28
Dec
Daga BASHIR ISAH Al'uma mazauna yankin Ebute Metta a Jihar Legas sun shiga hali na jimami da alhini sakamakon gobarar da ta auku a yankin ranar Talata da safe. Rahotanni sun ce, gobarar ta ƙone gidaje da dukiya mai mai yawa. An ce gobarar ta fara ne daga wani gida sannan ta faɗaɗa zuwa maƙwabta. Wani ganau ya ce, "Da misalin ƙarfe 9:05 na safe na kira Hukumar Kwana-kwana inda jami'ansu suka isa wurin bayan minti 40. "Cinkoson jama'a da ya haɗu a wurin ya haifar da jinkiri, domin sai da 'yan sanda suka taimaka kafin 'yan kwana-kwanan suka samu…
