21
Dec
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ashe matsalar tsaro da ake fama da ita a Arewa, na da nasaba da kisan ƙare dangi da Fulani ke yi wa ƙabilar Hausawa? Tun da ake samun ƙalubalen tsaro a jihohin Arewa maso yammacin Nijeriya tsakanin Fulani makiyaya da Hausawa manoma, ban taɓa kawo wannan tambayar a raina ba, don ina ganin ba batun kisan ƙare dangi ba ne, tsohuwar rigima ce da aka saba fuskanta tsakanin manoma da makiyaya, ƙalubalen ɗumamar yanayi da ya kai ga cinye burtalolin shanu zuwa filayen gonaki, da kuma uwa uba shigar vata gari cikin harkar satar shanu da…
