02
Oct
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom ya musanta rahotannin da ke cewa yana goyon bayan tsige Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Dr Iyorchia Ayu daga muƙaminsa, inda ya ce babu yadda za a yi ya goyi bayan cire wanda ya taimaka aka naxa. Jaridar TheCable ta rawaito cewa Ortom ɗin ya kuma ce yana da yaƙinin Mr Ayu zai jagoranci jam’iyyar ga nasara a zaven baɗi. Waɗannan kalaman sun ci karo da matakin da ɓangaren Gwamna Wike wanda Ortom mambe ne, da ke neman lallai sai an cire Iyorchia Ayu matuƙar ana son zaman lafiya…
