Editor

9513 Posts
Ambaliya: An yi kira ga gwamnati ta kai wa manoma ɗauki

Ambaliya: An yi kira ga gwamnati ta kai wa manoma ɗauki

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihohi su kawo cikakken tallafi don agaza wa mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa a ƙasar nan. Dattijon Arewa, Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpasa shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Kano. Ya ce gonakin da ruwa ya lalata amfanin gonarsu a Jihar Kano kaɗai sun haura dubu shida, "wasu ma suna shirin girbi Allah ya kawo wannan ibtila'in, mutane da dama sakamakon haka sun shiga halin tagayyara, abinda za su ci da iyalansu ma babu.  "Don haka ya kamata gwamnatoci su ɗauki mataki na…
Read More
Zargin ɓatanci: Abduljabbar ya zargi lauyansa da karɓar cin-hanci na miliya N2

Zargin ɓatanci: Abduljabbar ya zargi lauyansa da karɓar cin-hanci na miliya N2

Daga BASHIR ISAH Fitaccen malamin nan na Kano wanda ake zargi da ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW), Abduljabar Kabara, ya yi zargin lauyansa, Dalhatu Shehu-Usman ya karɓi kuɗi Naira miliyan N2 don bai wa alƙalin Kotun Shari'a ta Kano a ci gaba da shari'ar da ake yi masa. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya rawaito ana tuhumar malamin ne da laifuka guda huɗu da suka haɗa da ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW) wanda ya aikata a ranakun 10 ga Agusta, 25 ga Oktoba da kuma 20 ga Disamba, 2019. Yayin zaman da kotun ta yi a ranar Alhamis, lauyan…
Read More
APC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu na tabbatar da Machina ɗan takarar sanata

APC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu na tabbatar da Machina ɗan takarar sanata

Daga BASHIR ISAH Jam'iyyar APC mai mulki ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na tabbatar da Bashir Machina a matsayin ɗan takarar sanata a Yobe ta Arewa na APC a zaɓen baɗi. Idan za a iya tunawa, a ranar 28 ga Satumba, 2022, wata Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Damaturu babban birnin jihar, ta tabbatar da Bashir Machina a matsayin wanda zai yi wa APC takarar sanata a shiyyar Yobe ta Arewa a 2023. Kotun ta bai wa APC umarnin ta miƙa sunan Machina ga hukumar zaɓe INEC, a matsayin ɗan takara. Dambarwar takarar…
Read More
Haɗin kan Sin da Argentina ya zamo abin misali ga ƙasashe masu tasowa

Haɗin kan Sin da Argentina ya zamo abin misali ga ƙasashe masu tasowa

Daga CMG HAUSA A bana ne ake cika shekaru 50 da kafuwa hulɗar diplomasiyya tsakanin Sin da Argentina. A matsayin ɗaya daga cikin wasu ayyukan murnar wannan muhimmin lokaci, kana shekarar sada zumunta tsakanin ƙasashen biyu na shekarar 2022, an gabatar da dandalin manyan shugabanni, na mu’amalar al’adu tsakanin ƙasashen biyu, inda shugabannin ƙasashen biyu suka aikewa juna wasikar taya murna. Abin da ya bayyana cewa, shugabannin ƙasashen biyu na dora babban muhimmanci kan haɗin kansu. A cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, dangantakar dake tsakaninsu ta sauya, daga abokai masu nisa da juna zuwa abokan haɗin kai a…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Ibrahim Gusau ya lashe zaɓen NFF

Da Ɗumi-ɗumi: Ibrahim Gusau ya lashe zaɓen NFF

An zaɓi Alhaji Ibrahim Musa Gusau a matsayin sabon Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF). An zaɓi Gusau a wannan muƙamin ne yayin zaɓen NFF karo na 78 da ya gudana a Benin, babban birnin Jihar Edo a ranar Juma'a. Sakamakon zaɓen ya nuna Gusau ya samu ƙuri'u 21 wanda hakan ya ba shi nasara a kan tsohon Mataimakin Shugaban hukumar na 1, Barista Seyi Akinwunmi wanda ya samu ƙuri'u who got 12 kacal.
Read More
Xi Jinping ya gana da wakilan rukunin ƙera babban jirgin saman fasinja na C919

