnatin shugaba Buhari a 2015 a ka samu ƙarin da ya fi na kowane lokaci a tarihi wato daga Naira 87 zuwa Naira 145.

A lokacin akasarin ’yan Nijeriya miusamman na Arewa ba su tada jijiyar wuya ba don su na tunanin gwamnatin na neman kuɗin fara gyara ƙasa ne kuma sun amince da ita cewa za ta kawo sauye-sauye da talakawa za su samu cin moriyar mulkin dimokuraɗiyya.

A lokacin mutane ma kai tsaye kan ce Allah ya ba su kuɗin sayen man don sun amince da adalcin gwamnatin. Kusan a karo na farko jama’ar ƙasa su ka bijirewa zanga-zanga da yajin aiki da qungiyar ƙwadago ta buƙaci a yi don sassauto da farashin litar.

Don haka ba a rage ko sisin kobo ba daga vangaren gwamnati. Marigayi ma’ajin ƙungiyar qƙwadago, Komred Ibrahim Khalil ya ce tarihi zai tuna irin manufar ƙungiyar ƙwadagon na nuna cijewa don a samu ragin farashin. Khalil na magana ne lokacin da ƙungiyar ala tilas don rashin samun goyon baya ta yi taro ta janye yajin aiki ba tare da cimma muradi ba.

Tun daga wannan shekarar an cigaba da samun tashin farashin fetur kuma ba wata alama ta ranar da hakan zai zama sauƙi ga ‘yan ƙasa. Hasalima gwamnatin ta nuna ba yadda za a iya kaucewa yanayin sai dai a yi ƙoƙarin rage tsadar ko bi a hankali.

Shugaba Buhari a shekarun da ya yi ta adawa daga 2003 ya nuna bai amince da sahihancin ba da tallafin man fetur ba. Don haka ya aiyana cire tallafin da hakan ya cilla litar zuwa wannan matsayi da ya gagari talaka.

Har an dauka shikenana ba za a sake jin batun wani tallafi ba sai kuma kwatsam batun ya dawo daga bayanan ma’aikatar kuɗi ta hannun ministar kuɗi Zainab Shamsuna Ahmed. Nan fa a ka gano ashe gwamnatin ba ta daina tura tallafin shigo da fetur ba. Kuma abun fargabar dama in an cire tallafin litar za ta kai ga matakin da man sai wane da wane ne kaɗai za sui ya saya.

Ba a kuma samun bayanai filla-filla daga gwamnati na batun tallafin don ba mamaki ko an buɗawa mutane sun fahimci bayanin ba za su gamsu ba tun da ita kan ta gwamnatin ta shigo da ra’ayin cewa tallafin wata hanya ce ta almundahana daga wasu mutane ƙalilan. Rufe batun da ba da tallafin a gwamnatance ya sa in an zo batun ƙara farashi mutane kan nuna damuwa.

Amma in an sake nazartar lamarin damuwar mutanen ta kan zama ta fatar baki ce don kamar sun ma saba da tsadar ko kuma a ce sun miƙa wuya ga ko ma yaya ta kasance shikenan ba sa mamakin sauye-sauye marar sa armashi da ke faruwa. Dole ’yan ƙasa su ka sake bararar rayuwa da yin abubuwan da su ka zama wajibi kaɗai don akasarin kuɗi na tafiya ne kan abinci, makamashi da sufuri. In za asamu miya ba nama sai a ci kawai don ai ba dole sai da manja za a sha miya ba.

Akwai lokacin da na yi wani hasashe duk da ni ba masanin tattalin arziki ba ne cewa a ’yan shekarun baya in an kwatanta darajar Naira 5000 za a taras yanzu ita ce Naira 50,000. Mutane ƙalilan ne su ka kowa ra’ayi ko matsaya da ta ɗan gaza wannan amma waɗanda su ka amince ko ma nuna darajar ta fi haka sun fi yawa.

Kowa zai iya kwatatntawa ya duba kuɗin da ya ke kashewa a shekaru 10 da su ka wuce da yanzu zai fahimci abun da na ke nufi na yanda kuɗi ƙalilan ba sa iya biyan ko da ƙaramar buƙatar gida ta yau da kullum. Wannan sauyi ya ta’azzara ne daga tashin farashin litar mai da kuma tsadar canjin dala. Waɗannan dalilan guda biyu na kan gaba wajen zama ma’aunin tsada a tsakanin talakawa a Nijeriya.

Ba buƙatar sai an faɗawa mutum hakan don fetur da dala kai tsaye su ka shafi kusan dukkan lamuran rayuwar jama’a. Abun takaicin kawai yadda wasu da ba su da sassauci ga ‘yan uwansu kan ƙara farashin kayan da ba ma odar su a ke yi daga ƙetare ba da fakewa da tashin farashin dala.

