Gwamnati ta ayyana ranakun hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun 26 da 27 ga Disamba, 2022 da kuma 2 ga Janairun 2023 a matsayin ranakun hutun gama-gari.

Gwamnati ta ba da hutun ne albarkacin bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Ta ce 26 da 27 ga Disamba hutu ne don Kirsimeti da ‘Boxing Day’, yayin da 2 ga Janairu take hutu don bikin sabuwar shekarar 2023.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya fitar ranar Juma’a ta hannun Babban Sakataren Ma’aikatar, Dr. Shuaib M.L. Belgore.

Aregbesola ya yi amfani da wannan dama wajen taya al’ummar Kirista na gida da wajen murnan bikin Kirsimeti na bana, kana ya taya ɗaukacin al’ummar ƙasa murnar sabuwar shekara.

Haka nan, ya yi kira da a gudanar da bukukuwan cikin lumana, sannan a guji yaɗa labaran ƙarya don kare rayuka da dukiyar jama’a.

Ministan ya buƙaci al’ummar Kirista da su yi amfani da wannan dama wajen koyi da ɗabbaƙa karantarwar Annabi Isa (AS) kamar yadda ya koyar a lokacin rayuwarsa.