Editor

9513 Posts
Bunƙasar tattalin arzikin zamani na ƙasar Sin ya samar da sabbin damammaki ga duniya

Bunƙasar tattalin arzikin zamani na ƙasar Sin ya samar da sabbin damammaki ga duniya

Daga CMG HAUSA Alkaluman kididdiga da aka fitar na nuna cewa, daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2021, yawan tattalin arzikin zamani na Sin ya karu daga yuan triliyan 11 zuwa fiye da yuan triliyan 45, inda adadin tattalin arzikin zamani a GDP ya karu zuwa kashi 39.8% daga 21.6%. Ya zuwa ga watan Yuni na bana, masana’antun yanar gizo, sun shafi manyan nau’o’in tattalin azrikin al’umma guda 45, inda aka saki makamashin motsi na masana'antun zamani. A shekarar 2020, Sin ta fitar da ajandar tsaron kididdigar kasa da kasa, inda take fatan yin amfani da wannan mataki a matsayin wata…
Read More
Matsalar ƙarancin likitoci na ƙara taɓarɓarewa a Nijeriya, inji NARD

Matsalar ƙarancin likitoci na ƙara taɓarɓarewa a Nijeriya, inji NARD

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Nijeriya (NARD) ta ce, ƙarancin likitocin da ake fuskanta a ƙasar ya yi munin da a yanzu likita zaya ne ke duba marasa lafiya 10,000. Ƙungiyar ta ce, a halin da ake ciki, likitocin da ake da su a faɗin ƙasar ba su wuce 10,000 ba. Ta ce, adadin likitocin raguwa ya ke kullum sakamakon barin ƙasar da suke yi zuwa aiki a ƙasashen waje. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dokta Emeka Orji, ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da manema labarai. A cewarsa, kimanin likitoci 100 ne ke barin…
Read More
Dandalin shawara: Cikin da ke jikina ba na mijina ba ne

Dandalin shawara: Cikin da ke jikina ba na mijina ba ne

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Ina yini Asas, ya ayyuka. Don Allah ki ba ni shawara ba tare da kin yi min mummunar fahimta ba. Ciki nake ɗauke da shi, kuma sai aka samu tsautsayi ba na mijina ba ne, duk da cewa bai iya ganewa ba, amma na kasa samun natsuwa akan sirrin da na voye. Watanin baya na yi tafiya ganin gida garimu……, to kafin na tafi, maigidana ya yi fama da zazzaɓi, don haka mun kwana kusan goma sha bai taɓa ni ba, da ya samu sauƙi kuma sai na fara jinin al’ada, a cikin wannnan halin na…
Read More
Kotu ta ɗaure masu taimaka wa ‘yan bindiga a Neja

Kotu ta ɗaure masu taimaka wa ‘yan bindiga a Neja

Daga BASHIR ISAH Wata Koton Majastare mai zamanta a Minna, babban birnin Jihar Neja, ta ɗaure wasu mutum uku shekara uku a gidan yari bayan da ta same su da laifin taimaka wa 'yan bindiga a jihar. Alƙalin kotun, Hajiya Fati Kabir, ta ce masu laifin za su yi zaman kurkukun ne haɗi da aiki mai wahala. Kotun ta kama Abubakar Abdullahi da Abubakar Musa da kuma Kabir Mohammed ne da laifuka biyu, wato taimaka wa 'yan ta'adda da taimaka wa masu laifi wajen tserewa. Laifukan da Kotun ta ce sun saɓa wa sassa na 3 (1) da na 4…
Read More
Mabiya Shi’a sun gudanar da taron tunawa da ranar 12 ga watan Disamba

Mabiya Shi’a sun gudanar da taron tunawa da ranar 12 ga watan Disamba

Daga MOHAMMED ALBARNO A ranar Litinin 12 ga watan Disamba, Mabiya Shi'a ƙarƙashin Jagorancin Sheikh Zakzaky suka yi taron tunawa da ranar 12 ga watan Disamba wanda suke zargin sojojin Nijeriya da barin wuta kan ’yan uwansu a shekara ta 2015. Ranar 12 Disamba, rana ce da dukkan wani mabiyi na Sheikh Zakzaky ke ɗaukarsa a matsayin rana ta baƙin ciki. Rana ce da sojoji ke zargin ’yan shi'a da tare wa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na lokacin, Laftanar-Janar Tukur Burutai, hanya. Shekaru 7 baya, a shekara ta 2015, anyi varin wuta a Zaria, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane…
Read More
‘Yan Arewa na sayar da katin zaɓen su Naira 2,000, inji NEF

