Editor

9513 Posts
Kyan alƙawari cikawa

Kyan alƙawari cikawa

Daga Lubabatu Lei Daga ranar 13 zuwa 15 ga wata, an gudanar da taron kolin kasar Amurka da kasashen Afirka karo na biyu a birnin Washington, babban birnin kasar ta Amurka, wato shekaru 8 ke nan tun bayan da aka gudanar da taron a karo na farko. A shekarar 2014, gwamnatin Obama ta gudanar da taron karo na farko, inda kuma ya yi alkawarin karfafa huldar da ke tsakanin kasar Amurka da kasashen Afirka da ma gudanar da taron a kai a kai. Sai dai ba a yi zaton za a jima tsawon shekaru 8 kafin a kaddamar da taron…
Read More
An rufe babban taron COP 15

An rufe babban taron COP 15

Daga CMG HAUSA Jiya Asabar 17 ga wata ne, aka rufe babban taro a mataki na biyu, na sassan da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kare mabambantan halittu ta Majalisar Dinkin Duniya karo na 15, ko COP 15 a takaice a kasar Kanada, inda shugaban taron, wanda kuma shi ne ministan kula da muhallin halittun kasar Sin, Huang Runqiu, ya jagoranci bikin rufe taron. Bangarori mahalarta taron sun bayyana fatansu, na aiwatar da “tsarin kasancewar mabambantan halittu a duniya bayan shekara ta 2020” ba tare da bata lokaci ba. Huang ya ce, an cimma tudun-dafawa, a yayin babban taron na…
Read More
Gwamna Masari ya sallami Mataimakin Shugaban Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua

Gwamna Masari ya sallami Mataimakin Shugaban Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua

Daga UMAR GARBA a Katsina Majalisar Zartaswar Jihar Katsina ƙarƙashin jagoracin Gwamna Aminu Bello Masari ta umarci Shugaban Jami'ar jihar Farfesa Sanusi Mamman da shugaban hukumar gudanarwa na jami'ar da su ajiye muƙamansu ba tare da ɓata lokaci ba. Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan ilimi mai zurfi Dakta Bashir Usman ruwan godiya ne ya bayyana haka a ƙarshen zaman majalisar da ya gudana ranar Laraba a Fadar Gwamnatin Jihar. Sauke shi daga muƙamin ya biyo bayan rahoton da kwamitin da Gwamna Masari ya kafa a kan ya ba shi shawara dangane da ƙorafe-ƙorafen da aka yi wa shugaban…
Read More
Mun karɓe Naira biliyan 30 a hannun dakataccen Akanta-Janar, Ahmed Idris – EFCC

Mun karɓe Naira biliyan 30 a hannun dakataccen Akanta-Janar, Ahmed Idris – EFCC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa, ta ce, zuwa yanzu an karve Naira Biliyan 30 daga hannun dakataccen Akanta-Janar, Ahmed Idris.  Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa waɗannan biliyoyi su na cikin Naira biliyan 109 da ake zargin Ahmed Idris ya karkatar a lokacin yana riqe da ofishin Akanta Janar na Ƙasa.  Shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa ya shaida wa duniya wannan a lokacin da ya halarci wani taro da aka yi da manema labarai jiya. EFCC ba ta yi cikakken bayani a kan kuɗin da aka…
Read More
2023: Rundunar ‘yan sandan Kano ta gana da sauran hukumomin tsaro

2023: Rundunar ‘yan sandan Kano ta gana da sauran hukumomin tsaro

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano A ranar Talatar da ta gabata ne rundunar 'yan sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Mamman Dauda ta gana da Hukumar Zaɓe reshen Jihar Kano da sauran hukumomin tsaro dake jihar, don ɓullo wa matsalolin da ka iya bijirowa yayin gudanar da zaɓen shekarar 2023. Da yake jawabinsa lokacin taron, shugaban kwamitin hukumomin tsaro na Jihar Kano kuma jagoran rundunar 'yan sandan ta Kano CP Mamman ya bayyana cewa wannan taron na da nufin samar da kyakkyawan tsaro a dukkan guraben jefa ƙuri'a kimanin 11,222 dake akwai a faɗin ƙananan hukumomi 44 dake jihar.…
Read More
INEC ta koka: ’Yan siyasa na sayen katin zaɓe

