28
Sep
Daga CMG HAUSA A yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping da takwaran aikinsa na ƙasar Argentina Alberto Fernández sun miƙa wasiƙar murnar buɗe taron dandalin tattaunawa kan musayar al'adu tsakanin ƙasashen biyu. A cikin wasiƙar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 50 da ƙulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Argentina. A cikin rabin karnin da ya gabata, dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu ta himmatu wajen tinkarar ƙalubalen da ƙasashen duniya suke fuskanta, kana ta zama abin koyi na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe masu tasowa a fannonin hadin gwiwa da…
