Editor

9513 Posts
Sin tana dai da moriyar jama’a a G’gaban komai yayin da take aiwatar da matakan yaƙi da cutar Covid-19

Sin tana dai da moriyar jama’a a G’gaban komai yayin da take aiwatar da matakan yaƙi da cutar Covid-19

DAGA MINA Abokai, kasar Sin ta daidaita matakanta na kandagarkin cutar COVID-19, daga dakile yaduwar cutar COVID-19 da zarar an gano ta don tabbatar da kare rayukan jama’a, zuwa maido da zaman rayuwar jama’a da farfado da tattalin arziki. Matakin da ya nuna cewa, gwamnatin Sin tana tsai da manufar da ta dace da halin da kasar ke ciki da ma rikidewar nau’in kwayar cutar. Duk wata manufa da gwamnati ta dauka na mai da moriyar jama’a a gaban kome, abin da ya bayyana niyyar gwamnati ta bautawa jama’a. Mai zane kuma mai rubutu: MINA
Read More
A sanadin rubutu na auri matata – Abu Hisham

A sanadin rubutu na auri matata – Abu Hisham

"Ana cin mutuncin adabi da rashin bin ƙa'idojin rubutu" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Akwai wasu mutane da Allah ya yi wa baiwa da kwarjini a rayuwar su, saboda tsarkin zuciyar su, kyakkyawan tunani da kuma ma dai wani sirrin da shi kaɗai ya bar wa kansa sani. Irin waɗannan mutane ko yaya suka nemi voye kansu ba sa vata ko da a cikin dubban jama'a, sai wani abu ya fitar da hasken su. Ana samun irin su a cikin kowacce al'umma cikin su kuwa har da marubuta, fitilun al'umma. Sunan Mukhtar Musa ƙarami da ake yi wa laƙabi da Abu…
Read More
Hajjin 2023: Saudiyya ta maido wa Nijeriya gurbin maniyyata 95,000 da ta saba ware mata

Hajjin 2023: Saudiyya ta maido wa Nijeriya gurbin maniyyata 95,000 da ta saba ware mata

Daga BASHIR ISAH Masarautar Saudiyya ta sake maido wa Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON), gurbin maniyyata 95,000 da ta saba ba ta a baya don Hajjin 2023 idan Allah Ya kai mu. Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na hukumar, Mousa Ubandawaki ne ya bayyana hakan ranar Laraba. Ya ce, “Ma'aikatar Hajji da Umarah ta Saudiyya ta ware Nijeriya gurbin maniyyata 95,000 da ta saba ba ta don Hajjin 2023 a ƙasa mai tsarki. “Mai yiwuwa damar sauke farali ga ɗimbin 'yan Nijeriya masu buƙatar hakan ta samu ke nan kasancewar Saudiyya ta maido wa NAHCON gurbin…
Read More
CBN ya ƙara adadin kuɗin da za a iya cirewa zuwa dubu N500

CBN ya ƙara adadin kuɗin da za a iya cirewa zuwa dubu N500

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya sanar da ƙara adadin kuɗin da mutum zai iya cirewa a banki. Bankin ya ce, ɗaiɗaikun mutane na iya cire abin da bai wuce N500,000, sannan Naira miliyan N5 ga hukumomi a mako. Ya ƙara da cewa, za a iya cire kuɗin ne ta duka kafofin cire kuɗin da ake da su ba tare da wani hani ba. Wannan bayanin na ƙunshe ne cikin wasiƙar da CBN ɗin ya aike wa bankuna da ita a ranar Laraba. Wannan na zuwa ne mako biyu bayan da CBN ya rage adadin kuɗin da ɗaiɗaikun…
Read More
Yarjejeniyar kare mabambanta hallitu a duniya ta Kunming da Montreal ta fidda wata hanya mai dacewa a fannin kare hallitu

Yarjejeniyar kare mabambanta hallitu a duniya ta Kunming da Montreal ta fidda wata hanya mai dacewa a fannin kare hallitu

DAGA CMG HAUSA Taron COP15 ya taya murnar zartas da yarjejeniyar kare mabambanta hallitu a duniya ta Kunming da Montreal, a ranar 19 ga wata. Matsayin wannan yarjejeniya ya yi kama da yarjejeniyar Paris, a fannin kare mabambanta hallitu, wadda ta fidda wata hanya da ta dace ga kare mabambanta hallitu nan da shekarar 2030 masu zuwa, har zuwa gaba. Wannan yarjejeniya ta kunshi muradu 23. Daga cikinsu, abin da aka sa gaba shi ne, alkawarin kare filaye da koguna da tabkoki da tekuna da yawansu ya kai a kalla 30% a duniya kafin shekarar 2030, wanda ake kiransa “Burin…
Read More
Ƙungiyoyin cinikayya na Sin sun tafi waje don neman jari

