Editor

9513 Posts
Jawabin Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin game da sanya hannun Amurka kan dokar bada izinin tsaro ta ƙasa ta shekarar 2023

Jawabin Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin game da sanya hannun Amurka kan dokar bada izinin tsaro ta ƙasa ta shekarar 2023

Daga CMG HAUSA Yau Asabar 24 ga wata, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya rattaba hannu kan dokar ba da izinin tsaron kasa ta shekarar kasafin kudi ta 2023, wacce ta kunshi ayoyi marasa kyau masu yawa da suka shafi kasar Sin. Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi suka da kakkausar murya, kan matakin Amurka na rattaba hannu kan "Dokar ba da izinin tsaron kasa ta shekarar kasafin kudi ta 2023", wadda ke kunshe da munanan abubuwan da suka shafi kasar Sin, kuma bangaren Sin din ya gabatar da…
Read More
Rundunar ‘Yan Sanda ta taya Kiristoci murnar Kirsimeti a Zamfara

Rundunar ‘Yan Sanda ta taya Kiristoci murnar Kirsimeti a Zamfara

Daga MUHAMMAD SANUSI a Gusau A ƙoƙarinta na ganin an gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara cikin lumana, Rundunar 'Yan Sandan Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin CP Kolo Yusuf, ta tabbatar wa al’umma cewa an samar da matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a kafin, lokacin da kuma bayan bukukuwan. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, SP Muhammad Shehu. Sanarwar ta ce, an girke jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da dama a majami'u da sauran wuraren shakatawa domin tabbatar da an gudanar da bukukuwan…
Read More
Pele zai shafe lokacin Kiristimati a asibiti

Pele zai shafe lokacin Kiristimati a asibiti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shahararren da ƙwallon ƙafar duniya, Pele zai shafe lokacin bukukuwan Kiristimati a asibiti, kamar yadda iyali da likitocinsa suka bayyana, sakamakon magani da ake masa na cutar daji da ke ƙara ƙamari, da kuma matsalar ƙoda da zuciya. Sanarwa daga asibin Albert Einstein na birnin Sao Paolo ta tabbatar da cewa Pele mai shekaru 82 na fama da matsalar zuciya da ƙoda, a yayin da ake mai maganin sankara, inda ta ƙara da cewa ba ya ɓangaren rai kwakwai, mutu kwakwai na asibitin. Pele wanda ake wa kallo a matsayin ɗan ƙwallon ƙafar da ba a…
Read More
‘Yan bindiga sun ƙone wata kotu a Imo

‘Yan bindiga sun ƙone wata kotu a Imo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mahara sun ƙone wata Kotun Majistare a Owerri, babban birnin Jihar Imo, ƙasa da sa’a 24 da aka kai makamancinsa a wata babbar kotun jihar da ke yankin Orlu. Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun kai harin ne ta hanyar amfani da ababen fashewa kuma sun ƙone takardu da wasu muhimman abubuwa ƙurmus a kotun. Wasu mazauna yankin da suka leqa don gane wa idonsu yadda lamarin ya faru sun bayyana cewa maharan sun lalata kusan ɗaukacin kotun. Kakakin ’yan sandan Jihar Imo, Mike Abattam, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce rundunar…
Read More
Yadda jami’an Hisbah su ka wargaza auren ‘yan luwaɗi a Kano

Yadda jami’an Hisbah su ka wargaza auren ‘yan luwaɗi a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, hukumar da ke tabbatar da ɗa’ar addinin Musulunci, ta kama wasu matasa 19 da suka halarci bikin auren jinsi. Kakakin hukumar, Lawan Ibrahim ya bayyana haka a ranar Talata a Kano cewa matasan sun hallara ne domin shaida ɗaurin auren wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan liwaɗi ne Abba da Mujahid. “An kama shi ne bayan da wani saurayi nagari ya tsegunta wa hukumar game da shirin auren jinsin. “Jami’an mu da ke hedikwatar hukumar Hisbah, Sharaɗa Kano, sun isa wurin kafin a fara ɗaurin auren. “A cikin…
Read More
Babban jami’in Max Air, Bashir Mangal ya kwanta dama