Xi Jinping ya gana da wakilan rukunin ƙera babban jirgin saman fasinja na C919

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan tawagar rukunin da suka yi aikin ƙera babban jirgin saman fasinja ƙirar C919 a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, kana ya halarci bikin nune-nunen nasarorin da aka cimma, inda ya yaba da nasarorin da aka samu game da aikin ƙera jirgin saman. Shugaba Xi ya jaddada cewa, shawagin babban jirgin sama ƙirar ƙasar Sin a sararin sama, shi ne burin ƙasa da al’ummar Sinawa da kuma jama’ar Sin. Ya ce ya kamata a yi amfani da fifikon sabon tsarin albarkatun ƙasar, da martaba ƙa’idojin tabbatar da…
Read More
Csaba Korosi: Sin ta zmo babbar garkuwa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MƊD

Csaba Korosi: Sin ta zmo babbar garkuwa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MƊD

Daga CMG HAUSA Shugaban babban taron MƊD na 77 Csaba Korosi ya bayyana cewa, ƙasar Sin a matsayin babbar garkuwa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MƊD. Mr. Korosi, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin taron taya murnar cika shekaru 73 da kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, wanda ofishin wakilcin Sin a MƊD ya kira ta kafar bidiyo. Ya ce a matsayinta na daya daga cikin ƙasashen da suka assasa MƊD, kuma wakiliyar dindindin a kwamitin tsaron majalissar, Sin ta taka rawar gani yadda ya kamata. Korosi ya kuma taya Sin murnar manyan nasarorin da ta cimma…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe sufeton ‘yan sanda, sun sace fasinjoji a kan hanyar Katsina zuwa Jibiya

‘Yan bindiga sun kashe sufeton ‘yan sanda, sun sace fasinjoji a kan hanyar Katsina zuwa Jibiya

Daga UMAR GARBA a Katsina ‘Yan bindiga da ke aikin ta'addanci a dajin Ƙaramar Hukumar Jibiya dake cikin Jihar Katsina sun kashe wani sufeton ‘yan sanda mai suna Idris Musa a unguwar Maƙera da ke yankin Kwakware a kan hanyar Katsina zuwa Jibiya. Kakakin rundunar 'yan sanda na Jihar Katsina SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewar iftila'in ya rutsa da jami'in ɗan sandar a lokacin da yake tafiya cikin motarsa zai nufi wurin aiki. Wani da lamarin ya faru a gaban idonsa muka kuma sakaya sunansa ya shaidawa Manhaja cewar ‘yan bindigar sun isa…
Read More
‘Yan bindiga sun sace basarake a Filato

‘Yan bindiga sun sace basarake a Filato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun sace wani basarake, Alhaji Dabo Gutus a ƙauyen Tal da ke Ƙaramar Hukumar Pankshin a Jihar Filato. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne misalin ƙarfe ɗaya na dare a ranar Litinin. Wani mazaunin ƙauyen ya ce mutane na ta ƙoƙarin kiran 'yan bindigar don sanin halin da basaraken yake ciki. Prince Dakup Ezra, wanda yake wakiltar ƙauyen Panshin a majalisar dokoki, ya yi kira a kwantar da hankali, yana mai cewa babban burinsu shi ne a kuɓutar da…
Read More
An ceto jaririn da aka sace a Asibitin Koyarwa na ATBU – Mahukunta

An ceto jaririn da aka sace a Asibitin Koyarwa na ATBU – Mahukunta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar gudanarwar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi (ATBUTH), ta ce ɗaya daga cikin tagwayen jarirai 'yan kimanin makonni biyu da aka sace a asibitin an gano shi a Bauchi. Dr. Haruna Liman, Shugaban Kwamitin Bada Shawarar Likitoci, CMAC, na asibitin ya bayyana haka, a lokacin da yake miƙa jaririn ga mahaifiyar ranar Talata a Bauchi. Ya ce an sace jaririn daga hannun mahaifiyar a asibiti bayan kwana takwas da haihuwa. “An sace jaririn ne a ranar 21 ga Satumba, 2022 da ƙarfe 4:30 na yamma daga hannun mahaifiyar da…
Read More