Editor

9513 Posts
Taƙaita cire tsabar kuɗi da sauran batutuwa

Taƙaita cire tsabar kuɗi da sauran batutuwa

Manufar cire kuɗaɗe da Babban Bankin Nijeriya CBN ya yi a baya-bayan nan, wanda zai taqaita adadin kaɗaɗen da mutane da kamfanoni za su iya fitarwa a kowane mako, ya sha suka daga ’yan siyasa da sauran ’yan Nijeriya. Sabuwar manufar ta sanya mafi girman cire kuɗi a kowane mako akan Naira 100,000 ga kowane mutum da 500,000 ga ƙungiyoyi da kamfanoni. Manufar cire tsabar kuɗin ta zo ne bayan da CBN ya sake fasalin takardar Naira 200, 500, da 1000. Manufar babban bankin zai duba yawan kuɗaɗen da ake samu a wajen tsarin banki. A cewar CBN, kusan kashi…
Read More
Wahalar fetur: Barazana ga bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara

Wahalar fetur: Barazana ga bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara

*Duk da gargaɗin DSS ƙarancin fetur na gurgunta harkokin rayuwa*’Yan Nijeriya sun koka da tsadar abinci da sufuri*Mun samar da miliyoyin ayyuka a fannin noma – Buhari Daga MAHDI M. MUHAMMAD Daga dukkan alamu wahalar samun man fetur a Nijeriya cikin ’yan kwanakin nan yana matuƙar barazana ga samun walwala da jin daɗin al’ummar ƙasar a lokacin da suke ƙoƙarin gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara mai kamawa ta 2023. A ranakun Lahadi da Litinin, 25 da 26 ga Disamba, 2022, za a gudanar da bikin ranar Kirsimeti, sannan kuma a ranar wata Lahadin ce za ta kasance…
Read More
Nijeriya ta tafka asarar tiriliyan N64.3 a shekara huɗu – Bankin Duniya

Nijeriya ta tafka asarar tiriliyan N64.3 a shekara huɗu – Bankin Duniya

Daga WAKILINMU Bankin Duniya ya ce, Nijeriya ta tafka asarar kuɗi Dalar Amurka biliyan 144.1, kwatankwacin Naira tiriliyan 64.3. Bankin ya ce rashin iya tattalin harkar canji daga bagaren Babban Bankin Najeriya (CBN) ne ya janyo wa ƙasar wannan asara daga 2017 zuwa 2021. Ya ce yadda CBN ke tafiyar da harkokin canjinsa ya haifar da rarrabuwar ra’ayoyin masana tattalin arziki da masu sharhi kan lamurra. Bayanan da Bankin Duniyar ya wallafa a shafinsa na intanet sun rashin iya tafiyar da sha’nin canjin daga ɓangaren CBN hakan ya sa kasar ta tafka asarar Dalar Amurka biliyan 144.1 daga 2017 daga…
Read More
Kirsimeti: FRSC ta tura jami’ai 1,769 da motocin sintiri 35 a Kaduna

Kirsimeti: FRSC ta tura jami’ai 1,769 da motocin sintiri 35 a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa FRSC, reshen Jihar Kaduna ta tura jami’ai aƙalla 1,769 da motoci 35 domin tabbatar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara ba tare da cikas ba a jihar. Muƙaddashin kwamandan sashin, Garba Lawal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kaduna. Lawal ya ce ma’aikata 1,769 da aka tura sun haɗa da jami’ai 290, da Marshals 979 da kuma jami'a na musamman guda 500. A cewarsa, an ɗauki matakin ne domin tabbatar da kiyaye doka a manyan titunan Kaduna, musamman a wannan bikin…
Read More
Kirsimeti: Gwamnati ta sake ayyana ranakun hutu

Kirsimeti: Gwamnati ta sake ayyana ranakun hutu

Daga WAKILINMU A karo na biyu, Gwamnatin Taraya ta sake sanar da ranakun hutun gama-gari albarkacin bukukuwan Kirsimeti da na Sabuwar Shekara. Gwamnatin ta ayyana ranar 26 da 27 ga Disamban 2022, da kuma 2 ga Janairun 2023 a matsayin ranakun hutu don bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara. Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnati cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis. Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen taya Kiristoci ’yan Nijeriya da sauran ‘yan kasa murnar wadannan bukukuwa. Haka nan, ya yi kira ga Kiristoci da su yi…
Read More
Wacce rawa Ma’aikatar Jinƙai ta taka wajen magance talauci da zaman banza?

