Editor

9513 Posts
Kudancin Nijeriya ya ba wa Arewa tazarar shekaru 40 a fuskar arziki – Bankin Duniya

Kudancin Nijeriya ya ba wa Arewa tazarar shekaru 40 a fuskar arziki – Bankin Duniya

AMINA YUSUF ALI Bankin Duniya ya bayyana cewa, jihohin Arewacin Nijeriya sai sun ɗauki tsahon shekaru 40 kafin su kamo jihohin Kudu a fannin tattalin arziki duba da yanayin yadda abubuwa suke tafiya a halin yanzu. Bankin ya bayyana cewa, yanayin rashin cigaba da bunƙasa da yankin Arewa yake yi na tsahon lokaci shi ya jawo wannan wawakekiyar tazara a tsakanin yankunan guda biyu. A cewar Bankin an bar yankin Arewa a baya a fannoni kamar noman zamani, harkar ma'adanai da masana'antu. Wannan ra'ayi yana ƙunshe ne a wani jawabi a kan tattalin arzikin Nijeriya (CEM) wanda bankin ya saki…
Read More
Okupe ya yada ƙwallon mangoro a Leba

Okupe ya yada ƙwallon mangoro a Leba

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Siyasar zaɓen 2023 na ƙara kankama inda ’yan takara da muqarrabansu, ke bayyana manufofi da abubuwan da su kan yi alƙawarin za su aiwatar in an ba su dama. Akasari a kan ce alƙawarin ’yan siyasa tamkar zane ne kan ruwa don a kan ambata komai cewa za a gyara kama daga ilmi, tsaro, tattalin arziki, noma, kiwo, zamantakewa da sauran su amma ba lalle ne ka ga duk waɗanda su ka ɗauki alqawuran sun cika kashi 20% ba. Hasalima wasu kan maida gwamnatin tamkar ta ’yan uwa ne da abokai a yi ta sharholiya a…
Read More
2023: Mutanen kirki kaɗai za ku zaɓa, Sarkin Musulmi ga ‘yan Nijeriya

2023: Mutanen kirki kaɗai za ku zaɓa, Sarkin Musulmi ga ‘yan Nijeriya

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar, ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su zaɓi mutane nagari masu kishin ƙasa a matsayin shugabanni a zaɓe mai zuwa. Ya bayyana haka ne a wajen bikin Saukar Karatun Alƙur'ani na mahadata 825 da Makarantar Hizburrahim gudanar cikin Ƙaramar Hukumar Funtuwa, Jihar Katsina. Basaraken ya ce, zaɓen 2023 ya ƙarto don haka akwai buƙatar jama'a su fito don su zaɓi nagartattun shugabanni waɗanda za su jagoranci ƙasa wajen ficewa daga halin da tale ciki. A cewarsa, "Yau ƙasarmu na neman wanda zai ceto ta daga mawuyacin halin…
Read More
Ƙungiyar Tsofaffin Kansilolin Kano ta nemi gwamnati ta biya ta haƙƙoƙinta

Ƙungiyar Tsofaffin Kansilolin Kano ta nemi gwamnati ta biya ta haƙƙoƙinta

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano Ƙungiyar Tsofaffin Kansilolin Ƙananan Hukumomin Jihar Kano 44 na shekara ta 2018 zuwa 2021 ta yi kira ga gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Mai girma gwamna Dk. Abdullahi Umar ganduje ofr Kadimul Islam, gwamnati Mai adalci da ta taimaka ta cika alqawarinta na biyan tsoffin kansilolin haƙƙinsu da suka ƙarƙare mulki a shekara ta 2021. Mai magana da yawu na ƙungiyar, Tsohon Kansila daga mazaɓar unguwa uku Ƙaramar Hukumar Tarauni, Hon. Garzali abdull-rahman Dogo, shine ya yi wannan koke ga gwamnatin, a madadin sauran kansilolin cikin hirarsa da manema labarai, ciki kuwa har da jaridar…
Read More
Buhari ya taya Ganduje murnar cika shekara 73 da haihuwa

Buhari ya taya Ganduje murnar cika shekara 73 da haihuwa

Daga WAKILINMU Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje murnar cika shekara 73 da haihuwa. Buhari ya yi hakan ne cikin sanarwar da ya fitar ta bakin mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ranar Asabar a Abuja. Ya kuma yaba wa Gwamnan bisa salon shugabancinsa da kuma ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi a Kano, tare da taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Daga nan, ya yi kira ga Gandujen da ya ci gaba da bai wa walwalar talakawan jihar muhimmanci da bunƙasa jihar.
Read More
Wang Yi ya yaba da ayyukan diflomasiyyar ƙasar Sin a shekarar 2022

