An yi wa Buhari bore a Katsina

*Matasa sun yi ƙone-ƙone kan babbar hanyar da Shugaban Ƙasa ya buɗe

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu matasa da ake kyautata zaton ’yan bangar siyasa ne, sun yi zanga-zanga tare da ƙona tayoyi akan hanyar Yahaya Madaki dake birnin Katsina, Babban Birnin Jihar Katsina a jiya Alhamis.

Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya buɗe wasu tagwayen hanyoyin gadar ƙasa a yayin ziyarar aiki da ya kai jihar tasa ta haihuwa.

Matasan, waɗanda suka hau kan hanyar, sun yi ta ihu tare da faɗin “ba ma yi! Ba ma yin jam’iyyar APC!” kamar yadda Wakilin Blueprint Manhaja a Katsina ya ruwaita.

Lamarin bai tsaya nan ba, sai da matasan suka riqa jifar taron mutanen da suka halarci buɗe gadar, inda daga bisani suka fasa allon ƙaddamar da gadar ma.

Abdul  Suleiman, wanda lamarin ya faru a gaban idonsa, ya bayyana wa majiyar Manhaja cewa, “Jim kaɗan bayan Shugaban Qasa ya buɗe gadar, wasu mazauna kusa da wajen sun fito suna jifar motocin baƙin da suka halarci taron. Kafin mu farga, sai muka ga sun fara ƙona tayoyi.”

Sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar kwantar da tarzomar bayan da suka harba barkono mai sa hawaye, don tarwatsa matasan.

A jiya Shugaba Buhari ya ziyarci Jihar Katsina ne a wata ziyarar aiki ta kwana biyu da yake yi, don buɗe wasu ayyuka da gwamnatin jihar mai ci ta Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta aiwatar a faɗin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *