Editor

9513 Posts
Badaƙalar kuɗin harajin bankuna

Badaƙalar kuɗin harajin bankuna

A Nijeriya, batun harajin da bankuna ke cire wa waɗanda suka yi amfani da asusun ajiya wajen tura kuɗi ko cirewa na cigaba da janyo cece-kuce. A makon da ya wuce ne kwamati na musamman da Shugaba Muhammdu Buhari ya kafa domin gudunar da bincike kan cajin cirewa da ajiyar kuɗi a asusun banki ya yi zargin cewa wasu hukumomin da binciken ya shafa suna ƙoƙarin hana shi yin aikinsa, da kuma hana shi ya mika wa Buhari rahotonsa. Sai dai sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter, mai magana da ywun shugaban Nijeriya Malam Garba Shehu ya ce…
Read More
Gudaji da fadar Aso Rock: A gano mana gaskiya!

Gudaji da fadar Aso Rock: A gano mana gaskiya!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Tun 2003 da Shugaba Buhari ya fara neman takarar shugabancin Nijeriya ya ambata batun yaƙi da cin hanci da rashawa ya zama cikin kan gaba a abubuwan da zai yaka matuƙar Allah ya ba shi nasarar lashe zaɓe. Hatta a jawabin kifar da gwamnatin farar hula ta shugaba Shehu Shagari a jamhuriyya ta biyu, shugaba Buhari ya kawo dalilan amshe madafun ikon da yadda ’yan siyasa suka afka cin hanci da rashawa. A wannan lokacin ta kai ga shugaban amincewa da ɗaure mutane fiye da shekaru 100 a gidan yari don samun su da laifin zarmiya.…
Read More
Batun raba katin zaɓe

Batun raba katin zaɓe

Assalam alaikum. Fara ba da katunan zaɓe na dindindin ga wasu daga cikin masu zaɓe a Nijeriya ya ja hankalin 'yan ƙasa inda kowa ke bayyana ko tofa albarkacin bakinsa. A wannan Litinin din Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Inec ta soma wannan aiki kuma mutanen da za a bai wa katunan su ne mutanen da suka ba da sunayensu daga farkon 2022, zuwa lokacin da aka rufe aikin a watan Yuli. Sai dai kuma duk da irin tsare-tsare da INEC ta ce ta yi, ana ta samun masu ƙorafi da kokawa kan dogayen layuka wajen samun katin, da…
Read More
Buhari ya kinkimo bashin tiriliyan N3 duk da tiriliyan N45 da ake bin gwamnatinsa

Buhari ya kinkimo bashin tiriliyan N3 duk da tiriliyan N45 da ake bin gwamnatinsa

Gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Buhari ta sake kinkimo bashin Dalar Amurka biliyan $9 daidai da Naira tiriliyan 3.98 daga Bankin Duniya. Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Shubham Chaudhuri ne ya bayyana haka a wajen taron da ya shirya a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata. Shubham Chaudhuri ya ce, zaman Bankin Duniya a Nijeriya ba shi da burin da ya wuci taimaka wa ƙasar ficewa daga ƙangin talaucin da take ciki da kuma inganta rayuwar al'ummarta. A baya, jaridar Intel Region ta rawaito cewar, bashin da ake bin Nijeriya ya ƙaru zuwa Naira tiriliyan N45.8 ($103 billion) a…
Read More
Barazanar jefa ƙuri’ar ƙananan yara

Barazanar jefa ƙuri’ar ƙananan yara

Ƙuri’ar ’yan ƙasa da shekaru 18 wata ɓarna ce a tsarin zaɓen Nijeriya. Shekarun da suka cancanci shiga zaɓe a ƙasar sune ’yan shekaru 18 zuwa sama. Sai dai a lokacin zaɓe, ana barin yara su kaɗa ƙuri’a a wasu sassan ƙasar. Wani lokaci ma matattu ma suna yin zaɓe. Kuma wannan shine tushen fara rigingimu. Lokacin da aka ba wa yaran da ba su kai shekarun jefa quri'a damar jefa ƙuri'a ba, hakan yana kawo cikas ga sahihancin tsarin zaɓe kuma yana sanya alamar tambaya kan sakamakon aikin. A kwanakin baya, gamayyar ƙungiyoyin farar hula 10 (CSO) sun koka…
Read More
Ganduje zai rattaba hannu kan zartar da hukuncin kisan Abduljabbar – Kwamishina