Babban jami’in Max Air, Bashir Mangal ya kwanta dama

Allah Ya yi wa Babban jami'in kamfanin jiragen sama na Max Air, Bashir Mangal, rauwa. Sanarwar rasuwar ta fito ne ta hannun jami'in tuntuba kan sha'anin yaɗa labarai na kamfanin, inda ta nuna marigayin ya rasu ne da safiyar Juma'a. Rahotanni sun nuna an yi jana'izar marigayin kamar yadda Musulunci ya tanadar a Katsina. Bashir Mangal ƙani ne ga Dahiru Barau Mangal, mu'assasin kamfanin jiragen sama na Max Air, wanda jiragensa ke zirga-zirga a gida da ƙetare.
Read More
Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya ta yaye ɗalibai 100 a Nasarawa

Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya ta yaye ɗalibai 100 a Nasarawa

Daga BASHIR ISAH A ranar Litinin ta makon jiya, Kwalejin Nazarin Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Jihar Nasarawa da ke Keffi, ta yi bikin yaye wasu ɗalibanta da suka kammala karatu a wasu sassa biyu, wato sashen nazarin lafiyar ido da na nazarin kimiyyar abinci, wato 'Dietetics Technician' a Turance. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban kwalejin, Alh Dokta Sulaiman Abdullahi, ya ce wannan shi ne karo na biyu da makarantar ke yaye ɗalibai a waɗannan sassa. Ya ce tarin nasarorin da kwalejin ta samu ya sa makarantar ta zamo ɗaya daga cikin makarantun nazarin kiwon lafiya ukun da ke…
Read More
Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da Sakataren Wajen Amurka

Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da Sakataren Wajen Amurka

Daga CMG HAUSA Yau Jumm’a 23 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken bisa bukatarsa. Wang Yi ya yi nuni da cewa, wajibi ne bangaren Amurka ya mai da hankali kan halastattun muradun kasar Sin, tare da daina neman hana ci gaban kasar Sin da mayar da ita saniyar ware. Yana mai jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su mayar da hankali wajen aiwatar da yarjejeniyar Bali da shugabannin kasashen biyu suka cimma zuwa manufofi masu dacewa da kuma ayyuka na zahiri. A nasa bangare kuwa,…
Read More
Haɗin gwiwar Afirka da Sin haɗin gwiwa ce ta sada zumunta a tsakanin ’yan uwa

Haɗin gwiwar Afirka da Sin haɗin gwiwa ce ta sada zumunta a tsakanin ’yan uwa

Daga CMG HAUSA Ministan harkokin wajen kasar Mali Abdoulaye Diop ya bayyanawa ’yan jarida a wata rubutacciyar zantawa a kwanakin baya cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Afirka da Sin, hadin gwiwa ce ta sada zumunta a tsakanin ’yan uwa. Ya ce, tun bayan da aka kafa dandalin hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC, dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu ke bunkasa yadda ya kamata, yana kuma fatan za a ci gaba da inganta hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu bisa tunanin samun moriyar juna. Minista Diop ya bayyana cewa, tun bayan kulla huldar diplomasiya tsakanin Mali da Sin…
Read More
Sin ta ƙaƙaba wa wasu Amurkawa biyu takunkumi

Sin ta ƙaƙaba wa wasu Amurkawa biyu takunkumi

Daga CMG HAUSA A matsayin wani mataki na mayar da martani, gwamnatin kasar Sin ta kakabawa wasu Amurkawa su biyu takunkumi, biyowa bayan takunkumin da gwamnatin Amurka ta kakakawa wasu jami’an kasar Sin su biyu a ranar 9 ga watan nan na Disamba, sakamakon zargin da Amurkan ta yi musu, wai masu alaka da wasu batutuwa masu nasaba da hakkin bil adama a Tibet. A cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, karkashin tanajin dokar mayar da martani ga matakan takunkumi daga sassan ketare ta kasar Sin, bangaren Sin din ya yanke shawarar ramawa-kura-aniyarta, ta hanyar kakabawa Miles Maochun Yu, da…
Read More