Editor

9513 Posts
Ilimin abinci abu ne mai wahala, dole sai an jure – Chef Khadija

Ilimin abinci abu ne mai wahala, dole sai an jure – Chef Khadija

“Don riƙa yin jagoranci na yin abincin mu ka kafa ƙungiya Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Chef Khadija Idris Sulaiman ƙwararriya ce da ta ƙware wajen iya abinci da dukkanin nau'o'in snacks, baya ga haka, ita ce shugabar Ƙungiyar Mata masu saida Abinci ta Jihar Kano, wato Dexterity Food Forum. A hirarta da wakilinmu a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji irin ɗimbin nasarorin da ta samu da kuma ƙoƙarin da suke na shirya taron cin abinci na mutum 600 a Kano. Ku biyo mu don karanta yadda tattaunawar za ta kasance: BLUEPRINT MANHAJA: Masu karatunmu za su so ki gabatar…
Read More
Tarihin Sarakunan Fulani na Kano (I)

Tarihin Sarakunan Fulani na Kano (I)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yau, jaridar Blueprint Manhaja za ta kawo muku taƙaitaccen tarihin sarakunan Fulanin da suka mulki Kano tun daga jihadin Shehu Usman Ɗan Fodiyo. Malam Sulaimanu ɗan Abuhama: Ya yi sarautar Kano daga 1807 zuwa 1819, Miladiyya: Sarki Sulaimanu shi ne Sarki na 44 a jerin sarakunan Kano, kuma Sarki na farko a zuriyar Fulani. A farkon sarautarsa Fulani sun hana shi shiga Gidan Rumfa, saboda haka sai ya zauna a gidan Sarkin Dawaki. Yana nan zaune cikin wannan gida sai wani mutum ya ce da shi, “Idan ba ka shiga Gidan Rumfa ba Kanawa ba…
Read More
Kotu ta raba auren shekara ɗaya saboda rashin soyayya

Kotu ta raba auren shekara ɗaya saboda rashin soyayya

Wata Kotun Shari’ar Musulinci da ke Ilorin, Jihar Kwara ta raba wasu ma’aurata da aka ɗaura aurensu watanni 12 da suka gabata. Alƙalin kotun, Abdulƙadir Umar, ya ce, matar mai suna Roimat Qodir ta roƙi kotun ta kashe aurenta da mijinta Abdulƙadir AbdulRazak, saboda ba ta sonsa. Bayan alaalin ya tambaye ta ko tana da juna biyu, ta musanta hakan. Shi ma dai mijin ya bayyana wa alƙalin cewa ya amince da buƙatar matar, kuma ko a lokacin ta so za ta iya tafiya. A ƙarshe dai kotun ta raba auren, tare da bai wa matar umarnin yin iddar watanni…
Read More
Muhimmancin kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa

Muhimmancin kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ba da jimawa ba ne aka gudanar da bukin ranar kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa ta duniya, wanda ya mayar da hankali wajen tattauna muhimmancin bai wa lafiyar ƙwaƙwalwa fifiko a vangaren kiwon lafiya, saboda tasirin hakan ga cigaban rayuwa baki ɗaya. Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ware wannan rana a shekarar 1992 domin faɗakar da al'ummar duniya, da karkatar da tunaninsu ga muhimmancin kula da inganta lafiyar ƙwaƙwalwa da faɗakar da jama’a illar nuna wa masu fama da lalurar ƙwaƙwalwa ƙyama ko wariya. Har wa yau kuma tsayar da ranar na da muhimmanci duba da…
Read More
2023: An buga gangar siyasa

2023: An buga gangar siyasa

Daga BELLO MUHAMMAD SHARAƊA Akwai jihohi 36 a Nijeriya, akwai kuma Birnin Tarayya a Abuja. Akwai ƙananan hukumomi 774. Akwai mazavu dubu takwas da ɗari takwas da 12. Akwai akwatunan zave dubu 176 da 846. Akwai mutum miliyan 96 da dubu 200 waɗanda suka mallaki katin zaɓe. Akwai jam'iyyu 18 da suka tsayar da yan takarar shugabancin Nijeriya a zaɓen da za a yi ranar 25 ga watan Fabrairu 2023. A bisa doron tsarin mulkin Nijeriya na 1979 da 1989 da 1999 wanda duk zai zama shugaban ƙasar Nijeriya sai kashi 25 na waɗanda za su yi zaɓe a jihohi…
Read More
Ya harbe ƙaninsa yayin gwada maganin bindiga

