03
Jan
Daga BASHIR ISAH A ranar Talata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya rattaɓa hannu a kasafin 2023 na Naira tiriliyan 21.83. Rattaɓa hannun ya haɗa da na ƙarin kasafin 2022 da Majalisar Tarayya ta sahale wa Buharin. Wannan dai shi ne karo na takwas kuma na ƙarshe da Buhari zai rattaɓa wa Kasafin Ƙasa hannu tun bayan da mulkin ƙasa ya koma hannunsa kusan shekara takwas da suka gabata. Da yake jawabi, Buhari ya ce an samu ƙarin tiriliyan N1.32 kan tiriliyan N20.51 da aka kasafta tun farko wanda hakan ya sa kasafin ya ƙaru zuwa tiriliyan N21.83. Shugaban ya ce…
