Editor

9513 Posts
Yari ya yi kukan murna da ganin dandazon masoya a Anka

Yari ya yi kukan murna da ganin dandazon masoya a Anka

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari wanda kuma shi ne shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen Gwamna Bello Matawalle a zaɓe mai zuwa ya zubar da hawaye kan ɗimbin magoya bayan Jam’iyyar APC da ya gani ranar Lahadi a garin Anka, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara. Yari wanda magoya bayan Jamiyyar APC suka buƙaci ya bai wa ɗimbin magoya bayansa kulawarsa domin nuna goyon bayansu gare shi ya sanya shi zubar da hawaye saboda farin ciki. A jawabinsa, Abdulaziz Yari ya bayyana jin daɗinsa kan irin goyon bayan da magoya bayan APC suka nuna…
Read More
Me ya sa wasu ’yan sanda ke buɗe wuta kan marasa laifi?

Me ya sa wasu ’yan sanda ke buɗe wuta kan marasa laifi?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ba ma wani baƙon abu ba ne yadda wasu baragurbi a cikin ’yan sanda ko ma sojoji da sauran jami’an tsaro kan buɗe wuta kan waɗanda ba su yi laifin komai ba kuma bisa dalilin da bai taka kara ya karya ba. Wannan na jawo ɗar-ɗar a zuciyar fararen hula ga wannan aji na jami’an da a ke biya daga baitul-malin gwamnati su riqa juya makamansu, su na hallaka jama’a ba gaira ba dalili. Haƙiƙa mutane da yawa sun ran su daga albarusan wasu daga jami’an tsaro da ke keta ƙa’idar aiki. Abun da ya kamata…
Read More
Rashin amsa gayyatar ‘yan takara ba zai sa mu yi ƙasa a gwiwa ba – CITAD

Rashin amsa gayyatar ‘yan takara ba zai sa mu yi ƙasa a gwiwa ba – CITAD

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano Dangane da cigaba da gayyato 'yan takarkarun kujerar majalisar jiha da tarayya da jama'a ke yi don miqa qudurorin su ga 'yan takarar da suka fito don wakiltar su. Ita ma karamar hukumar Dala dake jihar Kano ta bi bayan 'yan uwanta don gayyato 'yan takarar daga kowa ce jam'iyya ɗan takara yake madamar ya fito da nufin ya wakilci wannan ƙaramar hukumar ta Dala. A haka ne ma cikin irin ƙoƙarin al'ummar ne ranar Talatar nan suka gudanar da taron jin ra'ayoyin 'yan takarar tare da miƙa nasu buƙatun don kawo cigaba, wanda…
Read More
Tsaro, lafiya, noma da sufuri sun samu kaso mafi rinjaye a kasafin 2023

Tsaro, lafiya, noma da sufuri sun samu kaso mafi rinjaye a kasafin 2023

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Laraba ne Majalisar Dokokin Nijeirya ta ƙara ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2023 daga Naira tiriliyan 20.51 zuwa 21.82 sannan ta amince da shi. Kwamitocin kasafin kuɗi na Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun ce ƙarin Naira tiriliyan 1.3 na kasafin kuɗin ya biyo bayan ƙarin kuɗaɗen da aka ware wa hukumar ƙidaya ta ƙasa gabanin ƙidayar jama’a a shekarar 2023 da kuma Naira tiriliyan 173 da aka ware wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, gabanin babban zaɓen 2023. Rundunar sojojin Nijeriya da rundunar 'yan sandan Nijeriya, da ma'aikatun noma, lafiya, jiragen sama,…
Read More
Gargaɗin NDLEA kan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi

Gargaɗin NDLEA kan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi

A baya-bayan nan Shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Muggan Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Mohamed Buba Marwa, ya ce, a cikin watanni 22 hukumar ta kama fiye da ƙwayoyin tramadol miliyan 100 na haramtacciyar hanya da sauran muggan ƙwayoyi masu cutarwa. Yawan shan waɗannan ƙwayoyi na varna da rayuwar al'umma musamman matasa, wanda ake saran al’umma za su fahimci ɓarnar da matsalar ke haifarwa. Shugaban NDLEA, wanda ya bayyana hakan a yayin bikin bayar da lambar yabo da kuma ƙawata sabbin jami’an da aka ƙara wa girma a Abuja, ya ce, “A cikin ƙanƙanin lokaci, hukumar ta kama masu…
Read More
Gobe za a yi jana’izar Pele