Ya harbe ƙaninsa yayin gwada maganin bindiga

Wani matashi ya harbe ƙaninsa mai shekaru 12 yayin gwada maganin bindiga a Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara. Wanda lamarin ya shafa dai ƙanin wani mafarauci ne da suka mallaki wani sabon maganin bindiga kuma suka yi yunƙurin tabbatar da ingancinsa. Lamarin a cewar rahotanni ya faru ne a makon da ya gabata, inda wanda ya yi aika-aikar tuni ya arce ya bazama cikin daji bayan lamarin ya afku. Da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Litinin, Jami’in Hulɗa da Al’umma na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce, Kwamishina ’Yan sanda Paul Odama ya ba…
Read More
Malam Shekarau: Baya ba zani

Malam Shekarau: Baya ba zani

Daga LARABI LARABEEN Ni ba ɗan siyasa ba ne, amma akwai mutanen da 'yan siyasa suke raina wa hankali. Suke wasa da ƙwaƙwalensu. Malam Ibrahim Shekarau na ɗaya daga cikin irin waɗannan mutanen duk da kusan duk 'yan siyasar haka suke. Amma nasa rainin da wasa da ƙwaƙwalwar mabiyansa tana yin yawa. Sanda Malam Ibrahim Shekarau ya bar Jam'iyyar PDP a 2019 ya koma APC, waɗanne muƙamai Ganduje ya bawa mabiyansa? Hatta Malam Salihu Sagir Takai da yake ɗan a mutum Shekarau, bai iya bamar masa ko da Mai ba Gwamna Shawara ba a mulkin Ganduje na APC. Sai Takai…
Read More
Nijeriya ƙasarmu ta gado!

Nijeriya ƙasarmu ta gado!

Daga YUSUF MUHAMMAD DOSARA Yau ma zan sake yin magana a kan wani abu da yake faruwa a jihar Zamfara da ma wasu sassan Nijeriya. Na ji wani sautin murya na waya da aka yi da ƙasurgumin ɗan ta’addan nan Bello Turji a kan harin da jami’an tsaro suka kai masa a kwanan nan. Yana ƙorafin cewa wai an yaudare shi an ci amanarsa, an yi sulhu da shi, amma an dawo an farmake shi, an kashe mai mutane kuma an ƙone masa gida. Wannan maganar ni a wajena babu wani kuskure ko kuma rashin adalci a kan wannan farmakin…
Read More
Ki guji zama ɗaya daga cikin waɗannan mata!

Ki guji zama ɗaya daga cikin waɗannan mata!

Daga AMINA YUSUF ALI Mai karatu a wannan makon za mu kawo muku wasu halaye waɗanda ba a so mace ta siffanta da su. Irin waɗannan mata da wuya maza su yarda su kasance a inuwa ɗaya da su, in dai har ya san da waɗannan halayen kafin ta shiga gidansa. Da fatan waɗannan baragurbin mata za su gyara ko kuma su zama abun gudu. *Mace maɓarnaciya/al-mubazzara: Ita ce macen da ba ta da tattali da kaffa-kaffa da kayan gida idan mai gida ya kawo. Irin waɗannan mata ba qaramin shaƙa wa maza baƙinciki suke a zukatansu ba. Musamman maza…
Read More
Takardun kuɗin da suka shaida yadda ƙasashen duniya suka ci gajiyar ci gaban Ƙasar Sin

Takardun kuɗin da suka shaida yadda ƙasashen duniya suka ci gajiyar ci gaban Ƙasar Sin

Daga LUBABATU LEI Jama’a, in kun yi la’akari da takardun kuɗi na ƙasa da ƙasa, za ku gano da cewa, hotunan da aka buga a takardun kuɗi na wasu ƙasashen Afirka, da ma sauran wasu ƙasashe masu tasowa, suna da alaƙa da ƙasar Sin. Zanenmu na yau ya kuma nuna wasu abubuwan da aka buga a takardun kuɗi na ƙasashen Aljeriya, da Sudan, da Madagarscar da Malawi, wadanda suke da alaƙa da ƙasar Sin. In mun ɗauki takardun kuɗi na Aljeriya ga misali, za mu ga cewa, an buga hoton babban masallacin ƙasar da aka sanyawa sunan Djamaa el Djazaïr,…
Read More