Wang Yi ya yaba da ayyukan diflomasiyyar ƙasar Sin a shekarar 2022

Daga CMG HAUSA Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana cewa, a shekarar 2022, kasar Sin ta fuskanci kalubale, kana ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na diflomasiyya bisa kuduri mai kyau, yayin da ake nazari da bitar yanayin da duniya ke ciki gami da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen ketare. Wang ya bayyana hakan ne Lahadin nan a jawabin da ya gabatar a yayin taron tattaunawa kan yanayin kasa da kasa da alakar Sin da kasashen waje na kasar Sin. Da yake bitar ayyukan diflomasiyya na kasar Sin a…
Read More
Bai kamata Amurka ta qara faɗawa hanyar da ba ta dace ba

Bai kamata Amurka ta qara faɗawa hanyar da ba ta dace ba

Daga CMG HAUSA A karshen shekarar 2022 da muke ciki, kasar Amurka ta sake rura wuta a kan batun Taiwan. A ranar 24 ga wata, shugaba Joe Biden na Amurka ya sa hannu kan shirin dokar NDAA dangane da kasafin kudi ta fuskar tsaron kasa a shekarar 2023. Wannan doka ce da Amurka za ta aiwatar a cikin gida, amma Amurka ta fifita dokar fiye da dokokin kasa da kasa. Ta rufe idonta da gangan don kaucewa gaskiya, ta baza jita-jitar barazanar kasar Sin, ta kuma tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin. Dokar tamkar tsoma baki ne kan…
Read More
Kasafin 2023 ya samu tazgaro a Majalisar Dokoki

Kasafin 2023 ya samu tazgaro a Majalisar Dokoki

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja A ranar Alhamis, Majalisar Dokoki ta Nijeriya ta gaza amincewa da kasafin kuɗi na 2023, kamar yadda ta tsara tun asali, sakamakon yadda ta ce, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa mata kasafin cike da tazgaro. A jawabinsa yayin zaman majalisar, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce, an tsara Majalisar Dattawan za ta amshi rahoton Kwamitin Majalisar Kan Ƙudirin Kasafin Kuɗi na 2023, amma hakan ya gagara. A cewarsa, “sakamakon wasu manyan ƙalubale da ake fuskanta, ba mu iya karvar rahoton kasafin na 2023 ba, kuma ba komai ya janyo hakan ba…
Read More
An gama kashi na farko na ginin yankin raya masana’antu na PK24 a Cote d’Ivoire bisa taimakon ƙasar Sin

An gama kashi na farko na ginin yankin raya masana’antu na PK24 a Cote d’Ivoire bisa taimakon ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA Ranar 23 ga wata, aka kammala kashi na farko na aikin ginin yankin raya masana’antu na PK24 da kamfanin gina tashoshin jiragen ruwa na kasar Sin na CHEC ya gudanar a kasar Cote d’Ivoire. A jawabin da ya gabatar yayin bikin kammala aikin, firaministan kasar Cote d’Ivoire Patrick Achi Jérôme ya bayyana cewa, wannan babban aikin zai taimaka wajen kyautata hanyar raya tattalin arzikin kasar, da farfado da masana’antun kasar. Ya kuma karfafawa kamfanoni gwiwa, da su zauna da gindinsu a yankin raya masana’antu na PK24, a kokarin bayar da gudummawa ga ci gaban tattalin arziki da…
Read More
Shin ya kamata a kama gwamnan CBN?

Shin ya kamata a kama gwamnan CBN?

Assalam alaikum. Ina godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki. Allah Ya cigaba da taimakon jaridar Blurprint. A Nijeriya dai akan yi wasu abubuwa masu kama da wasan kwaikwayo. Rahotannin da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai na cewa Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS na shirin kama gwamnan babban bankin Nijeriya CBN, Godwin Emefiele. Wata babbar kotu a Abuja babban birnin ƙasar ta yi watsi da buƙatar DSS ta kamawa da tsare Emefiele. DSS na tuhumar Godwin da laifukan da suka shafi taimakawa ta'addanci, sai dai kotun ta ce hukumar ta koma ta samo ƙwararan hujjoji da shaidu kafin ta…
Read More