23
Dec
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A na cigaba da alhinin rashin shahararren jami’in diflomasiyya kuma Yariman Sakkwato, Alhaji Shehu Malami, wanda ya rasu yana da shekara 85 a duniya. Marigayi tsohon Jakadan Nijeriya a Afirka ta Kudu (lokacin Marigayi Janar Sani Abacha), ya rasu ne a ranar Litinin a Ƙasar Masar. Marigayi Sarkin Sudan na Wurno, haifaffen gidan sarauta ne na Sarkin Musulmi, wanda kuma ya taso a gidan Sarkin Musulmi Abubakar, ya riƙe matsayin Babban Sakataren Sarkin Musulmi a shekarar 1960. Ya yi karatu a makarantu daban-daban da suka haɗa da firamare a Sakkwato, Makarantar Lardin Kano, Makarantar…