INEC ta koka: ’Yan siyasa na sayen katin zaɓe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce, wasu ’yan siyasa su na sayen katin zaɓe na dindindin (PVC) daga hannun masu kaɗa ƙuri'a. Mohammed Haruna, muƙaddashin kwamishinan INEC na ƙasa mai kula da babban birnin tarayya Abuja, Nasarawa, Kaduna da Filato, ya bayyana haka a ranar Litinin yayin ƙaddamar da shirin ‘VoteMatters’ na NESSACTION a Abuja. Kamar yadda aka ruwaito, Haruna ya ce, hukumar zaɓe na kai farmaki kan ’yan kasuwar bayan fage masu sayar da katin zaɓe. “Muna sane da cewa wasu ’yan siyasa sun duqufa sayen katunan zaɓe. Ba daidaj bane…
Read More
Shugaban Ƙasar Ghana ya buƙaci Buhari ya daina roƙon ƙasashen yammaci rance

Shugaban Ƙasar Ghana ya buƙaci Buhari ya daina roƙon ƙasashen yammaci rance

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasar Ghana, Mista Nana Akufo-Addo, ya buƙaci Shugaban Nijeriya, Muhammad Buhari, da sauran takwarorinsa na Afirka da su daina roƙon lamunin rance daga ƙasashen yammacin duniya, domin nahiyar Afrika ta samu karɓuwa a duniya. Shugaban na Ghana ya bayyana haka ne yayin jawabin buɗe taron shugabannin ƙasashen Amurka da Afirka da ke gudana a birnin Washington a ranar Talata 13 ga watan Disamba, 2022. A cewarsa, ƙasashen Afirka za su haskaka cikin ƙasashen da suka cigaba idan har nahiyar ta daina bara. Ya ba da shawarar cewa, a yi amfani da albarkatun da ke nahiyar…
Read More
Sin ta yi kira ga ɓangarori daban-daban na Libya da su daidaita matsalolinsu a siyasance

Sin ta yi kira ga ɓangarori daban-daban na Libya da su daidaita matsalolinsu a siyasance

Daga CMG HAUSA Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana a jiya cewa, Sin ta yi kira ga bangarori daban-daban na kasar Libya da su warware matsalolinsu a siyasance, da yin hakuri da juna bisa karfinsu da kiyaye zaman lafiya da aka wanzar da shi cikin wuya. Geng Shuang ya bayyana haka a taron tattauna kan batun Libya na kwamitin sulhu na MDD, an jinkirta zaben Libya har tsawo shekara guda tun daga ran 24 ga watan Disamba na bara. A cikin wadannan lokuta, bangarori daban-daban da abin ya shafa a Libya ba su kai ga…
Read More
Sin ta gudanar da taron shekara-shekara na ayyukan tattalin arziki don tsara shirin shekarar 2023

Sin ta gudanar da taron shekara-shekara na ayyukan tattalin arziki don tsara shirin shekarar 2023

Daga CMG HAUSA Daga ranar Alhamis zuwa Juma'a 16 ga wata ne, aka gudanar da babban taron kolin tattalin arziki na shekara-shekara a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda shugabannin kasar Sin suka yanke shawarar kan sassan da za a ba da fifiko kan ayyukan raya tattalin arziki na shekarar 2023. Da yake gabatar da muhimmin jawabi a yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi nazari kan ayyukan tattalin arzikin kasar a shekarar 2022, tare da nazari kan halin da ake ciki a fannin tattalin arziki, da kuma tsara aikin raya tattalin arziki na shekarar 2023…
Read More
Wakilin Sin: Ya kamata Sin da EU su haɗa kai don kiyaye tsarin samar da kayayyaki

Wakilin Sin: Ya kamata Sin da EU su haɗa kai don kiyaye tsarin samar da kayayyaki

Daga CMG HAUSA Shugaban tawagar kasar Sin a kungiyar Tarayyar Turai (EU) Fu Cong ya bayyana cewa, ya kamata kasar Sin da kungiyar tarayyar Turai, su yi aiki tare don kiyaye masana'antu da tsarin samar da kayayyaki yadda ya kamata, da yin watsi da dakile tsarin, da ba da kariya da sunan tsaro. Da yake jawabi a yayin taron shugabannin kasashen Sin da EU karo na biyar, kana taron tattaunawar tsoffin manyan jami'ai, Mr. Fu ya ce, kasar Sin ta bayyana karara a yayin babban taron wakilan JKS karo na 20 cewa, za ta tabbatar da dorewar manufofinta na cikin…
Read More