Editor

9513 Posts
Malamai a Bauchi sun ƙalubalanci hukuncin kisa a kan Abduljabbar

Malamai a Bauchi sun ƙalubalanci hukuncin kisa a kan Abduljabbar

• Sun ce za su ɗaukaka ƙara Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Wasu Jiga-jigan malaman addinin Musulunci dake ƙarƙashin tutar ‘As’habul Kahfi Warraqeen’ mazauna garin Bauchi sun yi kakkausar suka da fatali da abinda suka kira saɓanin addinin Islama, da hukunci kisa na jeka-na-yika da Alƙali Ibrahim Sarki Yola ya zartar a kan Shehin Malami Abduljabbar Nasiru Kabara bisa zargin yin ɓatanci ga Shugaban Halitta Muhammadu, (SAW) Aminci Allah ya tabbata a gare shi. “Wannan banbaraqwai da Islama, jeka-na-yi-kan hukunci da Ibrahim Sarki Yola ya zargi ɗumgurugum ɗinsa ba daidai ba ne kuma baya cikin Islama, saboda haka mun yi…
Read More
Sojojin Nijeriya sun kashe wasu kwamandojin Boko Haram a Borno

Sojojin Nijeriya sun kashe wasu kwamandojin Boko Haram a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu hare-hare ta sama da dakarun sojin Nijeriya suka kai ranar 20 ga watan Disamba a ƙauyen Mantari an yankin Gezuwa da ke cikin ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Nijeriya ya yiisanadin kashe wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Boko Haram. A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin sama na ƙasar Air Commodore Edward Gabkwet ya sanya wa hannu ya ce harin ya yi sanadin mutuwar manyan kwamandojin qungiyar da suka haɗar da Khaids Abbah Tukur da Maimusari da kuma Bakura Jega, tare da wasu 'yan ƙungiyar da dama. Labarin…
Read More
“Masu garkuwa da mutane ke iko da wani yanki na Jihar Zamfara”

“Masu garkuwa da mutane ke iko da wani yanki na Jihar Zamfara”

Daga SUNUSI MUHAMMAD a Gusau A Jihar Zamfara mutum huɗu sun mutu wasu goma sun samu raunuka a garin Ruwan Baure da ke cikin Ƙaramar Hukamar Gusau bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai a yammacin Litinin. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu garkuwa da mutanen suka sako wasu mutane sama da 200, sai dai sun kashe wasu mutum 28 a lokacin da suka yi garkuwar da su a garin Randa da ke cikin Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar ta Zamfara. Wannan mutumin da BBC ta sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya shaida harin da…
Read More
Kai ni fa na ga kamar Gwamna Ganduje Abba Gida-gida yake yi

Kai ni fa na ga kamar Gwamna Ganduje Abba Gida-gida yake yi

*Anya kuwa ba zai yi riƙo da dabarun Sanata Kwankwaso da Sanata Shekarau ba ne? Daga SUNUSI SHEHU Salamun alaikum, abokai da ‘yan uwa masu karatu. Na yi wannan rubutu ne cike da kokonto mai tarin yawa a zuciyata, saboda ganin yadda a hasashe da nazarina, kamar Gwamna Ganduje Abba Kabir na jam’iyyar adawa ta NNPP yake yi a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Kano, watau shi zai yi wa aiki a ɓoye, maimakon ɗan takarar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna. Ga dukkan alamu kuma bisa ga al’adar jagororin siyasar Kano na wannan zamani, wato tun daga 1999 ba sa…
Read More
Fashewa mai ƙarfi ta yi ajalin mutun huɗu a Kogi

