Editor

9513 Posts
Harin masallaci ya yi ajalin mutum 61 a Pakistan

Harin masallaci ya yi ajalin mutum 61 a Pakistan

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Pakistan sun tabbatar da aukuwar wani mummunan harin da aka kai masallaci wanda ya yi ajalin mutum 61. Waɗanda suka mutu a harin na ranar Litinin har da jami'an tsaro, kana mutum 150 sun jikkata. An kai harin ne a daidai lokacin jama'a suka haɗu domin gudanar da sallar Azahar a madallacin da ke hedikwatar 'yan sandan Pakistan da ke birnin Peshawar. Ana ci gaba da aikin ba fa agaji a inda iftila'in ya auku, wanda ginin masallacin ya tarwatse saboda ƙarfin fashewar da ta auku. Shugaba Rundunar 'Yan Sandan Peshawar, Mohammed Ijaz Khan…
Read More
Ko Kanawa sun yi lale da ziyarar Buhari?

Ko Kanawa sun yi lale da ziyarar Buhari?

Daga BASHIR ISAH A ranar Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyar aiki na kwana biyu a Jihar Kano domin ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Jihar ya aiwatar. Sai dai, da alama Kanawa ba su yi ɗaukin ziyarar Buharin ba saɓanin abin da aka saba gani a baya. Kafin ziyarar tasa, an abato Gwamnan Jihar, Abdullahi Ganduje, ya ce, ya nemi Shugaba Buhari ya ɗage ziyarar da ya shirya yi a Kano sakamakon jama'a na cikin mawuyacin hali saboda canjin kuɗi da aka yi. Rahotani, hotuna da ma bidiyoyi sun nuna yadda a wasu titunan jihar galibi yara kaɗai…
Read More
Tilas ce ta sa na fito takarar Gwamnan Sakkwato – Dakta Sifawa

Tilas ce ta sa na fito takarar Gwamnan Sakkwato – Dakta Sifawa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Yayin da manyan zaɓukan 2023 musamman ma zaɓen gwamnoni ke daɗa ƙaratowa, wani abu da ya soma ɗaukar sabon salo a siyasar Nijeriya shi ne, fitowar jama'a takarar gwamnoni a ƙananan jam'iyyun siyasa duk wasu na masu kallon 'yan amshin shata ne kawai ta la'akari da cewa, ba su fiye yin tasiri ba  a siyasar Nijeriya wajen kafa gwamnati. Wakilin Blueprint Manhaja a Sakkwato, Aminu Alhussaini Amanawa ya zanta da ɗan takarar gwamna na jami'ar ADP, Dakta Ibrahim Mahammad Liman Sifawa, wanda ya ce tilas ce ta sa shi fitowa takarar domin canza abinda ya…
Read More
Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya dawo aiki

Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya dawo aiki

Daga WAKILINMU Daraktan ayyuka na Hukumar Jiragen Ƙasa ta Ƙasa (NRC), Niyi Alli ne ya sanar da hakan ranar Litinin. Sanarwar da ya fitar ta nuna tsarin lokutan da jirgin zai riƙa zirga-zirgar jagilar fansinjoji. Sanarwar ta ce, “Ranar Talata, 31 ga Janairun 2023 jirgin zai kama aiki bisa tsari kamar haka: KA2 zai bar Rigasa da ƙarfe 0700 AK1 zai bar Idu da ƙarfe 10.00 KA4 zai bar Rigasa da ƙarfe 13.00 AK3 zai bar Idu da ƙarfe 16.00. “Sai dai a ranar Laraba, KA2 zai bar Rigasa da ƙarfe 0700 yayin da AK 3 zai bar Idu da…
Read More
Dandalin shawara: Mijina ba ya fashin kusanta ta lokacin da na ke jin al’ada

Dandalin shawara: Mijina ba ya fashin kusanta ta lokacin da na ke jin al’ada

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Assamu alaikum wa rahmatullahi. Hajiya Aisha ya ƙoƙari. Ya kuma fama da jama'a. Kwana da yawa. Fatan duk iyalai lafiya. Sunana…………daga nan………….. Mun ɗan yi magana da ke a shekarun baya, lokacin littafinki na 'Soyayyar Ƙarya', har ki ka ba ni shawarwari kan matsalata, kuma na ji daɗin su ainun, don sun fitar da ni matsalar. To yanzu ma wani abu ne ke ci min turo a ƙwarya. Wallahi mijina ne dai al'amarinsa ya fara damuna, matsala ce da ta kai kusan shekara yanzu, muna iya kwashe kusan sati uku zuwa huɗu bai damu da neman…
Read More
Har yanzu dai Nijeriya ita ce jagaba wajen samar da fetur a Afirka – OPEC

