INEC ta ƙara wa’adin karɓar Katin Zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tsawaita wa’adin karɓar Katin Zaɓe a faɗin ƙasar.

Bayanin ƙarin wa’adin na ƙunshe ne cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na hukumar, Festus Okoye, ya fitar ranar Asabar.

A cewar Okoye yanzu za a ci gaba da karɓar Katin Zaɓen daga 29 ga Janairu zuwa 5 ga Fabrairu, 2023.

“Hukumar ta yi zama a rana Asabar, kwana ɗaya bayan tattaunawar da ta yi da kwamishinoninta na jihohi 36 haɗi da Abuja inda aka tattauna wasu muhimman batutuwa dangane da shirin karɓar Katin Zaɓen da ke gudana a ofisoshin hukumar a tsakanin ƙananan hukumomi 774 a faɗin ƙasar,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa yayin zaman ne Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ba za ta ɓata lokaci ba wajen ɗaukar duk wani mataki da zai taimaka wajen tabbatar da ‘yan ƙasa kowa ya karɓi katin zaɓensa don amfanin zaɓe mai zuwa.