Editor

9513 Posts
Masanan Amurka: Cutar COVID-19 ba ta ƙare ba tukuna

Masanan Amurka: Cutar COVID-19 ba ta ƙare ba tukuna

Daga CMG HAUSA Yayin da ake mayar da martani game da maganar cewa, “Cutar COVID-19 ta riga ta ƙare a cikin Amurka”, kwanan nan wasu masana a Amurka suka fitar da wani bayani dake nuna cewa, ba a shawo kan cutar ba tukuna a cikin ƙasar, kuma ganganci ne da rashin hankali a riƙa wasa da annobar. A kwanakin nan ita ma jaridar Washington Post, ta wallafa wani sharhi, inda ta jaddada cewa, cutar COVID-19 ba ta ƙare ba a Amurka. A cikin bayanin, an ce cutar COVID-19 ta daɗe tana yaɗuwa, inda wasu mutane suka mutu sanadiyar kamuwa da…
Read More
Matsin tattalin arziki: Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙara mafi ƙarancin albashi – Ministan Ƙwadago

Matsin tattalin arziki: Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙara mafi ƙarancin albashi – Ministan Ƙwadago

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa, tana da shirin ƙarin ma fi ƙarancin albashi daga dubu 30 zuwa sama sakamakon matsin tattalin arzikin da ya addabi Duniya. Ministan Ƙwadago da ɗaukar aiki na Nijeriya, Dakta Chris Ngige, shi ya bayyana haka a taron bitar al'umma wanda ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta shirya a Abuja. A cewar Ngige, dole gwamnatin ta duba wannan lamari saboda abinda yake faruwa na yanayin faɗuwar tattalin arziki a Duniya. Ya ƙara da cewa, wannan karyewar tattalin arzikin ta tava Duniya bakiɗaya.…
Read More
KADA ta yi zaɓenta na 2022

KADA ta yi zaɓenta na 2022

Daga BASHIR ISAH A ranar Asabar ta ƙarshen makon jiya, aka gudanar da zaɓen ƙungiya Karofi Development Association (KADA) da ke Keffi cikin ƙaramar hukumar Keffi, Jihar Nasarawa. Zaɓen wanda aka soma da misalin ƙarfe 8, ya kammala ne da misalin ƙarfe 7 na yamma bayan tantance ƙuri'u, ƙirgawa da kuma sanar da sakamakon zaɓe. Zaɓen ya gudana ne ƙarƙashin kulawar Kwamitin Zaɓe (ELCOM) mai ƙunshe da mambobi bakwai ƙarƙashin shugabancin Dr Ismaila Yusuf Usman. Yayin ƙirga ƙuri'a Bayan kammalawa, Isah Umar (Turakin Kongo) shi ne wanda ya lashe zaɓe a matsayin sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙungiya da ƙuri'u 347. Sauran…
Read More
Ƙungiyar Direbobin Tifa ta rantsar da sabbin shugabaninta a Kano

Ƙungiyar Direbobin Tifa ta rantsar da sabbin shugabaninta a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar Direbobin Tifa ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, ta rantsar da sabbin shugabanin rassan ƙungiyar da ke Kano. Ƙungiyar dai ta gudanar da bikin rantsar da sabbin shugabanin rassan guda 196 da ya gudana a sakatariyar ƙungiyar da ke Kano a Lahadin da ta gabata. Da ya ke jawabi shugaban ƙungiyar ’yan tifa na jihar nan Mamunu Ibrahim Takai, ya buƙaci sabbin shugabanin rassan da su kasance masu kwatanta adalci wajen sauke nauyin da ke kansu. Shi ma a jawabinsa, shugaban hukumar kula da hanyoyin ruwa na ƙasa reshen Kano da Jigawa da Bauchi Maude…
Read More
Yadda za a magance matsalar kogon haƙora (2)

Yadda za a magance matsalar kogon haƙora (2)

Daga AISHA ASAS A satin da ya gabata mun kawo wa masu karatu bayyanin yadda matsalar kogon haƙora ke samun gindin zama da kuma yadda mu ke zafafa ta ba tare da sanin mu ba. Kazalika mun tavo asalin cutar, kafin mu kawo wasu daga cikin hanyoyin da za a magance matsalar. A wannan satin da yardar mai dukka, za mu ci gaba daga inda mu ka tsaya. Amfani da gishiri: Kasancewar gishiri na ɗauke da sinadarai da ke kashe ƙwayoyin cuta da kuma gyara ɓarnar da suka yi ta hanyar waraka ne ya sanya ya shigo cikin jerin ababen…
Read More
Dandalin shawara