Ba zan yi mamaki ba in ɗanyen kayan abinci da a ke nomawa a cikin gida ya yi tsada saboda tashin farashin fetur ko dala don za a duba ai takin zamani da manoma ke amfani da shi ya yi tsada ta fitar hankali hakanan wajen sufurin kayan ma an samu ƙari don tashin farashin fetur.

Alamu na nuna litar man fetur daga makon da jiya ta kama hanyar zama mai farashin ɗan karen tsada a sassa daban-daban na Nijeriya.

Baya ga samun dogayen layuka a gidajen man da kan sayar da rahusa, a wasu biranen an koma dogara ga samun man daga wajen ‘yan baƙar kasuwa. Za ka ga gidan mai ga man amma ba layi to amma farashin lita ba ta da bambanci da kusan na masu sayarwa a jarka a gefen titi. Sauyin kawai shi ne wannan na amfani da na’ura wannan na zubawa da hannu.

Litar man fetur ta bambanta inda a wasu gidajen mai a ka ga ta kai Naira 290-300 har ma fiye da hakan tamkar an bar man kasuwa ta yi halin ta kenan kamar yanda bayanai su ka gabata.

In za a tuna ƙaramin ministan fetur Timipre Sylva ya musanta duk wasu labaru da ke nuna gwamnati ta ƙara farashin man a asirce. Haƙiƙa tsadar farashin kai tsaye na nuna mutane sai su yi sabon shirin tinkarar kayan masarufi za su ƙara tsada ne a kasuwanni.

Bayanin da a ke yi yanzu daga fahimtar masana shi ne gwamnati ba za ta ƙara farashin sai bayan ta sauka wato a watan yuni mai zuwa kenan don ƙarshen wa’adi na zuwa a ranar 29 ga watan mayu ne. Tun wani batun sauyi ko tsari na tattalin arziki ya dogara ne ga sabuwar gwamnati da za ta zo bisa sakamakon da a ke sa ran samu a babban zaɓen da za a gudanar a ranar 25 ga watan gobe.

A fili dai koyaushe a na batun ƙarin farashi ne ba raguwa ba. In a na tattaunawa kan hakan za ka iya jin jami’an gwamnati na nuna farashin man fetur na Nijeriya na daga mafi araha a duniya. Abun da ba sa ƙarisawa shi ne in an kwatanta farashin da kamar na Saudiyya shin rayuwar yau da kullum ta ɗan Nijeriya da Saudiyya akwai bambanci?

Tsadar fetur ta kan ƙara tsadar kayan masarufi a ƙasashen da a ke magana? Yaya farashin burodi, magani a asibiti, tsaro, haya da sauran su. Nawa ne albashin ma’aikata? Ya zama mai muhimmanci sharhin ya yi faɗi zuwa tasirin farashin kan sauran abubuwan da jama’a ke buƙata.

Kuma ya na da kyau gwamnati ta riqa fitowa ƙarara ta na fadar yadda tallafin fetur ke tafiya da irin bambancin tallafin a ƙarƙashin gwamnatin PDP da kuma yanzu a APC. Za a gane yadda lamarin ya ke. Sannan me shugaba Buhari zai ce game da fahimtar sa ta da a kan tallafin fetur da kuma lokacin da ya haye karagar madafun ikon fadar Aso Rock.

Kammalawa;

Labaru masu daɗi na shigowar ’yan kasuwa wajen kafa matatar man fetur na da muhimmanci don ko ma dai yaya za a ce in a na tace ɗanyen man fetur a cikin gida za a huta daga dan karen tsadar da a ke samu daga shigo da man daga ƙetare. Ba mamaki shigowar ‘yan kasuwar ya zaburar da gwamnati ma ta farfaɗo da matatun ta don samun da wani kason man.

In an dace batun man fetur a Arewa ya ƙara bunƙasa ga sabbin matatun fetur, za a iya samun sauƙin rayuwa. Don baya ga man fetur na rijiyoyin Kolmani a Bauchi da Gombe ga kuma batun fara tono man a jihar Nasarawa. Alamu na nuna za a iya cigaba da samun sassan arewacin Nijeriya da ke da man.

Fatar da a ke da ita wannan batun man na arewa ya ƙara bunƙasa a ƙarƙashin gwamnati mai zuwa don hakan ya zama sabon buɗin arziki a yankin da ke da masu fama da ƙuncin tattalin arziki inda akasarin jama’a ke zama hannu baka hannu kwarya.