25
Sep
Daga CMG Hausa Gomman ɗalibai sanya da tufafi masu ban sha’awa ne suka buga ganguna tare da rera waƙe-waƙe domin murnar sake buɗe cibiyar koyar da harshen Sinanci da aka yi wa gyaran fuska, a Abuja, babban birnin Nijeriya. Sashen 18 na kamfanin gine-gine na China Railway ne ya yi wa cibiyar gyaran fuska. An gina cibiyar ne a shekarar 2008, a makarantar ƙaramar sakandare ta yankin Garki Area 11 na birnin Abuja, da nufin kyautata fahimta tsakanin ƙasashen biyu tun daga matakin farko. Alhassan Sule, shugaban hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta birnin tarayya Abuja, ya ce daddadiyar…
