KADA ta yi zaɓenta na 2022

Daga BASHIR ISAH

A ranar Asabar ta ƙarshen makon jiya, aka gudanar da zaɓen ƙungiya Karofi Development Association (KADA) da ke Keffi cikin ƙaramar hukumar Keffi, Jihar Nasarawa.

Zaɓen wanda aka soma da misalin ƙarfe 8, ya kammala ne da misalin ƙarfe 7 na yamma bayan tantance ƙuri’u, ƙirgawa da kuma sanar da sakamakon zaɓe.

Zaɓen ya gudana ne ƙarƙashin kulawar Kwamitin Zaɓe (ELCOM) mai ƙunshe da mambobi bakwai ƙarƙashin shugabancin Dr Ismaila Yusuf Usman.

Yayin ƙirga ƙuri’a

Bayan kammalawa, Isah Umar (Turakin Kongo) shi ne wanda ya lashe zaɓe a matsayin sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙungiya da ƙuri’u 347.

Sauran zaɓaɓɓun shugabannin sun haɗa da; Isah S. Isah a matsayin mataimakin shugaba, Jamilu M. Maihakuri a matsayin babban sakatare, Umar Bako (Ɗalla) a matsayin sakataren kuɗi da kuma Ibrahim Muhammad a matsayin PRO.

Sauran su ne, Solomon David a matsayin jami’in walwala, Abdulmumin Bayaro a matsayin sakataren tsare-tsre, Usman Muh’d Rabiu a matsayin jami’in bincike, Ibrahim Jawad a matsayin mataimakin sakatare da sauransu.

Akwatin zaɓe

KADA ƙungiya ce wadda unguwanni uku suka amince su haɗa kai don taimakon kai-da-kai da kuma cigaban al’umma da suka haɗa da unguwar Karofi da Kongo da kuma Gangaren Karofi.

Akan gudanar da zaɓen ne duk bayan shekaru biyu kuma bisa tsarin karɓa-karɓa da zummar samar da cigaban al’umma.