Dandalin shawara

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Barka da wannan lokaci Malama Aisha. Allah ya yi jagora. Na karanta wasu daga cikin shawarwarin da kike ba wa ‘yan’uwa a jaridar Manhaja, sai na ce tunda dai Ina da lambarki bari na turo da tawa matsalar a nan. Tun ina ɗan shekara tara na fuskaci wata matsala, inda kawuna ya yi lalata da ni. Kawuna na zaune ne a gidanmu, kuma yana sona sosai da siya min duk abinda ya gani na yara. Wannan dalilin ne ya sa kowa gidanmu yake kirana ɗan kawu. Da ya dawo gida zai kaiko kirana in same shi…
Read More
NLC ta gargaɗi Buhari kan yinƙurin ƙwace lasisin ASUU

NLC ta gargaɗi Buhari kan yinƙurin ƙwace lasisin ASUU

Daga WAKILINMU Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), ta gargaɗi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan take-taken neman ƙwace lasisin rijistar Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) saboda rashin miƙa bayanan hada-hadar kuɗaɗenta na tsawon shekaru biyar. NLC ta yi wannan gargaɗi ne a matsayin martani ga wani rahoton da ya nuna Gwamnatin Tarayya na shirin janye rijistar ASUU saboda saɓa ƙa'ida, inda ta aike da wasiƙar gargaɗin zuwa ga Ministan Ƙwadago, Chris Ngige da Shuganan NLC ma Ƙasa, Ayuba Wabba. NLC ta yi tsayin daka kan cewa, lallai ASUU ta miƙa rahoton hada-hadar kuɗaɗenta baki ɗaya har zuwa 2021, don haka ba ta…
Read More
An tsare tsohuwar matar MKO Abiola a kurkuku bisa zargin cin mutuncin ‘yar sanda

An tsare tsohuwar matar MKO Abiola a kurkuku bisa zargin cin mutuncin ‘yar sanda

Daga WAKILINMU An ingiza ƙeyar tsohuwar matar shahararren ɗan kasuwa kuma ɗan siyasar nan, MKO Abiola, Zainab Duke-Abiola, ya zuwa gidan kaso a garin Suleja bisa zargin cin mutuncin 'yar sandan da ke ba ta kariya, Teju Moses. Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa na zamani ya nuna yadda Zainab wadda lauya ce kuma 'yar gwagwarmayar kare 'yancin bil Adama, ta umarci 'yar aikinta, Rebecca Enechido, kan ta duki Teju saboda ƙin yin wasu ayyuka da ta ɗora mata. An ga jami'ar cikin rigar aiki yayin da jini ke fita daga jikinta zaune dirshan a ƙasa tana neman a…
Read More
ICPC ta koka kan yadda ake karkatar da kuɗaɗen jama’a

ICPC ta koka kan yadda ake karkatar da kuɗaɗen jama’a

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta, ICPC, ta yi tsokaci jiya Alhamis a Abuja kan yadda ake karkatar da kuɗaɗen jama’a. Shugaban hukumar ta ICPC, Farfesa Bolaji Owasannoye ne ya yi wannan tsokaci a wajen wani taron ƙara wa juna sani na kwana biyu da mambobin kwamitin majalisar wakilai kan yaƙi da cin hanci da rashawa suka gudanar. Shugaban ya fusata kan yadda ake karkatar da kuɗaɗen jama’a, ta hanyar karɓar kuɗaɗen shiga da kuma kashe kuɗaɗe, yayin da ya yi Allah-wadai da yadda ake tafiyar da harkokin kuɗi ba…
Read More
Wang Yi ya halarci muhawarar babban taron MƊD karo na 77

Wang Yi ya halarci muhawarar babban taron MƊD karo na 77

Daga CMG HAUSA Ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya halarci muhawarar babban taron MƊD karo na 77 a hedkwatar majalisar dake birnin New York na ƙasar Amurka, tare da gabatar da jawabi mai taken “Yin ƙoƙarin don samun ci gaba cikin lumana da kuma ɗaukar alhaki don samun ci gaba ta hanyar haɗin gwiwa”. Wang Yi ya bayyana cewa, wannan zamani na cike da ƙalubale da kyakkyawan fata. Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’Adama da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar bisa buƙatun zamanin da ake ciki. Ya…
Read More