31
Dec
Daga WAKILINMU Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan, Cristiano Ronaldo ya rattaba hannu kan kwatiragi da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al-Nassr da ke Saudiyya inda za a biya shi zunzurutun kuɗi miliyan £175 a shekara. Ronaldo ya koma ƙungiyar Al-Nassr ne bayan ficewarsa da ƙungiyar Manchester United watan Nuwamban da ya gabata. Ƙungiyar ta Al Nassr ta tabbatar cewa lallai Ronaldo ya rattaba hannu kan kwangilar shekara biyu da ita. Yanke shawarar komawa Saudiyya ya kawo ƙarshen aikin gwarzon ɗan ƙwallon a matakin farko. Ana tunanin ya daɗe yana fatan ganin ya canza sheka zuwa kulob ɗin gasar Zakarun Turai…