Gobe za a yi jana’izar Pele

Daga BASHIR ISAH Gobe Litinin za a yi jana'izar sarkin ƙwallon ƙafa na duniya, wato Pele, wanda ya mutu a ranar Alhamis da ta gabata. Tsohuwar kulob ɗinsa a Brazil, Santos ce ta sanar da hakan a ranar Juma'a. Sanarwar ta ce, "Za a yi jana'izar sarkin ƙwallon ƙafa na duniya a Estadio Urbano Caldeira da ke Vila Belmiro. “Daga Asibitin Albert Einstein za a dauki gwar zuwa babban filin wasa a ranar Litinin." Shugaban Ƙasar Brazil mai barin gado, Jair Bolsonaro, ya ba da hutun kwana uku don zaman makoki game da rasuwar marigayin.
Read More
‘Yan sanda sun tsare basaraken da ya yi lalata da ɗan shekara 14 a Zariya

‘Yan sanda sun tsare basaraken da ya yi lalata da ɗan shekara 14 a Zariya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta kama wani basarake a Zariya da ya yi wa ɗan shekara 14 fyaɗe. Kakakin rundunar Muhammadu Jalige wanda shine ya sanar da haka ranar Laraba, ya ce rundunar za ta maka basaraken a kotu da zarar 'yan sanda sun kammala bincike akai. Da ya ke tattaunawa da Kamfanin Dillanci Labaran Nijeriya wani ɗan uwan wannan yaro, Hamza Zubairu ya ce basaraken ya yi lalata da ƙanensa ne ranar 9 ga Disamba a Unguwar Ƙwarbai. Zubairu ya ce basaraken makwabcin su ne kuma kowa a unguwan na yi masa…
Read More
2023: Buhari ya taya ‘yan Nijeriya murnar sabuwar shekara

2023: Buhari ya taya ‘yan Nijeriya murnar sabuwar shekara

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya 'yan Nijeriya murnar shiga sabuwar shekara ta 2023. Cikin saƙon nasa Buhari ya gode wa Allah da Ya ƙaddari 'yan ƙasar da ke raye ganin wannan lokaci. Ya yi fatan duka 'yan Nijeriya da suka kwanta dama kafin sabuwar shekarar, mutuwa ta zama hutu a gare su. Ya ce nan da wata biyar Nijeriya za ta samu sabon Shugaban Ƙasa da gwamnoni da sauransu. Don haka ya sha alwashin gudanar da sahihin zaɓe ƙarƙashin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), don bai wa 'yan ƙasa damar zaɓen shugabannin da suka dace. Ya…
Read More
Tsohon Fafaroma Benedict XVI ya kwanta dama

Tsohon Fafaroma Benedict XVI ya kwanta dama

Daga WAKILINMU Fadar Vatica ta tabbatar da cewa tsohon Fafaroma, Benedict XVI ya mutu yana da shekara 95 a duniya. Rasuwar tasa ta ranar Asabar na zuwa ne ’yan kwanaki bayan Fafaroma Francis ya yi kira ga Kiristoci da su yi masa addu’a saboda jikinsa ya yi zafi. A cewar fadar ta Vatica, Benedict, wanda shi ne Fafaroma na farko dan asalin ƙasar Jamus cikin sama da shekara 1,000, ya rasu ne a gidansa da ke Mater Ecclesiae. Ya kasance a cikin gidan dai tun lokacin da ya sauka daga mukamin nasa a shekarar 2013. Sai dai fadar ba ta…
Read More
Ganduje ya sallami Kwamishinan Addinai, Baba Impossible

Ganduje ya sallami Kwamishinan Addinai, Baba Impossible

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Gwamnatin Jihar ƙarƙashin Gwamna Abdullahi Ganduje, ta sallami Kwamishinnan Harkokin Addinai na Jihar, Baba Impossible daga aiki. Sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Kwamared Muhammad Garba, ya fitar a ranar Asabar ta nuna an dakatar da Kwamishinan ne saboda rahin biyayya ga tsare-tsaren gwamnati. Ta kara da cewa, an samu Baba Impossible da yin gaban kansa wajen rage wa ma'aikatan da ke ƙarƙashinsa kwanakin aiki ba tare da izinin gwamnati ba. Wato ya zabtare Laraba da Juma'a daga ranakun aiki wa ma'aikatan ma'aikatarsa. Haka nan ba ya biyayya ga Gwamnatin sau da ƙafa. Tuni dai…
Read More