Ganduje zai rattaba hannu kan zartar da hukuncin kisan Abduljabbar – Kwamishina

Daga WAKILINMU Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari'a na Jihar Kano, Lawan Musa, ya bayyana cewa, a shirye Gwamna Abdullahi Ganduje yake ya rattaba hannu kan zartar da hukuncin kisan da kotu ta yanke wa Abduljabbar Nasiru-Kabara. A ranar Alhamis Kotun Shari'a ta Kano ta yanke wa Malamin hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da ta same shi da laifin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW). Kwamishinan ya shaida wa jaridar Daily Trust a ranar Alhamis cewa, Ganduje na bakin ƙoƙarinsa wajen tabbatar da ba a yi wa doka karan tsaye a jihar. Ya ce, gwamnatin jihar ce ta maka Abduljabbar a…
Read More
Abduljabbar: Za mu ɗaukaka ƙara kan hukuncin kisa – Ƙungiya

Abduljabbar: Za mu ɗaukaka ƙara kan hukuncin kisa – Ƙungiya

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Wata ƙungiya ƙarƙashin ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Alhaƙƙu ta bayyana shirinta na ɗaukaka ƙara kan hukuncin kisa da kotun shari'a ta yanke wa Sheikh Abduljabbar Kabara bisa samunsa da laifin ɓatanci. Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Juma'a a Kano, shugaban ƙungiyar Sa'id Bn Usman, ya bayyana cewa ƙungiyar ta tattaunawa da iyalai da makusantan malamin kan batun, kana daga bisani sun yanke shawarar ɗaukaka ƙara domin tabbatar da adalci. Ya ƙara da cewa, ƙungiyar ba ta gamsu da hukuncin ƙaramar kotun ba. A cewarsa, an kammala shirin ɗaukaka ƙarar nan…
Read More
Gwamnati ta ayyana ranakun hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara

Gwamnati ta ayyana ranakun hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun 26 da 27 ga Disamba, 2022 da kuma 2 ga Janairun 2023 a matsayin ranakun hutun gama-gari. Gwamnati ta ba da hutun ne albarkacin bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara. Ta ce 26 da 27 ga Disamba hutu ne don Kirsimeti da 'Boxing Day', yayin da 2 ga Janairu take hutu don bikin sabuwar shekarar 2023. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya fitar ranar Juma'a ta hannun Babban Sakataren Ma'aikatar, Dr. Shuaib M.L. Belgore. Aregbesola ya yi amfani da wannan dama wajen taya…
Read More
Ɓatanci: Ganduje ya samu damar rataye Abduljabbar Kabara

Ɓatanci: Ganduje ya samu damar rataye Abduljabbar Kabara

*A gaggauta kashe ni, inji malamin*Yadda kotu ta yanke masa hukuncin kisa*An haramta karantawa ko sauraron wa’azinsa Daga BABANGIDA S GORA a Kano A ranar Alhamis ta jiya ne wata Babbar Kotun Shari'ar Musulunci da ta ke Ƙofar Kudu a cikin birnin Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola ta bai wa Gamnan Jihar Kano izinin kashe Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ta hanyar rataya, wanda ta samu da hannu dumu-dumu kan furta kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW) bayan kimanin shekara ɗaya da watanni biyar da gurfanar da shi a gabanta. Malam Abduljabbar, wanda kotun ta same…
Read More
Matawalle ya buɗe Gasar Karatun Alƙur’ani ta Ƙasa karo na 37

Matawalle ya buɗe Gasar Karatun Alƙur’ani ta Ƙasa karo na 37

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau A ranar Juma'a Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya ƙaddamar da Gasar Karatun Alƙur'ani mai tsarki ta ƙasa karo na 37 da gwamnatinsa ta ɗauki nauyin gudanarwa a Gusau babban birnin jihar. Da yake ƙaddamar da gasar, Gwamna Matawalle ya bayyana gasar a matsayin wani nau’i na haɗin kan Musulmi a ƙasar nan. Ya ce, gasar za ta bai wa Nijeriya damar zaɓar waɗanda za su wakilci ta a Gasar Ƙur’ani ta Ƙasa da Ƙasa a tsakanin waɗanda suka fafata a gasar. Kazalika, ya ce gasar za ta taimaka wajen gudanar da addu’o’in samun…
Read More