‘Yan Arewa na sayar da katin zaɓen su Naira 2,000, inji NEF

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar Dattawan Arewa, NEF, ta yi zargin cewa 'yan Nijeriya mazauna arewacin ƙasar na sayar da Katin Zaɓen d'Dindindin (PVCs) kan Naira 2000. Daraktan Yaɗa Labarai na NEF, Hakeem Baba Ahmed, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Laraba. Sanarwar ta ce, NEF ta tabbatar da abin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce game da lamarin. Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne INEC ta bayyana cewa ta bankaɗo yadda wasu ’yan Nijeriya ke sayen katin zaɓe na PVC tare da…
Read More
DSS ta janye jami’anta daga tawagar Gwamna kan rashin jituwa da ‘yan sanda

DSS ta janye jami’anta daga tawagar Gwamna kan rashin jituwa da ‘yan sanda

Daga WAKILINMU Hukumar tsaro ta DSS ta janye jami'anta daga tawagar Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke. Mamhaja ta kalato cewa, hamayyar da ke tsakanin jami'an DSS ɗin da na 'yan sandan yankin ce ta haifar da janye jami'anta da DSS ta yi. Jaridar Vanguard ta rawaito cewar, a makon da ya gabata babban ofishin DSS ya janye jami'ansa daga tawagar Gwamna Adeleke, tare da buƙatar gwamnan ya kiyaye tsarin ba da tsaro yadda ya kamata. Cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi, Mai magana da yawun Gwamnan, Olawale Rasheed, ya ce hakan ya faru ne sakamakon rashin fahimtar da ya…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Argentina ta lashe Kofin Duniya

Da Ɗumi-ɗumi: Argentina ta lashe Kofin Duniya

A ranar Lahadi aka buga wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya da aka gudanar a ƙasar Qatar. An buga wasan ƙarshen ne tsakanin Argentina da Faransa. Bayan fafatawa na tsawon minti sama da 100 a wasan, a ƙarshe Argentina ta yi nasara a kan Faransa, inda ta doke ta a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Yanzu dai ya tabbata Argentina ce ta zama gwarzuwa a gasar wannan karon. Cikakken bayani na nan tafe...
Read More

Pierre Moussa: Hanyar da Ƙasar Sin ke bi ta zamanantar da ƙasa abun koyi ne ga ƙasashen Afirka

Daga CMG HAUSA Shugaban jam’iyyar PCT mai mulki a kasar Congo Mr. Pierre Moussa, ya ce hanyar da kasar Sin ke bi wajen zamanantar da kasa, abun koyi ne ga kasashe masu tasowa musamman ma kasashen Afirka. Moussa ya bayyana hakan ne, yayin wata zantawa da ya yi kwanan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya yi tsokaci game da jigon "samar da ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire" da sauran su, yana mai cewa, hakan zai wayar da kan kasashen duniya masu yawa, musamman wadanda suke a nahiyar Afirka. Jami’in ya kara da cewa, manufofin bunkasa kasa na…
Read More
Hukumar NEMA ta raba tallafin kayan abinci na Sarkin Saudiyya ga ‘yan gudun hijirar Borno

Hukumar NEMA ta raba tallafin kayan abinci na Sarkin Saudiyya ga ‘yan gudun hijirar Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, ta fara rabon kayayyakin abinci da cibiyar bada agaji ta Sarki Salman, KSrelief, ta raba wa sansanonin ‘yan gudun hijira guda takwas da kuma al’ummar jihar Borno. A cewar wata sanarwa a ranar Larabar da ta gabata ta bakin shugaban sashen yaɗa labarai na NEMA, Manzo Ezekiel, Gwamna Babagana Zulum ne ya ƙaddamar da rabon abincin a sansanin ‘yan gudun hijira na El-Miskin dake Maiduguri tare da taimakon babban daraktan hukumar ta NEMA, Mustapha Habib-Ahmed. A nasa jawabin, Gwamna Zulum ya miƙa godiyarsa ga Sarkin Saudiyya Salman…
Read More