27
Sep
Daga FA’IZA MUSTAPHA A baya-bayan nan ne aka yi bikin buɗe cibiyar koyar da harshen Sinanci da kamfanin gine-gine na ƙasar Sin na CRCC ya yi wa kwaskwarima, a makarantar sakandare ta Garki Area 11 dake Abujan Nijeriya. Haka zalika a jiya, an yi bikin buɗe kwalejin Confuscious a jami’ar Alkahira dake Masar, don ƙaddamar da shirin koyar da harshen Sinanci. Bambancin harshe babban ƙalubale ne dake karan tsaye ga kusan kowacce mu’amala, sannan fahimtar juna, ita ce tushen ingantacciyar dangantaka da za ta tabbatar da ɗorewarta. Muddin aka samu fahimtar juna ta fuskar al’adu da harshe, to za a…
