30
Sep
Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ƙungiyar Ƙwararrun Matan APC na Ƙasa wadda aka fi sani da APC Professional Women Council of Nigeria a turance reshen Jihar Nasarawa ta tabbatar wa gwamnan jihar injiniya Abdullahi Sule cikakken goyon bayanta ɗari bisa ɗari don samun nasarar sa karo na biyu a zaɓen gwamnoni na shekarar 2023 dake zuwa. Kodinitar ƙungiyar a jihar Kwamared Hajiya Halima Haruna Kunza ce ta bayyana haka a jawabin ta a wajen wani gangamin wayar da kawunan al’umma da neman goyon baya wa gwamnan wanda ƙungiyar ta shirya ta gudanar a cibiyar matasa na Ibrahim Abacha dake…