Har yanzu dai Nijeriya ita ce jagaba wajen samar da fetur a Afirka – OPEC

Daga AMINA YUSUF ALI Duk da qalubale da matsalolin da ta sha fuskanta, ya zuwa ƙarshen shekarar 2022, Nijeriya ta kasance ita ce kan gaba wajen samar da man fetur a Afirka. Wannan lafazin ya fito ne da yawun Ƙungiyar ƙasashen masu samar da man fetur a Duniya (OPEC). OPEC ta bayyana cewa, Nijeriya ta ƙarƙare shekarar 2022 a matsayin qasar da ta fi kowacce samar da man fetur a Nahiyar Afirka. A cewar OPEC, Nijeriya a watan Disamba na shekarar bara ta samu ƙarin kaso 4% na man fetur ɗin da take samarwa. Wato gwari-gwari ta tashi daga samar…
Read More
Tsoffin takardun Naira: Majalisa ba ta aminta da ƙarin wa’adin da CBN ya yi ba

Tsoffin takardun Naira: Majalisa ba ta aminta da ƙarin wa’adin da CBN ya yi ba

Daga WAKILINMU Majalisar Wakilai ta ce ba ta aminta da tsawaita wa’adin amfani da tsohuwar Naira da ƙarin kwanaki 10 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi ba. Kwamitin Majalisar mai ruwa da tsaki kan sha’anin sauya fasalin wasu takardun Naira, ya ce dole CBN ya yi abin da ya kamata kamar yadda yake ƙunshe a sassa na 20, 3, 4 da kuma 5 na Dokar Babban Bankin Ƙasar. A cewar Kwamitin, “Tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun Naira da kwana 10 ba shi ne mafita ba. “A matsayinmu na Kwamitin Majalisa ba za mu amince da wani abu sabanin…
Read More
Wane dalili ke sanya mata mantawa da Allah lokacin biki?

Wane dalili ke sanya mata mantawa da Allah lokacin biki?

A halin da ake cikin yanzu, kowa, musamman samari sun tabbatar da cewa galibin mata na shiga wani yanayi na mantawa da ibada lokacin shagulgulan biki, da har ta kan kai su manta yin salla tsawon wuni guda. An gano yadda galibin matan ke ƙin yin sallar saboda dalilan kwalliya, da yanayin hidimar bikin. Sauran dalilan su ne yanayin kayan da matan ke sawa masu kama da tsirara, sai kuma hayaniyar wurin biki, da kuma uwa uba rashin son kada abu ya wuce su ba a yi da su ba. Wasu na ganin cewa, kwalliya ita ce abu na farko…
Read More
Me ya sa ‘yan siyasa ke mantawa da mata idan sun samu gwamnati?

Me ya sa ‘yan siyasa ke mantawa da mata idan sun samu gwamnati?

Mata a Nijeriya sun koka da yadda ake mantawa da su bayan ’yan siyasa sun samu gwamnati duk da fitowar da suke ƙwansu da ƙwarƙwata wajen kaɗa ƙuri’a a yayin zaɓe. Wannan koke na matan na zuwa ne a daidai lokacin da ake daf da gudanar da zavukan ƙasar na 2023. Wannan matsala ta rashin damawa da mata a siyasa abu ne da ya daɗe yana ciwa wasu mata tuwo a ƙwarya ganin yadda suka ce ana watsi da su a lokacin da siyasa ta yi daɗi. Matan na cewa wataƙila hakan baya rasa nasaba da rashin ba su cikakkiyar…
Read More
CBN ya tswaita wa’adin daina karɓar tsoffin takardun Naira da kwana 10

CBN ya tswaita wa’adin daina karɓar tsoffin takardun Naira da kwana 10

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tsawaita wa'adin daina karbar tsoffin takardun Naira ya zuwa 10 ga Fabrairu, 2023. Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya ba da sanarwar ƙarin wa'adin a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi. Ya ce, sai da CBN ya nemi amincewar Shugaba Muhammadu Buhari kafin ɗaukar matakin tswaita wa'adin da kwana 10. “La'akari da halin da ake ciki, mun nemi yardar Shugaban Ƙasa kan waɗannan abubuwa: Sahalewar tswaita wa'adin da kwana 10 daga 31 ga Janairu zuwa 10 ga Fabrairu don ba ba da damar ci gaba da karɓar tsoffin takardun Naira daga hannun…
Read More