Wacce rawa Ma’aikatar Jinƙai ta taka wajen magance talauci da zaman banza?

Duk da rahoton binciken da aka samo kwana-kwanan nan daga Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa  (NBS) cewa, sama da 'yan Nijeriya miliyan 133 ne suke rayuwa cikin talauci, amma Ma'aikatar Jinqai da Agaji tana cigaba da jajircewa akan ƙudurinta na tsamo matasa daga ƙangin talauci da rashin aikin yi. Ma'aikatar tana gudanar da ƙoƙarin nata ne ta hanyar Shirin N-Knowledge da shirin raya al'umma (NSIP) da sauran horarwa daban-daban. Rahoton na Hukumar NBS cewar mutane sama da miliyan 133 ne a Nijeriya suke fama da talauci ya zama kamar wani ƙarin ƙaimi a wajen ma'aikatar ta jinƙai kuma ya zaburar da…
Read More
Ƙarshen maha’inta ya zo – Saƙon Buhari na Kirsimetinsa na ƙarshe a matsayin Shugaban Ƙasa

Ƙarshen maha’inta ya zo – Saƙon Buhari na Kirsimetinsa na ƙarshe a matsayin Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya bai wa 'yan Nijeriya tabbacin ƙarshen maha'intar ƙasa ya zo, sannan 'yan ƙasa za su ga alheri a 2023 da ma bayan nan. Buhari ya bayyana haka ne cikin saƙon taya murnar Kirsimetin 2022 da ya isar wa 'yan ƙasa. Ya ce, “Saƙona na ƙarshe ke nan game da Kirsimeti a matsayin Shugaban Ƙasa. Nan da makonni 22 wannan gwamnatin za ta miƙa wa ta gaba ragamar mulki. “Wannan wata dama ce da ya kamata mu nuna wa duniya cewa a shirye Nijeriya take ta ƙarfafa dimokuraɗiyyarta. “A ci gaba da raya…
Read More
Shugaban Ƙasar Equatorial Guinea: Ƙasashen yamma sun yayata furucin wai “Sin na kafa tarkon bashi” a yunƙurin su na daƙile ƙasar

Shugaban Ƙasar Equatorial Guinea: Ƙasashen yamma sun yayata furucin wai “Sin na kafa tarkon bashi” a yunƙurin su na daƙile ƙasar

Daga CMG HAUSA Kwanan baya, shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya zanta da wakilin CMG a shirinsa na “Leaders Talk”, inda ya bayyana cewa, ya zama dole shugabannin kasashen Afirka su yi tunani a kan ta yaya za a kyautata kasashensu. "Don in ba haka ba, kasashen ba za su ci gaba ba, kuma wannan dalili ne da ya sa kasar Equatorial Guinea ta amince, tare da aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” tare da kasar Sin, kasancewar kasar Sin ta farko da take taimakawa Equatorial Guinea, da ma nahiyar Afirka baki daya. Don haka,…
Read More
EFCC ta farauto fiye da Naira Biliyan 201 na kuɗaɗen harajin ma’adanai daga kamfanoni

EFCC ta farauto fiye da Naira Biliyan 201 na kuɗaɗen harajin ma’adanai daga kamfanoni

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Hukumar Yaƙi da yi wa Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), ta bayyana cewar ta farauto zunzurutun kuɗaɗe fiye da Naira biliyan 201 kuɗaɗen harajin ma’adanai daga kamfanonin man fetur da ya kamata su bai wa Hukumar Bunqasa Cigaban Yankin Neja Delta (NNDC) da suka yi wa Hukumar Daidata Ƙa’idojin Haƙo da Man Fetur (NUPRC) ƙurmusu. Shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa shi ne ya yi wannan furuci yayin da yake yin jawabin manema labarai a wani shirin faɗakarwa da tawagar manema labarai a fadar shugaban ƙasa ta shirya makon jiya. Ya ce daga cikin wannan adadi,…
Read More