Ƙungiyoyin cinikayya na Sin sun tafi waje don neman jari

DAGA CMG HAUSA Kwanan baya, kasar Sin ta sauya manufarta ta kandagarkin cutar COVID-19 bisa halin da ake ciki, hakan ya sa kamfanoni masu cinikin shige da fice na wuraren daban-daban na kasar Sin suka yi hayar jiragen sama na musamman domin fita waje neman jari. Ya zuwa yanzu, larduna 9, cikinsu har da Guangdong da Zhejiang da Jiangsu da Fujian da sauransu, sun kafa kungiyoyi ko hukumomin cinikin shige da fice, da nufin zuwa kasashen waje don habaka kasuwa da neman kwangiloli. Tun daga watan Yulin bana, birnin Ningbo na lardin Zhejiang ya kafa kungiyoyi a ko wace wata,…
Read More
Buhari: Don Allah ka dakatar da Gwamnan CBN

Buhari: Don Allah ka dakatar da Gwamnan CBN

Daga DAKTA ALIYU U. TILDE Shawarar da Ɗan Majalisar Tarayya, Alhaji Gudaji Kazaure, ya bayar na dakatar da gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, tana da kyau sosai kuma tana bisa ƙa’ida. Kai, ma iya cewa ma ta zama babbar buƙatar ƙasa a yanzu. Idan ba a ɗaga kaza daga makwancinta ba, ba za a san me fukafukanta suka boye ba. Don haka, ƙa’ida ce mai kyau idan za a yi bincike mai zurfi musamman idan wanda yake shugabantar wurin yana nuna tirjiya da ƙoƙarin danne gaskiya, to a dakatar da shi. Shugaba Buhari ya sa Honarabul Kazaure aikin bincike a…
Read More
Kyakkyawar Jumma’a….

Kyakkyawar Jumma’a….

Daga CMG HAUSA A yayin da ake tunanin ci gaban duniya zai yi rauni sosai a shekarar 2023, a hannu guda kuma ana sa ran tattalin arzikin kasar Sin zai farfado da kuma inganta, har ma ya amfani duniya baki daya. Idan ba a manta ba, a ranar Juma'ar da ta gabata ce aka kammala babban taron shekara-shekara kan aikin raya tattalin arzikin kasar Sin a birnin Beijing, inda aka tsara ka'idojin raya tattalin arzikin kasar na shekara mai zuwa, da tsara muhimman batutuwan da suka shafi harkokin tattalin arziki na shekara mai zuwa, gami da fadada bukatun cikin gida,…
Read More
Darajar kuɗin Nijeriya daga 2004 Zuwa 2022

Darajar kuɗin Nijeriya daga 2004 Zuwa 2022

Daga AMINU ƊAN ALMAJIRI Wanda duk ya kalli irin tuƙin da ake yi wa Nijeriya a yau, ya san ana yi mata tuƙin da zai kai ta ga halaka. Da yawa mutane ban sani ba, son zuciya ne ya sa idan Khalifa Muhammad sanusi II ya yi magana a kan shaanyin tattalin arziki da sha'anin mulkin ƙasar nan suke masa ca! Ko kuwa rashin sani? idan rashin sani ne, sai na ce dama masu hikima sun ce, 'Ɗan Adam maqiyin abinda ya jahilita ne'. idan kuwa son zuciya ne, ya kamata kam yanzu su fito su faɗa wa jama'a cewa,…
Read More
Kwankwasiyya JAMB, NECO da WAEC Kyauta: Anya?!

Kwankwasiyya JAMB, NECO da WAEC Kyauta: Anya?!

Daga FATUHU MUSTAFA Wato ina ga Kwankwaso yana abin nan ne da Bature ke cewa 'Clever by half'. Ga wanda bai san me ake nufi da wannan azancin na Bature ba, sai ya nemi Magana Jari ta ɗaya ya karanta labarin 'Mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi Jiɓi (Gumi)'. Ya yi hakan ne ta hanyar gaya wa mutane abinda suke so su ji ko da kuwa ba zai yiwu ba. Musamman tunda ya lura mutane, son ransu ne a gabansu ba son gaskiya ba. Amma in dai mutane gaskiya suke so, da sai su tambaye shi, mun ji za…
Read More