Fashewa mai ƙarfi ta yi ajalin mutun huɗu a Kogi

Daga BASHIR ISAH An samu aukuwar fashewa mai ƙarfi da safiyar Alhamis a yankin Okene cikin Jihar Kogi, lamarin da ya yi ajalin aƙalla mutum huɗu kamar yadda rahoton 'yan sanda ya nuna. Majiyarmu ta ce, fashewar ta auku ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe na wannan rana. An ce fashewar ta auku ne a kusa da fadar Sarkin Ibira da ke hanyar Kuroko a Okene. Haka nan, fashewar ta yi sanadiyar ƙonewar wasu abubuwan hawa a yankin. Wani ganau ya ce, fashewar ta auku ne a cikin wata mota da wasu babura, inda duka matuƙa baburan suka mutu…
Read More
Shekaru shida na kwashe Ina ƙirƙirar baƙaƙe da lambobin Hausa – Sadar Musa

Shekaru shida na kwashe Ina ƙirƙirar baƙaƙe da lambobin Hausa – Sadar Musa

"Hausa harshe ne dake da rinjayen masu amfani da shi a Afrika" Daga AISHA ASAS a Abuja Idan ana zancen baiwa ta rubutu, ba na jin a faɗin Nijeriya akwai inda ya kai Arewa yawaitar marubuta da za a iya bugar ƙirji a kira su da gwanaye. Wataƙila namijin ƙoƙarin da suke yi ne ya haifar da wanzuwa da kuma raya yaren Hausa ga masu tasowa duk da irin horo da ruɗin da yaren Ingilishi ke yi a ƙwaƙwalensu. Cikin irin wannan ƙoƙari, aka samu wani matashi da ya yi kishin ƙirƙirar baƙaƙe da kuma lambobi da malam bahaushe zai buge ƙirji…
Read More
Shugaban Ƙungiyar Ohanaeze, George Obiozor ya kwanta da dama

Shugaban Ƙungiyar Ohanaeze, George Obiozor ya kwanta da dama

Daga WAKILINMU Shugaban ƙungiyar nan ta ƙabilar Ibo Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor ya rasu. Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma ne ya sanar da mutuwar cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba da daddare. Ya ce, “A madadin gwamnati da al’umar Jihar Imo, ni, Sanata Hope Uzodimma, Gwamnan Jihar Imo na sanar da rasuwar Shugaban Ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor ga duniya. “Farfesa George Obiozor , fitaccen masani, dattijo kuma uban ƙasa ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya. “Rasuwar shahararren jagoran Igbon kuma tsohon jakadan Nijeriya a Amurka, babban rashi ne ga Jihar Imo, yankin Kudu…
Read More
Zan iya kwaikwayon takalmi har a kasa gane bambanci – Kadeeja Ahmad

Zan iya kwaikwayon takalmi har a kasa gane bambanci – Kadeeja Ahmad

“Na yi kwarewar da zan iya gane ingancin takalma kowanne iri” Daga AISHA ASAS A yau shafin mata a yau ya ɗauko wa masu karatu matashiyar da ta zama allon kwaikwayo ga kowacce mace da ta san ciwon kanta, babba ko ƙarama, domin ta ce wa matasan mata idan ba ku yi, to, ku  ba ni wuri, kuma ta tabbatar wa mata cewa, ba sana’ar da mace ba zata iya yi ba ko ta fi ƙarfinta, domin ta ɗauko ɗaya daga cikin sana’o’in da suka yi tambari da sunan jinsin maza, wato sana’ar ƙera takalma, inda ta koya, ta iya,…
Read More
Majalisa ta amince wa Buhari ƙarin kasafin biliyan N819

Majalisa ta amince wa Buhari ƙarin kasafin biliyan N819

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dattawa ta amince da ƙarin kasafin biliyan N819 da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar mata don cike giɓin kasafin 2022. wannan na zuwa ne bayan da Majalisar ta ƙara wa'adin aiwatar da kasafin na 2022 zuwa ranar 31 ga Maris, 2023. Da farko dai Majalisar ta amince da tiriliyan N17.12 a matsayin kasafin 2022, daga bisani ta ƙara kasafin zuwa tiriliyan N17.31 bayan da Shugaba Buhari ya buƙaci hakan inda ya ce tasirin yaƙin Ukraine da Rasha ga tattalin arzikin ƙasa ya haifar da buƙatar ƙarin. A ranar Laraba Majlisar ta amince da kasafin bayan…
Read More