24
Sep
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kocin AS Roma, Jose Mourinho, ya shaida wa ’yan wasansa cewar daga yanzu su riƙa yawaita faɗuwa ko da kuwa da gangan ne, don samun qarin damarmakin bugun daga kai sai mai tsaron raga. A ranar Lahadin da ta gabata, Mourinho ya yi fuskatar da ta kusan kai shi ga rafke alƙalin wasa Daniele Chiffi, saboda hana su damar bugun fanareti, a wasan da Atalanta ta doke su da 1-0. yayin tankiyar sai dai aka riƙe Mourinho domin hana shi make alƙalin wasan, saboda watsin da ya yi da kiran ya hukunta ɗan wasan Atalanta Caleb…
